Friday 29 June 2018

AL-KUR'ANI NE BABBAN KALUBALEN DA YA HANA KASASHEN MUSULMAI CI GABA DA KUMA WAYEWA - Gerhard Weinberger

Tura Wannan Zuwa
Tsohon jakadan Austria a Tunusiya, Gerhard Weinberger ya ce babu ta yadda za a yi a kafa wayayyiyar kasa ta hanyar kafewa da ayoyin Al Kur'ani kawai.




"Ba za a taba iya gina kasa ba da Kur'ani" , wannan shi ne sunan littafin da tsohon jakadan ya wallafa a gidan buga litattafai na Mymorawa.

A cewar marubucin,"Al Kur'ani ne babban kalubalen da ya hana kasashen Musulmai ci gaba da kuma wayewa.Saboda babu ta yadda za a yi, a gina wayayyiyar kasa ta hanyar kafewa da ayoyin Kur'ani.


A Tunusiya, wadanda suka rungumi rayuwar zamani sun yaki masu bugun gaba da Al Kur'ani da kuma fafutukar ganin an gudanar da komai kamar a zamanin Manzo" in ji shi.


"Yawancin ayoyin Kur'ani sun kafu ne kan wannan tsarin: Duk wanda bai yi imani ba za a hukunta shi...Wannan ba wayewa ba ce ko kuma demokradiyya,kusan sai mu ce kama-karya ce.Wannan shi babban kalubalen da ke gaban Musulmai.." in ji Weinberger.

Domin samun Labarai,Nishadi,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna, Hausa Videos,Wakoki Hausa, Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya


FARIN CIKIN KU SHINE FARIN CIKIN MU

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari  ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: TRT HAUSA

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user