Tuesday 1 May 2018

Karanta Kaji: Kowa Yasan A Mulki na bankunta tawa kowa ba sai zallan Adalci- Goodluck Ebele Jonathan

Tura Wannan Zuwa Ga

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya karyata furucin
da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi
cewa gwamnatin sa ta barnata naira biliyan 100 da wasu dala
miliyan 289 makonni kadan kafin zaben shekara ta 2015.

A cikin wata sanarwa da tsohon mai taimaka wa Jonathan ta
fuskar yada labarai Reno Omokri fitar, ya ce idan har abin da
Osinbajo ya fadi gaskiya ne, to ya shaida wa duniya cewa
hakanne ta hanyar bada hujjojin da za su tabbatar da gaskiyar
sa.

Ya ce Jonathan bai kashe naira biliyan 150 makonni biyu kafin
zaben shekara ta 2015 ba, idan kuma akwai shaidar ya yi
hakan a baza shi a faifai kowa ya gani.
Omokri, ya kuma karyata zargin cewa Jonathan ya kashe naira
biliyan 14 domin bunkasa ayyukan noma a Nijeriya cikin
shekaru uku.

A karshe ya ce gwamnatin APC da ba ta wuce shekaru uku a
kan mulki ba, ta ciwo bashin da jam’iyyar PDP ba ta ciwo ba a
tsawon shekaru 16 da ta yi ta na mulki.

Source  by ©Muryar 'Yanci
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user