Monday 23 April 2018

Karanta Kaji: Kuskure 10 da akai acikin Film din KALAN DANGI tare da Sharhin Fim din

Tura Wannan Zuwa Ga

Hotuna daga Shafin Muryarhausa24.com

Tare Da: Saddika Habib Abba
No. 09097438402
Email habibsaddika@gmail.com
Suna: Kalen dangi
Tsara labari: Fauziyya D Sulaiman
Furodusa: Abubakar Bashir Mai Shadda
Director: Ali Gumzak
Kamfani: Tsamiya Inbestment

Jarumai: Ali nuhu, Aminu Sharif Momo, Sadik S Sadik, Sani
Idris Moda, Baballe Hayatu, Aisha Aliyu Tsamiya, Jamila
Nagudu, Hafsat Idris, Maryam Booth, Hajara Usman, Hadiza
Muh’d, Rabi’u Rikadawa, Ibrahim Mandawari.


Hotuna daga Shafin Muryarhausa24.com

A farkon fim din an nuna gidan wani attajirin mai kudi
Alh.Mu’azzam Canji (Ibrahim Mandawari) shine shugaban
‘yan caji yana zaune a gidansa tare da matarsa (Hajara
Usman) da kuma ‘ya’yansa Guda biyu mata Fadila (Jamila
Nagudu) da kuma kanwarta Kubra (Maryam Booth) an nuna
cewar ita Fadila ‘yar karyace ‘yar nuna son a sani ce sannan
kuma ta tsani talaka tana kyamatarsa in har ya rabeta, ita
burinta ta auri me kudi, sai ita kanwarta ta Kubra ita babu
ruwanta da nuna ita mai kudi ce sannan tana da saukin kai
kuma tana harka da talaka, sai kuma bangaren masu aikin
gidan (Rabi’u Rikadawa) shine mai gadin gidan da matarsa
Marka (Hadizan Saima) da ‘ya’yansu ‘yan mata guda uku
duk a gidan suke zaune akwai Samira (Aisha Tsamiya) da
kuma Salma (Fati Washa) da kuma (Hafsat Barauniya)
amma dukkansu ‘ya’yan makaryata ne burinsu suyi wa
samari karya sannan su auri mai Kudi guda daya ce rak ta
kirki ( Hafsat Barauniya) itace bata goyon bayan abinda suke
yi sakamakon hakan ya haifarmata da tsana a wurin
mahaifiyarta Marka saboda ita  ma mahaifiyar mai idon cin
naira ce burinta ‘ya’yanta su auri mai kudi  a gurin
mahaifinsu Mai gadi  kadai ta ke samun sassauci domin shi
sam baya bin bayan abinda suke yi matar tasa ta fi karfinsa
ne kawai, Salma da Samira har kwalliya suke su tafi jami’a
da wurare na shakatawa su hada baki da direban gidan
Mado (Musa Mai Sana’a) ya daukesu yana zazzagawa dasu
acikin mota domin masu kudi su gansu suce suna san su
idan sun dawo zu kawo kudi su bawa Mado don dama kafin
su fita sai sun yi ciniki.


Hotuna daga Shafin Muryarhausa24.com

Sai bangaren Adamu (Ali Nuhu) wanda yake aikin direba a
gidan Alh.Sabo (Baballe Hayatu) shima babu abinda yake yi
sai karyar arziki idan ya dauki mota sai yaje yana yiwa ‘yan
mata karyar cewa motarsa ce domin yayansa shine
shugaban ‘yan kasuwa a haka har suka hadu da Samira suka
fara soyayya domin kowannensu yana zaton me kudi ne. sai
kuma bangaren Habu (Aminu Sharif)wanda yake zaune cikin
talauci da kakarsa kullum mafarkinsa ya zamto mai kudi ya
dinga hawa manyan motoci sannan burinsa iri daya tare da
wani Abokinsa Tukur (Sadik Sani Sadik) wanda yake shi
almajiri ne ma amma babu abinda suka saka a gaba sai son
su zama masu kudi domin su dinga yiwa ‘yan mata karya
ana cikin haka sai wataran Habu yazo gida ya tarar ankawo
wa kakarsa kayan abinci na zakka ya tambayeta waya kawo
tace masa Alh. Sunusi ne nan fa Habu ya fara tsalle da
murnar ashe dama a danginsu akwai mai kudi bata taba
fadamasa ba tace masa ba d’an uwanta bane sun yi zaman
makota ka ne tare da kakarsa shi kuma a lokacin yana yaro
Habu ya fara tsalle da murnar ai dan uwansu ne duk da haka
ba da bata lokaci ba ya nemi kwatancen gidan Alh. Sunusi
ya je ya yi masa bayani da farko bai gane shi ba sai da ya yi
masa bayanin ai shi jikan mai kosai ne wadda ya kawo wa
zakka dakyar Alh. Sunusi ya gane sannan ya daukeshi aiki
har yake bashi motarsa yana hawa anan  Habu ya  sake
samun lasisin yiwa abokai da ‘yanmata karya abotarsu da
Tukur ta sa ke kulluwa a haka har Habu ya hadu da Salma
suka fara soyyaya ita a zaton ta mai kudi ne shi kuma a
zatonsa ‘yar Alh. Mu’azzam canji ce domin haka tace masa
haka suka cigaba da yiwa juna karya.


Hotuna daga Shafin Muryarhausa24.com

A bangaren gidan Alh. Sabo kuwa matarsa bata haihuwa har
ya yi yunkurin kara aure ya hadu da Fadila ta nuna cewar ita
bata harka da talaka domin duk ita a zaton ta talaka ne bata
san babban me arziki bane shi yasa taci zarafinsa har ya
hakura da neman aurenta wannan abinda ta yi masa shine
ya yi masa ciwo ya sanya suka hada baki da abokinsa Alh.
Sunusi domin a nemo yaro dan karya a biya shi yaje ya
yaudari Fadila da cewar shi mai kudi ne idan yaso bayan
auren sai ya bayyana mata kansa domin ta gane kuskurenta,
Alh. Sunusi ya sanya Habu ya nemo musu yaro Habu kuwa
ya nemo abokinsa Tukur su Alh. Sabo suka yaba da Tukur
sannan suka ba shi manyan motoci da kaya masu kyau
domin ya je ya sato zuciyar Fadila haka kuwa aka yi domin
Fadila tana ganinsa da wannan manyan motocin ta rude ta
amshi soyayyarsa suka kulla, ana cikin haka sai Alh. Sabo ya
kuma haduwa da kanwar Fadila Kubra itama ya nuna yana
sonta cikin girmamawa ta amshi soyyarsa.
Alh. Mu’azzam Canji kuwa ana haka  sai  ya umarci duk ‘yan
matan gidansa su fito da mijin aure kowacce ta fadawa na
ta saurayin kowannensu kuwa ya fito shi Adamu ya yi hayar
waliyyai da kayan aure Tukur da Habu kuwa Alh. Sabo ya yi
musu komai aka zo aka daura aure sai bayan an daura a
gurin fatin bikin kuma duk asiri ya tonu shi Tukur da kansa
ma ya ta shi ya bayyana ko shi wanene su kuma ragowar
wasu mata ne da Mado direba suka zo suka tona asiri a
gurin fatin hankalin kowannesu ya tashi har da masu cewar
sun fa sa.


Hotuna daga Shafin Muryarhausa24.com

Abubuwan Birgewa:

1- An yi amfani da kayan aiki masu kyau a labarin.

2- shirin ya tabo wata matsala da take faruwa a wannan
zamanin kuma an nuna wa masu irin wannan dabi’ar illar ta.

3- Jaruman kowannensu ya yi matukar kokari wurin isar da
sakon.


Hotuna daga Shafin Muryarhausa24.com

Kurakurai:

1- Akwai wurin da aka ga abun daukar sauti ya
fito a jikin Habu.

2- ‘ya mace ‘yar kwalliya ce amma kwalliyar da aka din ga
nu no wa a fuskokin duk jaruman mata a kodayaushe da
kowanne irin lokaci ta yi yawa don bazai yu ace kullum
mutum da kwalliya ba irin wannan babu wani ranar hutu an
nuna kamar ana nuna wa masu kallo su ga kwalliyar ne.

3-Bazai taba yi wu wa a gaske ace suna yin wannan
karyace karyacen kuma duk sun nemi aure a gida daya ba
amma asirinsu bai taba to nuwa ba, shin a auren babu
bincike da akayi? kawai auren aka yi?

4- Shin dama Mado direba mawaki ne ? ko kuma M.C ne? a
fim din direba kawai aka nuna yana yi amma sai ga shi an
ganshi a wurin biki yana M.C kuma yana waka.

5- Sutturar matan masu kudi manyan lesina ne da atamfofi
manya amma yanda ake kuranta kudin Alh. Mu’azzam gidan
da aka nuna yana ciki da sutturar da ‘ya’yansa da matarsa
suke sakawa ya yi Kadan a yanda ake bayyanar da arzkinsa.

6- Akwai wurin da Alh. Sabo ya ke fadawa Alh.Sunusi ya
hadu da Fadila a jami’a ta wulakanta shi a gaban mutane ta
saka ana kallonsa amma masu kallo sun san wurin da aka
nuna sun hadu ba jami’a bane kuma wurin babu kowa sai su
kadai amma har ya ce jama’a suna kallonsa.

7-Ka’ida idan za’ayi aure kowa yasan kafin akai ga daurin
aure ake zuwa ganin wurinda amarya za ta dauna amma sai
ga shi an nuna sai bayan daurin aure aka nuna an zo gidan
Habu ganin dakin Salma

8- Akwai wurin da Marka ta ke fadawa mijinta kayan
abincinsu ya kare har Hajiya take fadin ta dibi na su kowa ya
san masu aikin da suke zaune a gidan iyayen gidansu ba sa
siyan abinci a gidan ake fitar musu ballantana su Marka da
suke gidan tsahon shekara Ashirin da wani abu.

9- Habu da Tukur kowa ya san basu yi karatun boko ba
saboda babu hasali ma shi Tukur kolo ne amma sai ga shi
idan sun je wurin ‘yan matansu suna yi musu turanci mai
kyau bana dan koyo ba.

10- A irin arzikin Alh.Mu’azzam bai kamata ace direba daya
ba ne kuma motar da ake fita da ita daya ba ce  da har idan
aka sami matsala ‘yarsa za ta fita ta hau adaidaita sahu
kamar yanda Kubra ta yi lokacin da Mado ya ce Mota ta
sami matsala.

Karkarewa: Labarin ya kayatar kuma ya bai wa mutane
dariya, amma kuma karyace-karyacen da a ka nuna babu
yadda za a yi a gaske su faru kuma har a yi auren asiri bai
tonu ba. Wallahu a’alamu!

Source by Leadership A Yau and  Muryarhausa24.com
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user