Sunday 27 May 2018

Kaga wannan hoton kuwa: Kalli Hotan Da Ronaldo yawa Muhammad Salah kallon 'Zaka sani'

Tura Wannan Zuwa

Wannan wani hoto ne da aka dauka kamin fara wasan jiya tsakanin Real Madid da Liverpool, Cristiano Ronaldo da Muhammad Salah sun hadu a kan hanya inda Ronaldon yawa Salah kallo me cike da alamar tambaya. Hoton ya dauki hankulan mutane sosai.

Sunan Salah dai ya daukaka sosai a kakar wasa ta bana saboda irin rawar ganin daya taka a kungiyarshi ta Liverpool wanda har takai ana kamantashi da Ronaldo da Messi.

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce raunin da Salah ya ji a gasar Zakarun Turai ya yi muni sosai, a yayin ake fargabar dan wasan ba zai buga gasar cin kofin duniya ba.

Ko da yake hukumar kwallon kafar Masar na da tabbacin cewa dan wasan zai murmure kafin soma gasar cin kofin duniya da za a fara a 14 ga Yuni.

Salah ya fice fili yana kuka bayan Sergio Ramos ya ma shi keta a wasan karshe da Real Madrid ta doke Liverpool 3-1.
"Raunin ya yi muni sosai," in ji Klopp.
"Yana kwance a asibiti za a yi hoton kafadarsa, raunin ya yi muni."

Amma a sakon da ya wallafa a twitter a ranar lahadi, Salah ya ce yana da tabbacin zai tafi Rasha.

It was a very tough night, but I'm a fighter. Despite the odds, I'm confident that I'll be in Russia to make you all proud. Your love and support will give me the strength I need. pic.twitter.com/HTfKF4S70e
— Mohamed Salah (@MoSalah) 27 Mayu, 2018

A nata bangaren, hukumar kwallon Masar ta ce an yi wa Salah hoto, kuma ya nuna ya samu targade ne a kafadarsa, tare da bayyana cewa tana da tabbacin zai murmure kafin gasar cin kofin duniya.

Salah wanda ya ci wa Liverpool kwallaye 44 a bana, ya yi kokarin ya ci gaba da wasa bayan ketar da Ramos ya yi masa ana minti 26 da wasa.

Amma dole daga bisani ya fice fili, inda Adam Lallana ya karbe shi.

Daga baya Ramos ya wallafa sakon fatan alheri ga Salah tare da masa fatan samun sauki, inda ya ce kwallo ta gadi haka.

El fútbol te enseña la cara más dulce a veces y la más amarga otras. Ante todo somos compañeros. Pronta recuperación, Salah. El futuro te espera.||Sometimes football shows you it's good side and other times the bad. Above all, we are fellow pros. #GetWellSoon @MoSalah
— Sergio Ramos (@SergioRamos) 27 Mayu, 2018

Magoya bayan Salah ba su ji dadi ba
Salah wanda ya fi yawan cin kwallaye a Premier ya samu farin jini a kakar bana.
Magoya bayan dan wasan musamman a kasarsa Masar hankalinsu ya tashi, inda suke fatar dan wasan zai murmure da wuri domin jagorantar tawagar kasar a Rasha.



Masar za ta tafi gasar cin kofin duniya a karon farko bayan shekaru 28, kuma 'yan kasar na ganin Salah zai jagoranci kasar ga nasara.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©Hutu Dole and Bbc Hausa
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user