Thursday 26 April 2018

Karanta Kaji: Kuskure 10 da akai acikin Film din KURU KURU tare da Sharhin Fim din

Tura Wannan Zuwa Ga

Suna: Kuru-Kuru
Tsara labari: A. U. Usman
Producer: Salihu Muhammad
Bada umarni: Nura Mustapha Waye
Kamfani: T.J multipopurse concept

Jarumai: Sadik Sani Sani, Maryam Jibrin Gidado, Bashir
Nayaya, Rahma MK, Adam M Adam, Hajiya Zulai, Alhassan
Kwalli, Baffancy, Mustapha B Maidala’ilu, Musa Mustapha da
Ibrahim Soja.

Sharhi: Saddika Habib Abba

A farkon fim din an nuna yadda ake zaman lafiya tsakanin
Saddam(Sadik S Sadik) tare da matarsa Islam(Maryam Gidado
cikin kwanciyar hankali da kaunar juna ana cikin haka sai Islam
ta fara rashin lafiya da suka je asibiti sai likita y tabbatar ai ciki
ne da ita har na tsahon wata hudu da kwanaki, nan da nan
labari yasha bam-bam Saddam ya tubure akan sharri likita ya
yi wa matarsa domin su duka-duka watansu daya rak da aure a
take ya dauketa suka tafi wani asibitin likita ta kuma aunawa
aka tabbatar wa da Saddam abinda wancan asibitin na baya
suka fada cikin tashin hankali Saddam da Islam suka dawo
gida ya fara tuhumarta akan wanene ya yi mata ciki?
Islam ta tabbatar masa akan cewar cikinsa ne Saddam yaki
aminta da hakan har ya dauketa ya maida ita gida Mahaifinta
(Bashir Nayaya) tare da mahaifiyarta suka kafe akan cewar
cikin Saddam ne domin ‘yarsu bata tsayawa da kowa sai shi,
Saddam kuma fafur yaki amincewa da cewar cikinsa ne har
mahaifin Saddam ya saka ‘yan sanda suka kama Saddam suka
fara azabtarda shi akan lallai sai ya fadi laifinsa amma Saddam
ya ki har sai da ta kai sun mika shi kotu sakamakon mahaifin
Islam alkali ne sai ya tura su kotun abokinsa aka shiga aka fara
shari’a Alkali ya tuhumi Saddam ya kara tabbatar da cewar shi
bazai amshi cikin da bana sa ba, alkali ya dogara da wata hujja
akan cewar Saddam ya taba daukar Islam ya kaita wani gida
kafin suyi aure to anan ne ya yi wannan lalata da ita shi kuma
Saddam ya aminta da cewar ya kaita gidan amma hira kawai
suka yi babu abinda ya shiga tsakaninsu Alkali yaki aminta da
abinda ya fada hakan tasa ya yankewa Saddam hukuncin
zaman gida yari na shekara sha biyu tare da tarar naira dubu
dari biyar abisa batawa Islam suna da ya yi da kuma rayuwarta
dungurun gun, nan da nan aka tasa keyar Saddam gidan yari
tun a wajen Islam ta fara nadama da tausayin Saddam hakan
tasa har ta kai masa ziyara gidan yari tana bashi hakuri amma
bai saurareta ba. ana cikin haka sai wani Barris.

Najib yazo abokin Saddam ne ya sami mahaifiyar Saddam ya
shai da mata cewar lokacin da abun ya faru yana kasar waje
amma tunda yanzu ya dawo baza su yarda ba za su daukaka
kara mahaifiyar Saddam ta aminta da hakan Barri.Najib ya
daukaka kara aka kai shari’ar kotun mahaifin Islam aka fara
shari’a Alkali ya tuhumi Saddam akan har a lokacin yana kan
bakansa? Saddam ya kuma cewa shifa bazai amsa laifin da ba
nasa ba, Alkali ya fara tuhumar Islam a lokacin labari yasha
bam-bam Islam ta tabbatarwa da Alkali shine ya yi mata
wannan ciki hankali kowa a kotun ya tashi Alkali ya fara gumi.

Islam ta fara bada labarin baya ashe asali ma ita marainiyace
mai shari’a ba mahaifinta bane kanin mahaifinta ne watarana
yazo ya tarar da ita gidan babu kowa sai ita tun a lokacin ya
fara haike mata bada son ranta bakuma duk sanda taki
amincewa sai ya ringa tsoratar da ita tun a lokacin ciki ya bulla
shine asalin samun cikinta amma Saddam ba shi da alaka
wannan cikin kuma don kowa ya kuma gamsuwa Isla har ta
nuna wani recording a wayarta a lokacin da mai shari’a yake
aikata lalata da ita domin ya kara zama hujja nan da nan kotu
ta hargitse shari’a kuma ta tashi Saddam ya fita daga zargi a
idon duniya bayan sun dawo gida maishari’a ya fara jinya yana
rashin lafiya har ya nemi yafiyar iyalinsa da Islam da Saddam
duk suka yafe masa domin ko shari’arsu ta farko ma shine
hada baki sukayi da wancan Akalin aka yankewa Saddam
wancan hukuncin na zalunci, duk suka ce sun yafe masa shi
kuma Saddam ya yi wa Islam alkawarin idan ta haihu zai
maida ita dakinta domin har a lokacin yana sonta kuma abinda
ya faru ba laifinta bane.

Abubuwan Birgewa:

1- Akwai darasi acikin fim din.
2- Labarin ya tafi har ya dire bai karye ba.

Kurakurai:

1- A farkon fim din yadda aka fara rubuto tsarin jerin sunayen
‘yan cikin fim din da sauran ma’aikatan fim din kwata-kwata
ba dai-dai bane rubutun don wani abun ma bazai karantu ba.

2-Akwai lokacin da Saddam yazo gurin mahaifiyarsa yake
fadamata cewar bazai iya cigaba da zama da Islam da ciki ba
sai akaji mahaifiyar Saddam tana cewa ya yi hakuri ya cigaba
da zama da ita shin mahaifiyar Saddam batasan dokar addini
bane? kuma an nuna jaruman suna tafarkin addinin
musuluncine domin a addinance auren mace da ciki haramun
ne to ita mahaifiyar Saddam duk batasan wannan bane ko
kuma wana hakurin take cewa Saddam ya yi tunda ita kanta ta
tabbatar danta yana da gaskiya.

3-Bayan asiri ya tonu an gane cewar Mai shari’a shine ya yi wa
Islam ciki amma masu kallo basu ga makomar shari’ar ba ko
kuma don shi Alkali ne shikenan doka bazata hukuntashi ba
idan ya yi laifi? yakamata ace an nunawa mai kallo yadda
abubuwan suka kasance domin ya gamsu.

4- An nuno Saddam a wani office tare da wani mutumi suna
muhawara akan shi bazai saka hannu a wata takarda ba domin
shi ba macuci bane shin menene amfanin wannan hotan tunda
bashida wata alaka da labarin fim din ko da shi ko babu shi
labari zai tafi dai-dai hasali ma ba’a sake nuno makomar
zancen ba.

5- ‘Ya’yan da aka nuna matar mai shari’a ta haifa a gaske
kwata-kwata bazata haifesu ba sun yi girma.

6- wasu daga cikin jaruman fim din kwata-kwata basu dace ba
kuma basu da kwarewa musamman lauyoyin fim din kwata-
kwata basu nuna kwarewaba basu taka rawar data dace ba
musamman lauyan daya ke kare Saddam a zamansu na kotun
farko.

7- ko’a gida rikici ya faru irin na su Saddam da Islam idan za’a
dai-dai ta abin za’ayi zama fiye da daya domin babban abu ne
wanda yake bukatar bincike da nazari amma sai aka ga zaman
da akayi a kotu na farko a shine aka gabatarda matsalar kuma
akayi bincike kuma aka yanke hukunci duk a rana daya shin
wacce irin kotu ce wannan kwata-kwata babu tsari acikinta.

8- An ga ‘yan sanda akan titi kawai sun sha gaban Saddam
sun kama shi da bindigogi kamar wanda ya yi fashi kuma sunje
sun garkameshi wannan abun babu tsari aciki kamata ya yi ace
an je har gida an same shi idan ma tafiyar zasu yi dashi amma
ba’a kan hanya yadda suka tareshi ba.

9- Lokacin da aka nuno Saddam da dansanda yana tuhumarsa
a office ana jiyo sautin hayaniyar ma’aikatan fim din.

10- Kayan aikin fim din kamar camera da daukar hoto da abin
daukar sauti ba wani fita suka yi yadda yakamata ba a fim din.

Karkarewa:
Labarin akwai darasi aciki amma akwai tarin kura-kurai wanda
suka so su kashe labarin wanda da an lura dasu da fim din yafi
haka kyau. Allahu a’alamu.

Source by ©Leadership A Yau
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user