Friday 11 May 2018

KARANTA A NATSE KAJI: NA TABBATA SAI YA GIRGIZA ZUCIYAR DUK WANI MAI IMANI BABBAN TASHIN HANKALI!!!

Tura Wannan Zuwa Ga
Hadisi ne zan karanta muku Amma ina neman alfarma guda awajenku kafin ku karanta Hadisin nan Alfarmar da nake nema awajenku ita ce, ku tsayar da duk abinda kukeyi, ku nutsu ku karantashi da kyau.

Domin na tabbata sai ya girgiza zuciyar duk wani mai Imani.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Tsira da aminci su tabbata bisa Annabin Qarshe,
da dukkan Iyalansa da Sahabbai baki daya.
Yazeedur Raqqaashiy ya karbo hadisin daga Anas
bn Malik (ra) yana cewa:

Watarana Mala’ika Jibreelu (as) yazo wajen
Manzon Allah (saww) awani lokacin da bai saba
zuwa masa ba. Yazo, gaba dayan launin fuskarsa
ya chanza. Sai Manzon Allah (saww) yace masa
“MAI YASA NAGA LAUNIN FUSKARKA DUK YA
CHANJA HAKA?”.

Yace “Ya Muhammadu (saww) nazo maka ne
awannan lokacin da Allah yayi Umurni da Masu
hura wuta suci gaba da Hura ta.

Duk wanda yasan cewa Jahannama gaskiya ce,
Wuta gaskiya ce, Azabar Qabari gaskiya ce, kuma
Azabar Allah ita ce mafi girma, to bai kamata yayi
wani farin ciki ba har sai ya tabbatar da cewa ya
samu tsira daga wannan”.

Sai Manzon Allah (saww) yace masa “YA
JUBREELU INA SO KA SIFFANTA MUN YADDA
JAHANNAMA TAKE”.

Sai yace “Na’am. Hakika Allah madaukakin Sarki
yayin da ya halicci Jahannama, yasa an hurata
tsawon Shekaru DUBU. Har sai da ta zama JA –
JAWUR. Sannan aka sake hurata tsawon Shekaru
DUBU har sai da ta zama FARI – FAT!!

Sannan aka sake hurata tsawon shekaru DUBU
har sai da ta zama BAQA – QIRIN!!!.

Tana nan har yanzu BAQA QIRIN ce, mai
tsananin duhu ce. Harshen Balbalinta basu
mutuwa ballantana Garwashinta.
Na rantse da Girman Ubangijin da ya aikoka da
gaskiya, da ache za’a bude misalin kofar allura
daga wutar Jahannama, Wallahi sai dukkan
Ma’abotan doron duniyar nan sun Qone baki
dayansu saboda tsananin zafinta.

Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da
gaskiya, da ache za’a ratayo tufafi guda daya
tufafin ‘Yan Wutar Jahannama a makaloshi
atsakanin Sararin Samaniya, da sai Dukkan
Ma’abotan doron Qasa sun Mutu baki dayansu
saboda tsananin Warin wannan Tufafin.
Da kuma zafin dake tattare dashi. Babu wanda
zai yi saura acikinsu don tsananib abinda zasu
riska na zafin wannan tufafin.

Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da
gaskiya amatsayin Annabi, da ache za’a dauko
zira’i guda na Sasarin nan na ‘yan wuta (wato
CHAINS din da ake daure su dashi sannan arika
jansu ajan fuskarsu). Wannan Wanda Allah ya
ambata Acikin Alqur’ani, a dorashi bisa wani
dutse daga duwatsun duniyar nan, da sai dutsen
ya narke ya zagwanye har zuwa Qasa ta bakwai.

Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da
gaskiya amatsayin Annabi, da ache za’a ajiye
wani mutum a mafa’dar rana ana yi masa azaba,
da sai wanda yake mahudar rana ma ya Qone
Qurmus saboda bala’in zafinta.

Zafinta mai tsanani ne. Zurfinta mai nisa ne.
Tufafin cikinta na Qarfe ne. Abin shan cikinta
HAMIMU ne (tafasasshen ruwan azaba) da kuma
ruwan Gyambo. Mayafan cikinta kuma an
yankosu ne daga Wutar”.

Tana da Kofofi guda bakwai, Kowacce Qofa tana
da wani yankin cikinsu da aka tsaga mata (zasu
shiga ta cikinta) daga Mazaje da mataye.
Sai Manzon Allah (saww) yace: “SHIN KOFOFIN
NAN IRIN NAMU NE?”.

Sai Jibreelu yace: “A’a sai dai ita kofofin abude
suke, wata kofar tana Qasan wata. Tsakanin
kowacce Kofa da wata kofar, tsawon tafiyar
shekara SABA’IN ne.

Kowacce Qofa ta ninka wacce take sama da ita
atsananin azaba har ninki SABA’IN.
Za’a rika kora makiyan Allah cikinta. Kuma duk
sanda aka koro wasu (‘Yan wuta) zuwa wata
kofa, Zabaniyawa ne zasu tarbesu da Sarkoki da
Sasarai.
Za’a zira musu Sasari (chains) ta cikin bakinsu
sai ya fito ta duburarsu. Sannan za’a daure
hannunsa na haggu ajikin wuyansa, hannunsa na
dama kuma za’a fasa Qirjinsa dashi aturoshi ta
cikin zuciyarsa sai ya fito ta bayan kafadarsa.

Sannan ahada adaure da wancan Sarkar.
Kowanne Dan Adam za’a hadashi tare da shaitani
guda acikin Sarkar Sasarin, Sannan arika Jansa
akan fuskarsa (acikin Garwashin wutar da kuma
dagwalonta) Mala’iku kuma suna Jibgarsu da
Gudumomin Baqin Qarfe.
Duk lokacin da suka nemi fita daga cikinta
saboda bakin ciki da wahala, Sai a sake dawowa
dasu cikinta.

Sai Annabi (saww) yace ma Jibreelu (ra) “SHIN
SU WANENE MAZAUNAN CIKIN WADANNAN
QOFOFI?”.

Sai Mala’ika Jibreelu yace: “Kaga amma Qofar
nan wacce take chan Qarkashin Qas, ita ce
mazaunar Munafukai da kuma wadanda suka
kafirce daga Mutanen Annabi Eisa (as) (Wadanda
aka ce kar su boye abinci amma sukayi taurin kai
suka boye). Da kuma Mutanen Fir’auna.
Ita wannan wutar sunanta “HAAWIYAH”.
Sai kuma Qofar nan ta biyu, wadanda zasu shiga
cikinta sune MUSHRIKAI. Kuma sunanta “AL-
JAHEEM”.
Qofar ta uku kuwa masu bautar taurari ne zasu
shiga ta cikinta. Sune mazaunan cikinta. (awani
wajen ance zasu zauna tare da masu wasa da
sallah).
Kuma sunan wannan wutar “SAQAR”.
Qofar wuta ta hudu, ta nan ne IBLIS (L. A.) zai
shiga cikinta tare da Mabiyansa da kuma
Majusawa masu bautar Wuta. Kuma sunanta
“LAZAA”.
Qofa ta biyar kuwa ta cikinta YAHUDAWA zasu
shiga. Kuma sunanta “ALHUTAMAH”.
Qofa ta shida kuwa, NASARA ne zasu shiga ta
cikinta. kuma sunanta “SA’EER”.
Daga nan kuma sai Mala’ika Jibreelu ya sunkuyar
da kansa yayi shuru, ya kasa ci gaba da magana
son jin kunyar Manzon Allah (saww).

Sai Manzo (saww) yace masa “SHIN BA ZAKA
BANI LABARIN KO SU WAYE MAZAUNAN CIKIN
WANNAN QOFAR TA BAKWAI DIN BA?”.

Sai Jibreelu yace: “Sune Ma’abotan Manyan
Zunubai daga cikin al’ummarka. Idan har suka
mutu basu tuba ba”
Nan take Sai Sayyiduna Rasulullahi (saww) ya
fadi YA SUMA!!!!
Sai Mala’ika Jibreelu ya dauki kansa ya dora
akan cinyoyinsa har sai da ya farfado sannan
yace:

“YA KAI JIBREELU LALLAI MUSIBA-TA TA GIRMA!
KUMA BAKIN CIKINA YA TSANANTA!!! YANZU
ASHE AKWAI WANDA ZAI SHIGA WUTA DAGA
CIKIN AL’UMMATA?”.

Sai yace “Eh amma Ma’abotan Manyan zunubai
daga cikinsu”.
Daga nan Sai Manzon Allah (saww) yasa kuka,
Mala’ika Jibreelu ma yana kuka…!!!”.
Ibnu Katheer ya kawo wannan hadisin da
ruwayoyi daban daban acikin Littafinsa mai suna
AN-NIHAYAH FIL FITAN WAL MALAHIM. Acikin
babin dake magana akan wuta da azaba cikinta.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: Zauren Fiqhu

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user