Sunday 1 April 2018

Karanta Kaji: Babu Mace Mai Dadin Zaman Aure Kamar ‘Yar Hausa Fim – Ladidi Tubeeless

Tura Wannan Zuwa

A duk lokacin da aka dauko
batun aure, wasu da yawa kan yi
wa ‘yan fim gani-gani. To amma
a wannan karon magana ta kare,
domin jarumar da muka tattauna
da ita a wannan makon ta ce
rashin sani ne ke sa mutane
kyamatar auren ‘yan fim.

Idan mutum ya fahimci lamarin
kuwa, zai fi wadanda ke auren
wadanda ba ‘yan fim ba jin
dadin zaman aure, ko me ya sa?

Sammam Masu karatu ko kun
san shahararriyar jaurmar wasan
kwaikwayon ta taba yunkurin
shiga aikin soja kafin ta fara
wasa?

A karanta firar duka a ji:

Taurarin Nishadi

Muna so mu ji cikakken tarihin
rayuwarki
Ni dai sunana Ladidi Abdullahi
An fi sani na da suna Tubeeless.

An haife ni a Kaduna a wata
unguwa da ake kira Sabon Gari
Nassarawa, wato dirkania ke
nan. Na yi Furamare wato a
Nassarawa na kuma je
makaratar gaba da
Furamare.duk a Kaduna wato,
ina gama sakandare aka yi min
auren fari sai Allah bai yi
zamana da mijin ba, sai muka
rabu.

Daga nan sai na ji ina son yin
aikin kaki, na je na sayi ‘form’
din aikin soja na ruwa na cika
na ba da aka kira mu, na je duk
abubuwan da ake yi na yi daga,
baya ban sake bin ta kan shi
kuma ba saboda oda wasu
dalillai.

Yaushe kika fara fim din Hausa,
da wane fim kika fara, kuma Me
ya jawo ra’ayinki kika shiga?

Wata rana sai Rabi’u Rikadawa
ya zo gida ya same ni ya ce
min, ki zo mu je ki yi aikin fim,
shi da Obina. Na ce musu ku je
zan zo,
Amma sai na ki zuwa na neme
su. Sai muka hadu da Zainab
Abubakar muna hira ta ce min,
ki zo mu yi aikin fim mana. Na
ce mata zan bi ki. Ta ce, min,
duk ran da za ta yi aikin za ta
kira ni mu je mu yi tare. Na ce
mata ba damuwa. kuma kafin
nan, muna Hausa ‘drama’ a
makaranta dama. Ran da Alfa
‘care’ zai yi wani fim sai ta ce
na zo mu je. Na ce mata to,
muka je muka gana, sai shi ya
tambaya da ma ina fim ne?
Saboda ya ga ba na kuskure.

Daga nan sai na muka cigaba da
zuwa N TA. Oganmu George ya
ce,, na iya ‘drama’ ana ta sani.
Daga nan kuma ’yan Kano suka
zo Kaduna za su yi wani flm sai
aka kira ni. Kafin nan mun yi
wani flm wanda Rabi’u Koli ya
sa Wada Rikadawa ya kira na yi,
sai na ciga da aiki sai aka
cigaba da kira na ina yi, shi ne.

Sai dai na manta shekarar
gaskiya. Nasiru Gwagwazo zai yi
wani fim Balarabe da Balarabe
dila ya kira ina Abuja ya ce na je
Kaduna za mu yi wani fim. Shi
ma Nasiru Gwagwazo ya kira ni,
na ce musu ina zuwa nako zo
muka yi.

Fim din da na fara na Turanci
ne, shi ne na Alfa ‘care’.

Yaya kike kallon rayuwar mace a
fim ‘industry’ yandu?

Gaskiya tun daga Alfa ‘care’ na
zo NTA .rayuwar mace a harka
fim gaskiya tana fuskantar
kalubale sosai.

Mafi yawan lokaci sai a ce ba
za a aure ki ba saboda ’yar fim
ce, amma kuma rashin sani ne
yake kawo haka. Babu mace
mai dadin aure da kuma dadin
zama irin ’yar fim. Rayuwar
mace a fim ‘industry sai dai na
ce kalilan ne saboda za ta yi
aure komai girmanka kuma
komai tashenta wannan shi ne.

A matsayin ki ta tsohuwar ’yar
fim, wace shawara za ki bai wa
yara masu tasowa yanzu a
harkar?

Shawara ta gare su shi ne su yi
karatu, saboda na ga gaba
abubuwa za su canje wanda zai
kai lokaci da sai kana da karatu
za ka yi shi kansa fim din ma.
In ba ka da karatu wallahi ka
zama ‘sorry’. Ita ce kawai
shawarata gare su.

Shin Ko Kina da yara da miji
kuwa? In da yaran su nawa ne
kuma ta yaya kike hada
dawainiyar aikinki da hidimar
iyali?

Hmmmm! Ba ni da yara, amma
insha Allahu zan yi aure kuma
zan haihu, amma yanzu kam ba
ni da ko daya.

Ko Kina da sha’awar ‘directing’
ko ‘producing’ fim na kanki nan
gaba?

Na yi ‘producing’ har sau 5,
amma ban ji dadi ba, a gaskiya,
saboda haka na bari na hakura
na koma ‘acting’ dina kawai.

A karshe shin bayan fim kina
wani sana’ar ne ko Aikin ofis?

Baya ga fim ba na wani aiki
.amma ina yin aure zan nemi
aiki, saboda mijin da zan aure ba
zai bari na yi fim, ba. Zan
kakkabe kwalina na nami aikin
ofis, tun da ina da kwali kuma
don haka ne na yi karatun.

Mun gode sosai da hadin kan da
kika ba mu, Allah ya taimaka
Ni ma na gode da kika ba ni
lokaci na amsa sa tambayoyin.
Na gode Allah ya raya zuriya.

Source by ©Leadership

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: