Saturday 14 April 2018

Karanta Kaji: Kuskure 6 da akai acikin Film din HANGEN NESA tare da Sharhin Fim din

Tura Wannan Zuwa Ga

Suna: Hangen nesa
Tsara Labari: Yakubu M. Kumo
Furodusa: Usman Mu’azu
Bada umarni: Nazifi Asnanic
Kamfani: MM Haruna English Academy

Jarumai: Adam A Zango, Rahma Sadau, Hauwa Maina, Shehu Hassan Kano, Maryam CTB, Isa Bello Ja, Bashir Nayaya, Ibrahim Mandawari, Nuhu Abdullahi da Aina’u Ade.

Sharhi: Saddika Habib Abba

A farkon fim din an nuna Zarah (Rahama Sadau suna soyyaya tare da Nazir(Adam A Zango) har ma an yi musu baiko tsakaninsu,  a wani bangaren kuma an nuna Alhaji Habibu (Ibrahim Mandawari) tare da abokansa ‘yan siyasa suna taro wanda har a lokacin abokan aka yanke shawarar an tsaida shi takarar gwamna a jihar, bayan an kammala taro sun taho hanya shi da abokinsa Alhaji Umar (Shehu Hassan Kano) sai Alhaji Umar ya fuskanci cewar Alhaji Habibu yana cikin damuwa ya tambayesa dalilin damuwarsa sai ya fadamasa cewar shi babbar matsalarsa itace gashi an tsaida shi takara kuma amma matarsa bata jin turanci yaya zaiyi da ita a duk lokacinda aka yi bakin turawa wanda basa jin hausa ko kuma idan ana yin wani muhimmin taro wanda a gurin baza’a yi magana da hausa ba shi wannan shine babbar damuwarsa sai abokin ya bashi shawara akan ya saketa kawai ya kawo mai jin Turanci sai Alhaji Habibu yace shi bazai saketa ba domin Matarsa tayi masa halacci tun bashi da komai take tare da shi saboda  har ma akwai lokacinda aka koreshi daga aiki itace wadda taringa ci da su ba tare da ta taba fadawa kowa ba saboda haka shi bazai iya sakinta ba sai Alhaji Umar yace masa to tunda haka ne to ya karo mata kishiya wadda ta iya turanci idan yaso ita kishiyar sai a dinga damawa da ita a harkokin gwamnati ita kuma uwar gidan tunda bata jin turanci sai ta dinga kulawa da harkokin gida a take Alhaji Habibu ya karbi wannan shawarar bayan yadawo gida ya fadawa matarsa Amina (Hauwa Maina) cewar an tsaida shi takara amma sakamakon bata jin turanci zai karo wata matar wadda take jin turanci ita kuma sai ta cigaba da kulawa da da harkokin gida Amina ta daga hankalinta domin ta fadamasa ita tafiso ta cigaba da mallakar mijinta ita kadai amma duk da haka bata ci mutuncin mijinta ba saboda an nuna ita macece mai hangen nesa da sanin yakamata acikin zamantakewar rayuwar aure don wasu matan ma ‘yan uwanta wanda ma suka yi karatun bokon har zuwa suke yi gurinta neman shawarwari akan zamankewarsu ta aure saboda ita tanada wannan gogewar shiyasa ta cigaba da lallaba mijinta akan kada ya yi auren amma fafur ya bijire mata akan shi lallai sai ya yi sai ta rabu da shi ya tafi ya cigaba da maganar neman aurensa har shi wannan Abokin nasa Alhaji Umar ya yi masa shawarar akan ya nemi auren ‘yar yayansa wato Zarah domin tana jin turanci don a kasar waje ma ta yi karatu Alhaji Habibu ya amince da hakan bada bacin lokaci ba har Alhaji Umar yaje gidansu Zarah ya sanar musu da halin da ake ciki Zarah da iyayenta suka yi murna sosai saboda suna ganin ‘yar su zata zama first lady Zarah ta kori Nazir ta fadamashi halin da ake ciki hankalin Nazir ya yi matukar ta shi amma sai ya hakura ya rabu da ita, mutanan unguwar su Zarah ko ina ya dauka zata auri dan takarar gwamnan jihar har mata sun fara yi mata tururuwa tana yin taro da su domin tuntuni har an yi mata baiko da Alhaji Habibu, duk abinda yake faruwa a gari zan tukan suna komawa kunnen Amina har ta kai wataran ‘ya’yanta Rashida da Yassir(Nuhu Abdullahi) sun ji labari a gari sun zo sun sami mahaifinsu akan ya janye auren Zahra amma fafur ya ki janyewa.

Wata rana ‘yan jam’iyyarsu Alhaji Habibu sun hada wani gagarumin taro na duk ‘yan takarkaru kowanne da matarsa kuma matan ma zasu yi bayani amma da turanci hankalin Alhaji Habibu ya tashi a gurin taron domin yasan matarsa bata jin turanci ya tashi ya kirawota gefe yace ta ta zauna a waje kada ta shigo shi kuma zai san abinda zai je ya fadamusu Amina da taki yarda amma daga karshe sai ta yarda ta zauna amma yana shiga ciki kawai sai tabi bayansa  ba tare da ya sani ba shi kuma adaidai lokacin ya karbi Mic yana yiwa mahalarta taron karyar cewa bata da lafiya ita kuma a lokacin ta kawo kai ta karbi Mic hankalinsa ya yi matukar tashi ganin cewar zata kunyata shi, ya koma ya zauna Amina ta fara bayani da turancin sahihi kuma bayanai masu ratsa jiki akan nawin shugabanci har ta kawo aya da hadisi tana ta zubda hawaye sannan a karshe tayi wa maigidanta nasiha akan yaji tsoran Allah akan nawin da yake shirin hawa kansa a take jikin kowa a gurin ya mutu harda masu hawaye aciki harda maigidan nata aka tashi daga taro kowa ya watse, bayan sun dawo gida Alhaji Habibu ya jinjina mata akan abinda tayi ya nuna farin cikinsa akai sosai sannan ya yi mata alkawarin cewar ya janye aurensa da Zahra tunda dama matsalar turanci ce kuma gashi ta iya kuma ya tambayeta a ina ta koyi turanci acikin karamin lokaci? Amina ta yi farin ciki sosai sannan ta fadamishi cewar wata kawarta ce proffessor Rukayya(Aina’u Ade)ta yi mata hanyar wata makaranta ta koyar turanci mai suna MM Haruna English academy to anan ta koya Alhaji Habib ya yabawa makarantar sosai. a bangaren gidansu Zarah kuwa Alhaji Umar yaje ya fadamusu an fasa aure hankalinsu ya yi matukar tashi Zarah kamar zata haukace kuma rigima ta kacame musu da Alhaji Umar domin ya ranta musu kudi an sayi kayan daki da zummar idan aka yi aure abinda ta wawura a gwamnati za’a biya shi kudinsa, daga bisani kuma Nazir ya kawo wa Zarah  katin bikinsa tare da ‘yar gidan Alhaji Habib ya fadamata cewar ita bata zama first lady din ba amma shi ga shi yanzu ya zama dan first lady don ‘yar gidan Alhaji Habib zai aura, Zarah tana jin haka ta sake gigicewa sosai.

Abubuwan Birgewa:

1- Fim din ya yi ma’ana sosai, sannan ya ilimantar ta kowanne fanni, addini da boko, kuma akwai darasi mai karfi a ciki musamman a fannin zamatakewa irin ta auratayya.

2- Labarin ya sami cikakken tsari mai kyan gaske sannan ya tafi tiryan tiryan bai karye ba har ya dire.

3- An yi amfani da kayan aiki masu kyau da gurare wanda suka dace da labarin.

4-Jaruman sun matukar kokari gurin isar da sakon musamman Alhaji Habibu da Amina.

Kurakurai:

1- Wasu daga cikin wuraren da akai magana da turanci kamar in da Yassir da Rashida suke magana da babansu acikin harabar gidansu ba’a fassarawa mai kallo da hausa ba a rubuce ta yanda kowa zai fahimta saboda fim din na hausa ne.

2-Akwai wasu wuraren an ji Yassir da Rashida suna yiwa Amina turanci tun kafin taje ta koya menene ma’anar yin hakan tunda sun san bata iya ba? ko dama suna fada ne don ‘yan kallo suji ba don  Amina ta fahimci me suke cemata ba?

3- Akwai lokacin da Alhaji Umar suke magana a office tare da Alhaji Habibu aka bugowa Alhaji Umar waya ya daga akan screen din wayarsa da aka hasko bai nuna cewa waya ake amsawa ba kawai kara ta ya yi.

4- Mahaifiyar Zarah ta sami tuntuben harshe a gurin da wani ya shigo gidansu ya sameta tare da Zarah ya fadawa Zaran  cewa ta yi bakin mata a waje sai akaji mahaifiyarta tace a fadamusu su shiga dakin maigadi su jira ta shin mantawa ta yi ta fadi hakan a maimakon tace su jira kusa da dakin maigadi? domin yanda ta fada din sam bai kamata ba yaya za’ayi suna mata wata’il ma harda matar aure amma ace su shiga dakin maigadi su jira ‘yar gida.

5- Shin Alhaji Umar ba shida iyali ne? a matsayinsa na babban mutum yakamata ace ko sau daya ne an nuno su ko kuma an fadesu a baki.

6- An fada cewar Zarah tayi karatu a ingila amma sai gashi an ji iyayenta suna rigima da Alhaji Umar akan cewar ya ranta musu kudi sun sayi kayan daki, shin wanda yakai ‘yarsa karatu ingila shine har wani zai ranta masa kudin kayan daki?

Karkarewa:

Fim din ya yi matukar kyau kuma ya yi ma’ana amma akwai abubuwan da ya kamata a kuma inganta su. Allahu a’alamu.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by ©Leadership A Yau

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: