Friday 27 April 2018

Karanta Yanzu Kaji: Shin dagaske ne Gwamnati ta tuhumi Sheikh El-Zakzaky da laifin kisan kai a Nigeria ???

Tura Wannan Zuwa

Gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da kara a gaban kotu inda ta
ke tuhumar jagoran kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta 'Yan Shi'a
Sheik Ibrahim El-Zakzaky da kisan wani soji.

Kisan sojan na cikin tuhumce-tuhumce takwas da gwamnatin
ta shigar a gaban kotun a kan malamin da wasu karin mutum
uku.

Sauran mutanen biyu da ake zarginsu tare sun hada da Yakub
Katsina da Sanusi Koki - shugabannin kungiyar a jihohin
Katsina da Kano.

Sojan mai mukamin kofaral na cikin ayarin da ke tare da
Hafsan Sojin kasa Janarar Tukur Burutai lokacin da suka yi
arrangama da 'yan shia a garin Zaria a ranar 12 ga watan
Disamba na shekarar 2015.

Daga bisani kuma sojoji sun kai wa jagoran 'yan Shi'a hari a
gidansa da ke Zaria inda suka kashe mutum sama da 300.

Sai dai magoya bayan malamin sun ce mutanen da aka kashe
musu sun doshi 1,000, sannan an yi awangaba da wasu da
dama.

Tun daga lokacin ne hukumomi ke tsare da Sheikh Zakzaky da
matarsa Zinatu a wani wuri da ba a bayyana ba, duk da cewa
kotu ta bayar da izinin a sake su a lokuta daban daban.

Gwamnati jihar Kaduna ta kuma bayyana kungiyar a matsayin
haramtaciyya kuma ta hanata yin taro a cikin jihar.

A farkon watan da mu ke ciki magoya bayan Sheikh Zakzaky
suka fara zanga-zanga cikin lumana a kowace rana inda suka
nemi a sako mu su jagoran nasu.
Ibrahim El-zakzaky ya yi shekara biyu yana tsare ba tare an
gurfanar da shi a gaban kotu ba, in ban da yanzu da
gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da kara a gaban kotu.

Gwamnatin Najeriya ta ce tana tsare da jagoran 'yan na Shi'a
da kuma matarsa soboda tsaron lafiyarsu.

A baya ta gabatar da su a gaban 'yan jarida inda malamin ya ce
yana cikin koshin lafiya.

Ko da yake daga bisani lauyansa Femi Falana ya ce an shirya
taron manema labaran ne ba tare da sanin jagoran 'yan Shi'ar
ba.

Rahotanni sun ce idan aka samesu da laifi za a iya yanke mu
su hukuncin kisa.

Source by ©BBC HAUSA

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: