Tuesday 24 April 2018

Karanta Kaji: Kadan daga cikin Ciwon Hanta Da Alamominsa

Tura Wannan Zuwa Ga

Jama’a barkanmu da sake saduwa a wani makon a wannan
shafin da muke yin Tsokaci game da wasu abubuwa da
muka hango da za su amfani jama’a.

A wannan makon Ina so ne in shiga harkar kiwon lafiya, bisa
bincike da kuma shawarwarin masa harkar, inda za mu dan
yi tsokaci a ctar nan ta HEPATITIS.

08148507210 mahawayi2013@gmail.com

Idan aka ce Hepatitis, kai tsaye ana nufin ciwon Hanta a
Hausance. Sunan Cutar Ya Samo Asaline Daga Yaren Greek
(Girka); “Hepato”=Liber =Hanta, sannan “itis” dafi (prefid) ne
da ya ke nufin radadi A Kimiyance.
Hepatitis (wato ciwon Hanta) Yana da Ire-ire Har Guda Biyar;
Hepatitis A, Hepatitis B, Hepatitis C, Hepatitis D, Hepatitis E.
Cikinsu Akwai Masu dacewa da Kansu Bayan Sun Kama
Mutum, Wasunsu Kuma Sai An yi Magani. Haka Nan
Wasunsu Ba sa Tsananta, Wasunsu Kuma Suna Tsananta.

Sai dai Bincike Ya yi Nuni da Cewa; Hepatitis A, Hepatitis B,
da Kuma Hepatitis C su ne Suka fi Wanzuwa Tsakanin
Mutane.

Kowacce cikinsu Alamominta, Abin da Yake Haddasata,
Yadda Ake Maganceta, Hanyoyin Kamuwa da Ita, Yadda Ake
Kare Aukuwarta Ya Bambanta da Kowacce.
Kamar Yayda Bincike Ya Nuna, A Shekarar 2015 Akalla
Mutane Miliyan 11 4 Ne Ke Dauke da “Hepatitis A” a Duk
Fadin Duniya, Yayin da Akalla Mutane 343 Million Ne Ke
Dauke da “Hepatitis B”.
Haka Nan Akalla Mutane Miliyan 142 Ne Ke Dauke da
“Hepatitis C” A Duk Fadin Duniya. Akalla Mutane Miliyan
Daya ne Ke Rasuwa duk Shekara A Kuma Duk Fadin Duniya
Sanadiyyar Hepatitis.

A Kasar Amuruka Akalla Mutane 250,000 Ne Ke Kamuwa da
Wannan Cuta Duk Shekara, Yayin da Akalla Mutane 75 Ke
Rasuwa Duk Shekara Sanadiyar Hepatitis.

ALAMOMIN CIWON HANTA

-Hepatitis A:- Ciwon Ciki (Abdominal Pain), Zafin Jiki
(Feber), Amai (Bomiting), Tashin Zuciya (Nausea), Kasala
(Fatigue), Bakin Fitsari (Choluria), Yellow Idanuwa da Yellow
Fata (Jaundice Symptoms) da sauransu. Kwata-kwata Ba ta
tsananta Bayan Mutum Ya Kamu da Ita.

-Hepatitis B:- Zafin Jiki (Feber), Kasala (Fatigue), Yellow
Idanuwa da Yellow Fata da Idanuwa (Jaundice Symptoms),
Gudawa (diarrhoea), da Kuma Wasu Alamomi Masu Kama
da Cutar” Flu”. Wani Lokacin Ma Ba ta Nuna Alama. Tana Iya
Tsananta da Kaso 10 cikin 100 Na Mutanen da Suka Kamu
da Ita.

-Hepatitis C:- Iri Daya ne da Hepatitis B. Sai dai wannan tana
iya tsananta da Kaso 75-80 cikin 100 Na Mutanen da Suka
Kamu da Ita.

Tsawon Kwanaki Daga Lokacin Shigar Kwayar Cutar Cikin
Jikin Mutum Zuwa Lokacin Bayyanar Alamominta

(Incubation Period):-

-Hepatitis A:- Sati Biyu Zuwa Sati Bakwai (2-7 weeks).
-Hepatitis B:- Sati Shida Zuwa Sati Ashirin da Uku (6-23
weeks).

-Hepatitis C:- Sati Biyu Zuwa Sati Ashirin da Biyar (2-25
weeks).

Abubuwan Da Su Ke Haddasa Ciwon Hanta:-

-Hepatitis A:- Abun da Yake Haddasata Shi ne Wata Kwayar
Cuta da Ido Ba Ya Iya Gani Mai Suna” Hepatitis A
Birus” (HAB).
-Hepatitis B:- Hepatitis B Birus (HBB).
-Hepatitis C:- Hepatitis C Birus (HCB).

Sannan Yawan Shan Giya, Guba (todic substances), Matsalar
Garkuwar Jiki (Autoimmune diseases), Yin Amfani da
Kwayoyin Magani Ba Bisa Ka’ida Ba, Gado (Genetic cause),
da sauransu Na Iya Haddasa ciwon Hanta.
Hanyoyin Kamuwa Da Cutar Ciwon Hanta:-
-Hepatitis A:- Gurbatuwar Abinci Ko Ruwan Sha Wanda Ya
Gaurayu da Kashin Wani Mai Dauke da Cutar, Wanda Kwari
(Flies) Ke Yadawa, da Kuma Hada Jiki (Body Contact), da
Sauransu.

-Hepatitis B:- Idan Aka Sanya wa Mutum Jinin Mai Dauke da
Ita (Transfusion of infected blood), Yin Amfani da Allura Ko
Reza, ko wasu Karafa Masu Dauke da Kwayar Cutar (Use of
infected sharp objects). Haka ma Daga Uwa Zuwa Danta
(Mother to Newborn), Lokacin Saduwa da Mai Dauke da
Cutar (Sedual contact), da Sauransu.
-Hepatitis C:- Sanya wa Mutum Jinin Mai Dauke da Cutar
(Transfusion of infected blood), Amfani da Allura Ko Reza ko
wani Karfe Mai Dauke da Kwayar Cutar (Use of infected
sharp objects), Musayar Abubuwan Tsafta, Wanda Mutum
Daya ne Ya Kamata Ya Yi Amfani Da Shi ( Sharing of
personal hygiene implements), da sauransu.
Yadda A Ke Gano Cutar A Jikin Dan Adam:-
A na iya Gano Cutar Hepatitis (ciwon Hanta) Ne A Jikin
Mutum Bayan Alamunta Sun Fara Bayyana, Daga Nan Sai A
Yi Gwajin Jini Biyo Bayan Zukar Jinin Mutum Don A
Tabbatar.

Yadda A Ke Magance Cutar Hepatitis:-

Maza Garzaya Asibiti ko Wata Cibiya Magani Mafi Kusa Don
Saduwa da Ma’aikacin Lafiya da Zarar Ka Fara Jin
Alamomin Da Aka Ambata A Sama.
Hadurran Da Ke Tattare Da Wannan Cuta:-
Babban Hadarin Da Ke Tattare da Wannan Cuta Shi Ne;
Hantar Mutum Za Ta Iya Lalacewa ta Yadda Dole sai Dai A
Chanza Masa Wata, Idan Kuma Ba Allah Ne Ya Kiyaye Ba, to
Mutum Na Iya Rasa Ransa.

Yadda A Ke Kare Jiki Daga Aukuwar Cutar:-

A na Iya Kare Aukuwar Wannan Cuta ne ta Hanyar Yin Allurar
Rigakafi. Hepatitis Baccine sunan Allurar. Ita Kuma Ana Yi
wa Mutum Ne da Zarar An Haife shi, Sai Kuma A Sati Na
Shida, Sati Na Goma, da Kuma Sati Na Goma sha Hudu da
Haihuwar Jariri. A Dunkule Ana Kiran Allurar da Takwarorinsu
da Suna “Pentabalent Baccine”.
Sai Kuma Inganta Tsaftar Jiki Da Ta Muhalli, da Kuma Kiyaye
Hanyoyin Kamuwa da Cutar.
Saboda haka ne muke ganin yana da muhimmanci a garzaya
dakin binciken cututtuka domin mutum ya tabbatar ba shi da
ita. Idan kuma an bincika mutum ba shi da ita, to a je a yi
Allurar rigakafi.

Allaah Ya Kare Mu Daga Sharrin Wannan Cuta Da Sauran
Cututtuka, Amin.

Ina kuma amfani da wannan dama wajen mika godiya ta
musannan ga wani masanin harkar kiwon lafiya da ke Zariya
ta jihar Kaduna, Malam Muhammad Awwal Adam bisa
gudumawar da ya ba ni wajen wannan rubutun.

Source by ©Leadership A Yau
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user