Monday 23 April 2018

KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN JARUMA AISHA ALIYU TSAMIYA: ABUBUWAN DA BAKU SANI BA GAME DA JARUMA AISHA ALIYU TSAMIYA

Tura Wannan Zuwa Ga

Hoto daga shafin muryarhausa24.com

A’isha Aliyu, wacce aka fi sani da lakanin ‘Tsamiya,’ yau
shekarunta uku ke nan da fara harkar fim din Hausa, amma
sunanta ya zama tamkar ruwan dare gama duniya, musamman
ganin yadda ta samu amsuwa ga ’yan kallo. Ta ta’allaka wannan
shahara tata ga yadda take maida himma da kokari wajen
fuskantar sana’arta.

Haka kuma, ’yar wasan ta bayyana cewa ba
za ta yi aure ba har sai ta samu gamsasshen ilimi, ke nan bayan
ta kammala makaranta.


Hoto daga shafin muryarhausa24.com


Ga shi kin samu amsuwa a harkar fina-finan Hausa, yaya haka
ta faro?

A lokacin da na kudurta cewa in fara harkar fim din Hausa, ban
taba tsammanin zan shahara ba cikin kankanen lokaci. Amma
bayan da fim dina na dakin Amarya ya fito, shi ke nan sai
sunana ya daukaka, na samu amsuwa. Daga nan ne fa sai
furodusoshi suka yi ta ribibina, suna saka ni a fina-finansu. Ai
fa shi ke nan sai na zama ko’ina an san ni, ta kai ga babu
yadda za a yi in shiga wani wuri ba tare da masoya suna kula
ni ba. Za ka ji suna kiran sunana, musamman ma idan na shiga
kasuwa ko wata matattarar jama’a. Na zama ko’ina a
Arewacin Najeriya an san ni kuma ana kauna ta.


Hoto daga shafin muryarhausa24.com


Wadanne fina-finai ne suka zama linzamin nasararki?

Fina-finai biyu, wato fim din So da dakin Amarya, su ne suka
zama silar shahara ta. Na ta’allaka nasarar kuwa ga darakta,
domin kuwa na sanya wa raina cewa bari in yi iyaka kokarina
wajen bin umurnin duk da daraktana ya ba ni. Lokacin da fina-
finan biyu suka fita, na sanya ina kallo, sai na yi ta mamakin
kaina, na ga kamar ma ba ni ba ce ke yin wannan wasa. Babu
shakka na yi matukar gamsuwa kuma na yi mamakin yadda na
fito a fim din dakin Amarya. Haka kuma na ji dadin yin wasa
tare da manyan ’yan wasa, kamar Ali Nuhu da Halima Atete.

Fim din So shi ne ma na fi kauna, musamman inda na fito tare
da shahararren dan wasa, Adam Zango. Babu shakka fim din
ya kayatar, musamman ma na gamsu ne da labarin fim din,
wanda nake ganin kamar gaskiya ne, ba kirkirarre ba.


Hoto daga shafin muryarhausa24.com

Me ya ja ra’ayinki ga harkar fim?

Babban abin da ya ja hankalina kuma na ji ina son shiga harkar
fim shi ne, domin ina son in shahara, musamman domin in
zama mai taimakon gajiyayyu da mabukata. A rayuwata, ba na
gajiyawa da yin kyauta ga mabukata. Na fito daga cikin
al’ummar da ke cikin wahala da bukata, don haka ya zama
wajibi a kaina in taimaka masu da abin da Allah Ya hore mani
ga mabukata. Nakan bayar da abinci da tufafi da kudi ga
mabukata a inda nake zaune, wato Kano, kamar kuma yadda
nake ziyartar sansanin ’yan gudun hijira da ke nan Kano.

Na yi
haka a lokacin azumin Ramadan, musamman domin mutanen
su samu saukin ibada. Duk da cewa ni ba attajira ba ce amma
dai ta sana’ar da nake ta fim, nakan samu dan abin da zan
agaza wa gajiyayyu da mabukata, komai kankantarsa.


Hoto daga shafin muryarhausa24.com

Me ke burinki a wannan harka ta fim?

Duk da cewa ina samun nasara a fagen wasan fim, babban
burina a harkar nan shi ne in zama darakta, mai ba da umurni
a fina-finai, kamar dai yadda Muhibbat Abdussalam take yi. Ina
da burin in ci gaba da karatu, domin zurfafa ilimina. A yanzu
haka na samu shiga Jami’ar North-West da ke Kano. Ina
bukatar in samu isasshen ilimi, kafin daga bisani in yi aure.
Amma duk da haka na dogara ga Allah kuma na yadda da
kaddara, wanda al’amarin na iya canzawa, yadda Allah Ya so.

babu mamaki a kan haka in samu mijin da ya dace, kafin in kai
ga kammala karatuna. Amma dai burina in kammala tukunna
kafin in yi aure.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode







Source by ©Aminiya and  Muryar Hausa24
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user