Wednesday 23 May 2018

Karanta Yanzu Kaji: Shin dagaske ne Akwai Soyayya a tsakanin Adam A Zango da Zainab Indomie???

Tura Wannan Zuwa

Daya daga cikin taurari kuma fitattun jarumai a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood sannan kuma shahararren mawakin Hausa din watau Adam A. Zango ya fito fili ya nunwa duniya irin yadda yake da matukar kyakkyawar alaka da jarumar nan Zainab Indomie.

Tauraron na fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango din dai ya saka wani hoto ne nasa kenan tare da tauraruwar fim din ta Hausa da tauraruwar ta ta dan lafa, Zainab Indomie a shafin sa na sada zumunta na Facebook.

Adamu din ya bayyana cewa yana tare da ita cikin daukaka da rashinta, cikin arziki da talauci, ya kare da cewa "Allah yi miki Albarka Indo."

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a baya tauraruwar Zainab ta haska sosai a duniyar fina-finan Hausa amma sai aka dena jin duriyarta, inda wasu ma har suka rika yin surutai iri-iri akan musabbabin abinda ya sa aka daina jin duriyar Zainab ciki hadda wanda aka rika cewa ciwon kanjamaune ya kamata.

Amma dai jarumar daga baya ta fito ta karyata hakan harma tayi Allah ya isa ga duk wanda suka mata wancan kazafin.

A shekarun baya Adam Zango da Zainab indomie sunfi ko wane Jarumai kawo kudi idan aka hada su tare a film, sunyi fina-finai irinsu Ga duhu Ga Haske, walijam, Balarabe Na balaraba, Adon Gari, Garin mu Da Zafi, Ahalil Kitabi da dai sauran finafinai wadanda suka zama zakara a wancan shekarun.

Har ana Hasashen cewa Ko akwai soyayya mai karfi a tsakaninsu, duk dai babu tabbacin haka amma an sheda cewa abokai nan Junana.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©Fim Hausa
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user