Thursday 5 April 2018

Kalli Yadda A tona Asirin Wadanda su Kashe Janar Sani Abacha- Manjo Hamza Al-Mustapha

Tura Wannan Zuwa
Tsohon mai tsaron lafiyar, tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha yayi karin haske akan yadda shugaban nasa ya rasa ran shi. Hamza Al-Mustapha ya karyata zacen da ake na cewar wai Abacha Tufa (Apple) yaci ya mutu.

Ya ce tun ranar wata lahadi bakwai ga wata shida na shekarar alib dubu daya da Dari Tara da casa'in da takwas (7-6-1998) lokacin da Tsohon Shugaban kasa Sani Abacha ya gaisa da wani daga cikin masu tsaron shugaban kasar Palestine Yaseer Arafat a filin sauka da tashi na jirgin sama dake babban birnin tarayya Abuja hada hannun su keda wuya shikenan yanayin tsohon shugaban kasar ya canja.

Da gari ya waye likitan da yake duba shi yazo yayi mishi Allura ya kuma bashi shawara akan ya samu ya kwanta ya dan huta, da misalin karfe 9 na dare baki suka fara shigowa wurin shugaban, wanda ya shigo daga karshe shine Janar Jeremiah Timbunt Usteni wanda a lokacin shine ministan Abuja, sunyi ta hira dashi har zuwa karfe 3:35 na dare.

Da misalin karfe biyar 5 na Asuba sai daya daga cikin masu tsaron gidan shugaban kasar ya rugo a guje gidana yace maigida yana cikin wani hali mai ban tsoro saboda haka in zo ana bukatar gani na cikin gaggawa, a wannan lokacin sai nayi tunanin ko dai ana so ayi mana juyin mulki ne? Sai nace wa matata taje ta dauke wa Sojan hankali tace ya jira ni, ni kuma sai nabi ta kofar baya na je inda shugaban kasar yake; ina zuwa sai na tarar dashi yana Huci, numfashin sa na fita sama-sama, a lokacin bazai yiwu in taba shi ba kamar yadda tsarin dokar aikin mu yake. Banyi kasa a gwiwa ba sai naja da baya na kame na kwala mishi kira da karfi da nufin ya bani dama in taba shi, sau biyu ina yin haka amma baice dani komai ba.

Daga wannan lokacin sai na gane akwai babbar matsala sosai nan da nan na kira babban likitan shi Dakta Wali ya bayyana a cikin mintuna da basu wuce 8 ba, take ya yiwa maigida Allurori guda biyu daya a kirji shi daya kuma a kusa da wuya shi; ba a jima ba Likitan ya bayyana mini cewar gaskiya sai dai muyi hakuri domin maigida ya riga mu gidan gaskiya.

Daga wannan lokacin na umarci Dakta Wali ya jirani naje gidana don shirya wa dukkan matsala da zan iya fuskanta saboda mutuwar maigidan. Saboda haka a zance na gaskiya babu wata magana dake nuna cewar Tsohon Shugaban Kasa Sani Abacha guba yaci a Apple ya mutu; inji Manjo Hamza Al-Mustapha.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum
An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke
KARIN BAYANI
Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode
Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.
Source by ©Hausa Naija
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user