Friday 27 April 2018

Karanta Kaji: Yadda Buhari ya kwashi dala miliyan 462 ba tare da sanin Majalisar Tarayya ba

Tura Wannan Zuwa Ga

Tabbatattun bayanai sun nuna cewa Shugaba Muhammadu
Buhari ya rattaba hannun amincewa a kwashi dala milyan 462
daga asusun gwamnatin tarayya, aka bai wa Gwamantin
Amurka domin sayo jiragen yaki 12, ba tare da amincewar
Majalisar Tarayya kamar yadda dokar kasa ta bayyana ba.

Shugaba Buhari dai ya yi rantsuwa da Alkur’ani cewa ya yi
alkawarin zai yi aiki a kan yadda ka’idar tsarin mulkin Najeriya
ya gindaya. Kuma irin wannan abin da ya yi ne ya ce ya zo ya
gyara irin wanda gwamnatin baya ta rika yi.

Idan za a iya tunawa, Gwamna Ayo Fayose ya ce bai yarda a
cire kudin ba, domin wayau ne gwamnatin Buhari za ta yi, don
ta kwashi kudin kamfen na zaben 2019, shi ne ita ma ta cire
kudi da sunan cinikin makamai.
Dokar Najeriya ta ce Shugaba ba shi da ikon sa hannu ya
kwashi kudi ko bayar da iznin a kwasa daga Asusun
Gwamnatin Tarayya, ba tare da amincewar Majalisa ba.

Sai dai kuma wata wasika da shugaba Buhari ya aika wa
Majalisar Tarayya daga baya, ya fake da cewa Gwamnatin
Amurka ce ta bayar da wa’adin wasu kwanaki, cewa kada
Najeriya ta wuce kwanakin ba tare da ta bayar da kudin ba.
Wannan shi ne dalilin da ya sa Buhari ya yi riga-malam-
masallaci ya sa a hannu a cire kudaden Majalisa ba ta sani ba.

Buhari ya aika da wasikar ranar 13 Ga Afrilu, amma sai ranar
17 Ga Afrilu wasikar ta je ofishin Kakakin Majalaiar Tarayya.
Sai dai kuma wasikar ta nuna cewa sanarwa ce kawai aka yi,
domin an rattaba cewa an rigaya an sa hannun cire kudaden,
da kuma dalilan da suka sa aka yi gaggawar cire su ba da izni
ba.

A cikin wasikar da Buhari ya aika wa Majaisar Tarayya, ya
shaida wa Saraki da Dogara cewa tunda dai dama kowa na
sane da wannan batu tun bayan wani taro da ya yi da
gwamnoni, cikin watan Disamba, inda suka nuna amincewa a
cire kudin, to tuni an ma cire kudin an kuma tura a cikin
asusun gwamnatin kasar Amurka
Buhari a ce za a sayo jiragen yaki ne guda 12, saboda matsalar
tsaro. Adadin kudaden inji Buhari sun kai dala miliyan
496,374,470.00, watau kwatankwacin naira biliyan
N151,394,421,335.00 cif da cif.

Daga nan sai ya roki majalisa da cewa, tunda dai ya rigaya ya
cire kudin ba tare da amincewar su ba, ya na rokon su rubuta
adadin kudaden a cikin kasafin kudi na 2018 kawai, maganar ta
wuce.
Daga nan sai ya ce sauran kudin kuma da ba a rigaya aka cire
ba, tunda dama dala biliyan daya ce za a cira, to nan gaba
idan sauran hukumomin tsaro sun gama gabatar da abubuwan
da suke bukata, sai shi Shugaban kasa ya gabatar wa majalisa
da bukatun, ba zai yi azarbabin cirar kudi nan gaba ba tare da
ya tsallake majalisa ba.

Idan ba a manta ba, farkon watan nan ne Ministan Tsaro
Mansir Dan’Ali ya bayyana wa manema labarai a fadar
Shugaban Kasa cewa Buhari ya sa hannun cire makudan
kudaden.
Wannan magana ta tashi hankulan jama’a da dama a kasar
nan, inda nan da nan Majalisar Tarayya ta ce ita dai Buhari bai
sanar da ita ba, kuma bai nemi iznin ta ba.
Nan da nan hadiman Buhari suka fara bayanin cewa ai ba zai
cire kudin ba tare da ya sanar da majalisa ba.

Amma abin mamaki, sai ga shi bayanai sun nuna cewa an ma
cire kudin, kuma sai bayan da aka cire ne sannan Buhari ya
aika wa majalisa takardar sanar da cire kudin, amma ya roke
su da cewa a tari gaba.

Source by ©Premium Times Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: