Tuesday 17 April 2018

Karanta Kaji Dalili: Babu wanda zai zama shugaban Nigeria sai dai idan shi barawo ne- Balarabe Musa

Tura Wannan Zuwa

Tsohon gwamnan jihar Kaduna a arewacin Najeriya Alhaji Balarabe Musa ya ce barawo ne kawai zai iya zama shugaban kasar.

Balarabe Musa ya bayyana hakan ne a yayin da mawallafin jaridar Sahara Reporters Omoyele Sowore, wanda ke son tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa, ya kai masa ziyara.

"Babu wanda zai zama shugaban Najeriya sai dai idan shi barawo ne ko kuma barayi ne suke goyon bayansa... kashi 99 cikin 100 na mutanen da ke rike da madafun iko duk barayi ne."

"Ta yaya mutum zai zama shugaban Najeriya in har bai fara zama barawo ba tukunna? Gaskiyar a bayyane take karara, idan ba haka ba waye zai iya kashe biliyoyin kudi a yakin neman zabe," a cewar Alhaji Balarabe.

Sai dai babu wata shaida da ya bayar da ta karfafa kalaman nasa.

Alhaji Musa ya ce sai dai a baya an samu shugabannin da suka yi mulkin kasar nan wadanda ba barayi ba inda ya ba da misali da jamhuriyya ta biyu, "Shagari ya mulki Najeriya kuma bai yi sata ba, amma a yanzu ba za a iya samun irin haka ba."

Ya kara da cewa dalilin da ya sa Najeriya ba ta samu ci gaban da ya kamata ba duk kuwa da irin dumbin arzikin da Allah ya yi mata shi ne, "rashin kyawawan tsare-tsaren tattalin arziki da na siyasa."

"A duk lokacin da aka kasa samun kyakkyawan tsari, to dole a samu kai a yanayin da Najeriya ke ciki a yau na bakin talauci da rashin hadin kai duk kuwa da dumbin arzikinta.
"Kuma idan ba a yi hankali ba sai abun ya fi haka muni nan gaba," in ji tsohon gwamnan.

Tsohon gwamnan na Kaduna ya dade yana sukar al'amuran gwamnatocin Najeriya da kuma yadda suke tafiyar da al'amuransu.

A baya ma ya sha sukar Shugaba Buhari da tsohon Shugaban kasar Olusegun Obasanjo.

Source by ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: