Thursday 22 February 2018

SHIN KO KASAN MATA IRI BAKWAI A DUNIYA TO KARKU AURE SU-Karanta Kaji

Tura Wannan Zuwa

1. Al-Annaanah : itace mace mai yawan karyar
ciwon kai ko kuma wani ciwon wani abin daban
amma kuma alhali karya takeyi, alhalin babu
abinda ke damunta. To tin kafin ka aureta idan
kagane ta da wannan halaye na karyar ciwo don
cinma wani manufarta to kayi hattara.

2. Al-Mannaanah : mace mai yawan gori wa
mijinta musamman idan tayi masa kyauta ko tayi
wani aikin da shi yasa ta, wanda zakaga tana
yawan cewa " na maka kaza da kaza ai" haka ma
ranan nayi maka kaza ai" to idan kagane
bazawarar da zaka aura ko budurwar da zaka
aura tanada wannan hali to kayi mata nasiha idan
taki dainawa to kayi hattara.

3. Al-Hannaanah : mace mai yabon ya'yan
tsohon mijinta agaban sabon mijinta. Wanda
zakaga tana cewa " ai yaran tsohon mijinta sunfi
naka yaran da dai sauran cin fuska, idan kagane
tanada wannan hali na yabon yaran tsohon
mijinta to kahakura da ita yafi maka alheri.

4. Kai' Atul Qafaa : macen da takeda "bad
record", wanda yakaiga duk jama,a suna ganinta
da mummunan hali da rashin kima to kayi hattara
da auren irin wannan matar inji shaikh
muhammad al uthaymeen .

5. Al-Haddaaqah : macen da idan taga wani abu
wanda takeso saita tilasta ta takurawa mijinta
yasai mata kota halin meye itadai yasai mata.

Yawanci ana ganesu saboda sune tin kafin ka
aure su zakaga tana damunka da sai ka sai mata
kaza ko saika bata kudin anko da dai sauran
su,duk mace ,mai irin wannan naciya da
takurawa ma saurayi to irin sune Al-Haddaaqah.
Sai kayi hattara

6. Al-Shaddaaqah : macen da takeda yawan
surutu, tayadda bata rike sirrin mijinta , yawanci
ana ganesu idan suna yan mata, domin sune
zakaga idan kayi magana da ita ta sirri zakaga ta
kwashe ta fadawa kawayenta duk hirar ku. Idan
kagane budurwarka nada wannan
halaye to kayi hattara don ko kunyi auren bazata
fasaba sai dai wani ikon Allah.

7. Al-Barraaqah : mace mai yawan bata lokacinta
arayuwa wajen yin kwalliya, wanda zakaga tana
ta faman kwalliya har tsawon

Allah yasa muda ce da Dacewar sa ya kuma sa muyi Kyakykyawan Karshe Amin Suma Amin

Source by ©M. Kabiru Muhammad

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: