Sunday 18 March 2018

Karanta Kaji: Shin Dagaske ne Hadiza Gabon tayi Rawa Tsirara a wani Sabon Video???

Tura Wannan Zuwa Ga
Wani bidiyo ya bayyana da Sunan hadiza gabon ce tayi Rawa tsirara wasu suna ganin itace wasu suna ganin ba ita bace Haka dai wasu suke cewa ya kara tabbatar da itace domin an bayyana surarta da fuskarta harzuwa tafin kafarta.

sannan akwai wani gilas da take yawan sawa idan zata fita wani wajen Sannan sukace ita kanta Hadiza har yanzu bata karyata ba.

Haka ma wani ya shaida mana wannan rawa tsirara Hadiza gabon ce tayi. Yace Babu wata majiya mai kyau da ta bayyana Hadiza Gabon ta bayyana ba ita bace.
Wanda sanin kowane duk wanda ake zargi da aikata masha'a matsawar bai aikata ba, to fitowa fili yake ya kare kanshi koda baza'a yarda ba. Amma ita Hadiza shiru ake ji taki kare kanta.

Tayaya baza ace ita bace?

Amma daga bangaren jaruman fina finan Hausa wani jarumin Hausa Fim yace sabanin fahimta ne akan zargin da akeyiwa Hadiza Gabon na rawa da tayi tsirara.
Yace wannan karyane akayiwa Hadiza Gabon, kuma hadin kwamfiyutane kawai, amma ko kama da ita basuyi ba. Domin waccan ba bahausa bace ma, yaci gaba da cewa komai aka kwaso sai anufo 'yan Fim dashi wannan sharrine ai Hadiza ba mahaukaciya bace.

Haka dai wasu sukai ta gardama akan bidiyon Sakamakon yada jita jitar da akeyi akeyi da kuma musu akan rawar Hadiza Gabon cikin ikon Allah rumbun kannywood ya samu damar zantawa da Hadiza Gabon ga yadda hirar tasu ta kasance:

Muna ganin wani bidiyo da sunanki Wanda kike rawa a club har kina cire kayan jikinki zamuso muji gaskiyar lamari??

Ai ina tunanin ko ni arniyace bazan iya yin hakanba, komai za'a bani, sannan yaren da akeyi a wurin kamar Spanish Ne ko Mexican, ba yaren najeriya ko Niger, ko Gabon bane, sannan nafi wannan tsinanniyar girman jiki da sauran abubuwa, duk da yake abin mamaki ta kusa yin kama dani a fuska, amma bani bace ba. Bazan taba lalacewa irin haka ba.

Gabon ta ci gaba da cewa:

Nidai nasan bani bace kuma Allah da ya halliceni yafi kowa Sani, saboda haka ina ganin dani dakai duk musulmai ne ya kamata kayarda da abinda Na fadimaka.
Gabon ta yi kira da masu tura Bidiyon da su ji tsoron Allah sannan ta ce Allah (SWT) a cikin hujurat ayata shidda yana cewa idan munafukai sukazo maku da labari Ku tantanceshi kafin Ku gayawa wasu.

Kamar dai yadda ka tuntubeni din nan a matsayinka Na Dan jarida, don haka masu turawa din nan da sunbi wannan ayar sun tantance Labarin da ba suje suna turawaba, sannan mummunan abune yada tsiraci masoyana Su Sani bani bace, makiyana kuma suji Tsoron Allah Su Sani Allah ya tsare mutuncina bazasu iya zubar min dashiba.

Takaitaccen Tarihin Hadiza Gabon da Hotunan ta: Abubuwan da Yakamata Kusani dangane da Rayuwar Jaruma Hadiza Gabon - Karanta Yanzu Kaji

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki Mungode

Source: Sadikblog
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user