Monday 2 April 2018

KARANTA KAJI: TAKAITACCEN TARIHIN ZUWAN TURAWA ZARIA

Tura Wannan Zuwa

Tun gabannin mamayar turawa ga daular Zazzau,
an samu cewa karfin daular ya ragu nesa da
yadda ta kasance a baya sabili da wasu dalilai
Da fari dai, akwai rikicin cikin gida daya mamaye
kabilun fulani da suka jagoranci karɓe ikon
Zazzau a zamanin Jihadi saboda neman mukami.

Ance tun zamanin Sarki na farko aka soma
wannan saɓanin tsakanin Jagora kuma sarkin
Zazzau na farko Mallam Musa da wani Ja'e
shugaban kabilar fulani Yesgwamawa, amma sai
aka bashi sarautar Kajuru aka zauna lafiya.

Daga baya sai rikicin ya sake kamari bayan
rasuwar Sarkin Zazzau Usman Yero, a wajajen
shekara ta 1897 kenan.

Hakan ya samu ne ta yadda kabilu huɗu na
fulani da aka sani da mulkin zazzau suka nuna
bukatarsu ga mulkin, kabilun sune Mallawa,
Katsinawa da Barnawa.

A cikin masu neman mulkin akwai ɗan marigayi
Sarki Yero mai suna Madaki Kwasau, sai Mallam
Lawan ɗan tsohon Madaki da kuma wani daga
cikin 'ya'yan tsohon sarkin zazzau Mallam
Sambo.

Babban abinda kuma ya samar da saɓani a
lokacin shine yadda Galadima ya tsaya kai da
fata cewar wani kurma kuma Makaho mainsuna
Mallam Muhammd ya kamata a baiwa sarauta.

Mutane sunce hakan nada nasaba da kokarinsa
na ɗora wanda ba zai iya kataɓus ba a mulki ta
yadda zai rinka juya shi.

Ganin karfin ikonsa yasa waɗancan kabilu na
fulani suka dunkule tare da goyawa Madaki
kwasau baya domin ya zama sarki.

Akan haka
suka nemi gudunmuwar Sarkin Kano Aliyu Babba,
da kuma rundunar 'yan bindiga da mahaifin
Madaki Kwasau ya kafa a zamanin rayuwarsa,
shikuwa Galadima sai ya nemi goyon baya daga
Sokoto.

Ana cikin wannan kiki-kaka, sai wazirin sokoto
Buhari yazo zazzau da niyyar masalaha. Ya lura
da haɗarin dake ciki ainun idan aka ɗora wani ba
Kwasau ba akan gadon mulki, tunda yasan yadda
Basasa ta kaya a kano, sai kurum ya ɗora
Madaki Kwasau sarautar Zazzau.
Yin haka keda wuya sai wasu daga mabiya da
garuruwa suka fara yin bore.
Sarki Kwasau ya shirya yaki ya tafi Gwari, da
Kataf da Kadara tare da tilasta musu yin biyayya
a gareshi.

Abu na biyu kuma da ya sake raunana zazzau
shine hare-haren da take samu daga wasu
sarakunan hausa misalin Maraɗawa da Ningawa.
Idan dai ba'a manta ba, a lokacin Maraɗawa na
tsaka da kai hare-hare kasar hausa. Bayan sarkin
su Dan baskore ya mutu, sai wanda ya gajeshi
mai suna Baratiya ya ɗora akan inda ya tsaya.
Baya danan sai Mutanen Ningi, waɗanda akai-
akai suke kawo hari ga birnin Zazzau. Shine har
akace sun taba yiwa zazzau ɗin ruwan kibiyoyi a
lokacin da suka kawo faɗa zazzagawa suka shige
cikin ganuwa suka kulle kansu.

Kuma har sun
kwace ikon wasu garuruwa irinsu Soba, Dutsen
Wai da Kubau daga Zazzau.
Kari akan haka shine Sarkin Kwantagora
Nagwamutse, shima a lokacin ya addabi
zazzagawa da hari.
Duk kuma a wannan lokaci turawa fakare sukai
suna kallon zazzau. Saboda ance sun gama
lissafa cewar itace cibiyar da zata fi a garesu
wajen kafa sansani kafin kaiwa Kano da Sokoto
hari.

Kuma kasancewar akwai turawan mishan dake
al'amuransu a Zaria sai ya zamana turawa basu
da burki gareta, suna shigowa suyi hurɗoɗinsu
babu tsangwama.

Ana haka sai labari yazowa Sarkin Zazzau
Kwasau cewa turawan mishan sun nemi wurin
zama a Kano amma sarki Alu ya koresu, sannan
rundunar dakarun turawa mai suna 'West African
Frontier Force' (WAFF) ta kone garuruwan Remo
da Kaje dake karkashin zazzau, kuma da raɗe
raɗen zasu kawowa zaria yaki don hana cinikin
bayi. Sai kawai sarki Kwasau shima ya kori
turawan mishan daga kasar sa suka koma Girku
da zama.

Yin wannan keda wuya sai shugaban waccan
runduna ta turawa mai suna Kaftin Kambell ya
kawo ziyara ga sarki Kwasau, yace yazo kulla
abota ne dashi tare da samar da yarjejiniyar
zaman lafiya a tsakaninsu.

Abinda ya kara kwantar wa da Sarki Kwasau
hankali a game da turawa shine yadda suka
kame kwantagora tare da korar sarkin su abokin
hamayyarsa Sarki Ibrahim Nagwamutse a
shekarar 1901, sannan kuma suka kame sarkin a
wani faɗa da sukayi a Maska suka aike dashi
garin Lokoja aka tsare.

Wannan yasa hankalinsa ya kwanta dasu domin
sunyi masa maganin abokin hamayyarsa, suka
rinka kwararowa cikin zaria suna lamurorinsu.
Sai dai kwatsam babu aune, sai sarkin Zazzau
Kwasau yaji turawa Sun ayyana Zaria a matsayin
garin da suke iko dashi tare da kawo wani bature
mai suna Kaptin Abadie da akafi sani da suna
Mai jimina a matsayin Rasdan na garin, wannan
yasa sarkin cikin damuwa da ɓacin rai.

Ya shiga tunanin mafita a wannan lamari, gashi
yana da rauni wajen faɗa da turawa, sannan
sarkin Bidda ya aiko masa da gargaɗin kada ya
kuskura yace zai buga dasu, gashi kuma yana jin
kaskancine ya cigaba da zama a kasansu.

Don haka mafitarsa biyu ce, kodai ya hakura ya
zauna cikin kaskanci, ko kuma ya nemi taimakon
sarkin Kano Alu yayi yaki dasu.
Da tunani yayi zurfi, sai kurum ya zaɓi shawara
ta biyu..

Sarkin Zazzau Kwasau ya gamsar da zuciyarsa
cewa ko kaɗan ba zaiyi biyayya ga turawa ba,
tunda kasar sace ba tasu ba. Kuma ba addini
ɗaya gare suba. Don haka ya soma tunanin
mafita.

Akan haka ya aike wa Sarkin Kano Aliyu Babba
wasikar neman tallafi, yana mai shaida masa
cewar kiristoci sun yawaita a Zazzau, har kuma
sun yi kaka gida gareta tare da maisheta
mallakinsu, don haka yana neman mafita.

Ana haka sai rikicin kisan Kyaftin Moloney ya
bijiro.
Shi Kyaftin Moloney, shine Rasdan na Kyaffi. Ita
kuwa Kyaffi tana karkashin daular Zazzau ne a
lokacin. Kuma Sunan shugabanta wanda yake a
matsayin wakilin sarkin Zazzau a Kyaffi shine
Magaji Dan Yamusa.
Akace rannan Kyaftin Moloney ya tara mutane
yana musu jawabi, yana karanto turanci garesu,
wani bakin mutum kuma yana tafintan abin da
duk ya faɗa.
Magaji Dan Yamusa da tarin wasu jama'a duk
suna wurin.

Kwatsam sai rashin fahimta ya dabaibaye
tafintan kyaftin Moloney sakamakon tsauraran
kalmomin turancin da Moloney ke karantawa,
shikuma tafinta sai ya rinka yiwa turancin
fassarar kalma da kalma..

Akan haka ya faɗawa mutane cewar turawa keda
iko dasu, da komai nasu. Har matayensu ma
mallakin turawa ne.

Ance kafin a ankara sai ganin kan Kyaftin
Moloney akayi yana mirginawa a kasa, Magaji
Dan Yamusa ya saro shi.
Daga nan faɗa ya ɓarke tsakanin mutanen
Magaji da dakarun Moloney.
Daga karshe dai, Magaji Dan Yamusa ya gudu da
tawagarsa zuwa kano. Sarkin Kano Alu Babba
yaji daɗin abinda Bakonsa yayi, ya karrama shi
tare da bashi mafaka.

Duk da cewar akwai saɓanin inda wannan rikici
ya auku, shin a Keffi ne ko a Zaria, amma dai
turawa sun ɗora alhakin faruwar hakan akan
Daular Zazzau, tunda acikin ikon ta abin ya faru.
Sannan kuma sun damu matuka bisa abinda
Sarkin Kano yayi, wannan yasa suka sake ɗaura
aniya da kaimin tafiya kano da yaki duk da cewa
daman fakonta sukeyi.

Ganin haka sai Sarki Kwasau ya soma shirin
guduwa, saboda ya tabbatar abinda zai faru ba
mai daɗi bane.
Ya sake aikewa da wasika ga Sarki Alu Babba na
kano yana sanar masa da cewar lallai ba-suga ta
zama ba, haɗari gagarumi na zuwa garesu.
Sukuwa turawa sai suka ji tsoron idan Sarkin
Zazzau ya gudu da mutanensa, to fa zaije ya
haɗu ne da Sarkin Kano su kara karfi, don haka
sai suka baza dakarunsu akan hanyoyin Zaria
zuwa kano, zaria zuwa Katsina da Zaria zuwa
Bauchi, da niyar hana sarkin gudu ko kuma a
kame shi idan ya gudo.

Rannan sai kurum Rasdan na zaria watau kyaftin
Abadie, ya aikewa Sarki Kwasau gayyata domin
tattaunawa.
Sarki Kwasau ya fusata da haka, yace don me
kamar kyaftin Abadie kirista da yake a kasarsa
zai kira shi yazo, don haka ba zai jeba.

Daga nan sai turawa suka samu yadda suke so,
suka turo dakaru masu ɗumbin yawa cikin zaria,
suka yiwa fadar Sarki kwasau kawanya, sannan
suka shiga suka kama shi tare tafiya dashi
Wushishi. Acan suka tsare shi har Allah yayi
masa rasuwa.
Kuma an samu cewar Sarki Kwasau yayi
rubututtuka dangane da yadda aka kamashi da
halin daya tsinci kansa. Aciki akwai wata takarda
mai suna 'Nuzhatul Asiyr' inda ya rubuta cewar
turawa sun kama shine bisa kin yi musu biyayya,
a yammacin wata ranar jumua cikin kwanaki
goman karshe na watan Jumada Ula. (dai-dai da
19-satumba-1902).

Sannan kuma ya bayyana farin cikinsa bisa
yadda suka kamashi ba tare daya bi umarnin
suba ya zauna akarkadhinsu, har ma ya kamanta
kansa da mutanen Ashabul Kahfi a wata waka ea
aka samu ya rubuta.

Daga karshe, sai turawa suka naɗa Galadima
Salmanu sarkin Zazzau a farkon shekarar 1903.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by © Sadiq Tukur Gwarzo

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: