Monday 28 May 2018

Karanta Kaji: Kuskure 9 da akai acikin Film din ABBANA tare da Sharhin Fim din

Tura Wannan Zuwa Ga


Tare Da: Saddika Habib Abba
Suna: Abbana
Tsara labari: Yakubu M Kumo
Furodusa: Abdul Amart
Director: Sadik N. Mafiya
Kamfani: Amart Entertainment

Jarumai: Ali Nuhu, Sadik Sani Sadik, Aisha Aliyu Tsamiya, Asma’u Sani, Tijjani Asase, Tanimu Akawu, Rukayya Dawayya da Basma Baba Hasin

A farkon fim din an nuna Nabila (Aisha Tsamiya) akwai matukar soyyaya da shakuwa tsakaninta da baban ta (Ali Nuhu) sai kuma mahaifiyar ta Laila wadda aka nuna tana jiyya, sannan akwai saurayin ta wanda aka nuna suna soyyaya tare Umar (Sadik Sani Sadik) har lokacin bikinsu ya zo anfara biki duk wasu shirye-shirye sun kammala ana cewa gobe za a daura musu aure sai ciwon Babar ta ya tashi ta yanke jiki ta fadi suka dauke ta suka kai ta asibiti, ana zuwa likita ya tabbatar musu cewar ta rasu wannan rasuwa da ta yi daga nan maganar daurin aure ta tsaya saboda tashin hankalin da suke ciki, dalilin mutuwar Laila shi ne abin da ya saka Nabila da baban ta a cikin tashin hankali soboda son da suke yi mata har ta kai ga Baban Nabila ya yanke jiki ya fadi likita ya tabbatar musu da cewar barin jikinsa ya shanye hawan jini ya tashi.

Tun daga lokacin rayuwar Nabila ta shiga jikin garari ba ta da wani farinciki, saurayin ta Umar kodayaushe yana rarrashin ta har ta kai ga likita ya sallame su daga asibiti sun koma gida wahalhalun Baban Nabila suka rubanya tunda duk abin da ake yi masa a asibiti yanzu ita za ta yi kuma ta ce akwai bukatun da za ta yi masa wanda haramcine idan takai hannunta kansa,
sakamakon wannan ne ya saka Nabila ta yanke hukuncin ita Abban ta za ta aura wannan furuci na Nabila da ta yi ya yi matukar jefa Umar cikin shakku da mamakin na cewa kanta daya kuwa? Nabila ta kafe akan burinta Baban Nabila ya nuna rashin amincewarsa har ta kai ga ya fara tunanin baya a kan cewar asali Nabila ba ‘yarsa ba ce hasali ma shi bai taba haihuwa ba kuma asalinsa ba dan garin ba ne shi ya sa ba shi da kowa a garin asalin yadda ya samu Nabila tun tana karama Nabila ta kasance marainiya gaba da baya, kuma mahaifin ta kafin ya rasu mai arziki ne sosai lokacin da ya rasu ya barta a hannun kannensa wanda suke uba daya. Bukar (Tijjani Asase) suka handame dukiyar Nabila sannan kowannen su ya azabtar da ita a gidajensa ko abinci ba sa ba ta harta kai ga kowannen su ya ce shi ba zai iya rike Nabila ba har ta kai ga suna muhawara tsakaninsu a kofar gida kowanne yana turowa kowa Nabila ya ce ba zai rike ba a gurin Abban Nabila ya zo wuce wa ya fada musu shi yana so su ba shi amma yana so suje wurin ‘yan sanda domin a yi rubutu suka shaida masa cewar su kawai ya karbeta babu wani rubutu amma duk da haka bai yi kasa a gwiwa ba sai da ya je ya kirawo ‘yan sanda ya saka hannu suma suka saka sannan ya tafi da ita wannan shi ne asalin yadda aka yi ya sami Nabila.

Nuna damuwar Nabila shi ne ya sanya mahaifin ta ya amince aka daura musu aure shi da ita, Nabila ta ci gaba da kulawa da shi. A bangaren Umar kuma damuwa da bacin rai sun yi masa yawa a kan rasa masoyiyarsa da ya yi har mahaifiyarsa ta yi masa ishara da wasu matan a kan ya je ya aura amma ya ce shi sam aure ba yanzu ba har tasa ya yi tafiyarsa kasar waje domin ya yi karatunsa na PHD domin ya debe damuwa, sai bayan shekara uku ya dawo yana zuwa ya tarar mahaifin Nabila ya rasu ana cikin zaman makoki Umar ya zo ya yi mata gaisuwa Nabila ta shaida masa cewar mahaifinta yabar mata wasiyyar ta aure shi sannan kuma ta je ta nemo dangin mahaifinta watakila ko suna da bukatar ganinta sosai, Umar ya yi farin cikin jin wannan furucin na Nabila sosai.

Abubuwan birgewa:

1- Jaruman sun yi matukar kokari wajen isar da sakon.

2- An yi amfani da kayan aiki masu kyau musamman kamara ta daukar hoto da kuma abin daukar sauti.

3- An yi kokari wajen samar da wuraren da suka da ce da labarin.

4- An nuna muhimmancin kyautatawa dan Adam.

Kurakurai:

1-A lokacin da iyayen Nabila suka rasu shin dama ita ba ta da wani dangi sai Bukar da Lawan kannen mahaifinta? duk ina dangin mahaifiyarta har aka bayar da ita tsawon wannan lokacin babu wanda ya neme ta?

2- Akwai lokacin da Abban Nabila ya biya kudin sadakinta dubu goma a ka’idar shari’ar musulunci sadakin mace budurwa ya fi yadda suka fada.

3- An nuna ana bukin Umar da Nabila har ana cewa gobe daurin aure amma da aka nuno gidansu Umar da Nabila babu wata alamar ana buki ko mutum daya babu a gidajansu.

4- akwai wurin da Abban Nabila yake bai wa su Umar tarihin yadda ya sami Nabila amma da a ka dawo daga labari sai mai kallo ya ga Umar din baya wajen.

5- A ka’idar musulunci idan mijin mace ya rasu ba ta sake kula wani ko ta yi maganar aure har sai ta yi idda amma sai ga shi lokacin da Umar ya zo yi wa Nabila gaisuwa ana cikin makoki sai ga shi tana yi masa maganar aure.

6-A gidansu Nabila an nuna su kadai ne kuma ba sa kiwon komai kuma gidane mai kyau wanda ba zai kasance a ce idan ma ana kiwo ba zuwa har cikin harabar gidan yadda kowa zai gansu ko kuma a dinga jiyo kukansu amma sai ga shi masu kallo suna jiyo kukan zakaru da karar dakan turmi bayan gidan su kadai ne.

7- Yakamata a ce an nuna mahaifiyar Umar ko sau daya ne ta zo gidansu Nabila ta duba mahaifinta ko kuma a ce an ganta ta zo yi musu gaisuwar mahaifiyarta da ta rasu kasancewar kwana daya ne ya rage a daura auren Umar da Nabila mahaifiyar ta rasu.

8- Ba a nuna lokacin da Abban Nabila ya fada mata cewar shi ba mahaifin ta ba ne daga baya sai mai kallo ya ji tana ba da labarin abin da ya faru tana karama kuma lokacin da aka dauko ta ta yi kan kanta ace ta tuna duk abinda ya faru.

9- Yakamata a ce an nuna karshen Lawan da Bukar saboda sako ga irin masu aikata irin halayyarsu.

Karkarewa:

Fim din ya kayatar kuma akwai sako, amma kuma wasu abubuwan da su ka faru ba za su faru a gaske ba. Allahu a’alamu!.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©Leadership A Yau
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user