Sunday 6 May 2018

Wata Sabuwa: Kalli Sabbin Hotunan Adam Zango Dasuka Jawo Cece Kuce Ashafukan Sada Zumunta-Bude Ka gansu Kasha Mamaki

Tura Wannan Zuwa


Fitaccen mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa,
Adamu Abdullahi Zango ya tayar da kura bayan
ya sanya wadansu hotuna biyu a shafinsa na
Instagram.

Jarumin wanda ake kira da Fresh Prince ya
sanya hoto na farko hannunsa a kan kafadar
wata budurwa da ya kira ta da suna Hanaan.

A hoton jarumin da budurwar suna dariyar farin
ciki, sannan a karkashin hoton jarumin ya
rubuta kamar haka : “Yawancin mutane suna so ku yi
tafiya da su a cikin mota kirar Limo, amma abin da kake so
shi ne ka samu wanda zai yi tafiya da kai a mota bas idan
Limo din ta baci. Na yi farin ciki da ganin ki @hanaan, ’yar
uwata.”
Hoton ya tayar da kura, inda hakan ya sanya
jarumin ya kara sanya wani hoto mai dauke da
mutane hudu.

A hoto na biyun, jarumin ya dora hannuwansa
biyu a kan kafadun wadansu mata biyu, yayin da
wani matashi mai gemu yake daga farko ta
bangaren dama a hoton. A hoton dukkansu suna
dariya.
Hakan ya sa wani daga cikin mabayan jarumin a
Instagram mai suna Hamid Ibrahim cewa,
“ Wannan ba dabi’a mai kyau ba ce, a dai rika yi ana
tunawa da mutuwa.”

Ita kuwa Khadijat Arabi cewa ta yi sai masu hassada da
Zango su kashe kansu, amma babu yadda za su yi da Zango.
“Sai dai masu hassada ku kashe kanku, amma Zango ya yi
gaba.” Inji ta.
Samira Hassan kuwa cewa ta yi, budurwar da jarumin ya
dora hannu a kafadarta yayin daukar hoton, to ’yar uwarsa
ce ta jini, don haka babu wani laifi, ko abin cece-kuce da za
a ce jarumin ya jawo.

Shi kuwa Ahmed Isa cewa ya yi Zango abin koyi
ne ga miliyoyin jama’a, don haka bai kamata ya
rika sanya irin wadannan hotuna ba.
Ya ce, “ Zango kai babban jarumi ne, wanda miliyoyin
jama’a suke koyi da kai, don haka bai kamata ka sanya irin
wadannan hotuna ba.”

Haka ne ya sanya Adam A. Zango yin karin
bayani, inda ya ce wacce ya dauki hoton da ita
kanwarsa ce, kuma babu laifi don ya taba
kanwarsa, al’amarin da ya sanya mutane suka
sake yi masa caa! Kasuwar kuda.
Ibrahim Idris ya ce, bai gamsu da bayanin da
jarumin ya yi ba, inda ya ba shi shawara ko da
zai dauki hotuna da ’yan uwansa, to ba lallai sai
ya dafa su ko ya rungume su ba.

“ Koda ’yan uwansa ne bai kamata ya dafa su ba, bai
kamata ya rungume su ba, kowa ya san yadda akuyar ’yan
fim ta yi kuka, ana yi musu kudin goro wajen kiransu ’yan
iska, don haka sai ya bar halal don kunya. Ma’ana bai san
adadin wuraren da hotunan za su zaga ba, ba kuma kowa
ne zai gane cewa ’yan uwansa ba ne, wadansu za su yi
amfani da hotunan wajen yada sharri.
“Su rika cewa ga abin da ’yan fim din Hausa suke yi, kamar
yadda aka rika yada na Nafisa Abdullahi da Zainab Indomie
da Ibrahim Maishinku da sauransu, don haka ina ganin
rashin sanya hotunan shi ne mafi alheri a kan sanya shi.”
Inji Idris.

Amina A. Baba a lokacin da take tofa albarkacin bakinta
cewa ta yi ko da jarumin zai sanya hotunan da suka shafi
’yan uwansa ba lallai ne sai ya dafa su ba.
“Idan har ya zama dole sai jarumin ya sanya hotunansa
tare da ’yan uwansa, to bai zama dole sai ya dafa su ba, za
su tsaya ko su zauna a dauki hoton ba tare da ya dafa su ba,
hakan kwata-kwata bai dace ba, kuma ya kamata Zango ya
sani shi fa ba yaro ba ne, kuma ya san dole jama’a za su
caccake shi amma ya sanya, inda hakan yake nuna cewa da
gangan ya yi,” Inji ta.

Hakan ne ya sa daga baya jarumin ya boye
maganganun mutane dangane da hotunan, duk
da cewa har zuwa lokacin da aka kammala
rubuta wannan rahoto bai cire hotunan ba.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©Hausaloaded
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user