Saturday 30 June 2018

Shin Ko Kasan Amsar Da Jaruma Rahama Sadau Ta Mayarwa Da Wanda Ya ce Naji Ance Kin Koma Addininin Kirista Shin Gaskiya Ne?

Tura Wannan Zuwa Ga
Fitacciyar Jarumar Fina-Finan Hausa da Kuma na Turanci wato (Kannywood da Nollywood)  ta mayar wa da ɗaya daga cikin mabiya Shafin ta na Twitter amsar Tambayar da yayi Mata.





Mabiyin nata a Shafin ta ya Rubuta Tambaya Kamar Haka:


Naji jita-jitar Cewa"Wai kin zama Kirista amma ban yarda ba, shin gaskiya ne ko kuwa ba gaskiya bane?".

Inda jaruma Rahama  Sadau ta mayar mai da amsar kamar haka:

Naji Cewar"Yanzu Kai ba mutum bane , shin da  gaske ne?

Idan ba zaku manta ba tin lokacin da aka bayar da labarin Cewar"Rahma Sadau ta amsa gayyatar da shahararen mawakin nan na kasar Amurka, Akon ya yi mata zuwa kasar Amurka".

Ciki harda Shafin Muryar Hausa24 ta Wallafa Labarin, tin bayan fitar wannan labarin kowanne sashi da lungu da sako na shafukan Sada Zumunta Labarin ne yake yawo.

Musamman Shafukan Hausawa Wanda mafi aka sarin su Musulmai ne wanda hakan ya sabawa tsarin addinin musulunci yin Fina-Finan Hausa,  haka kuma ya sabawa al'adun Malam bahaushe yin tarayya tsakanin mace da namiji, musamman wanda suke da banbancin Al'adu ko Addini

Kamar yadda Binciken Shafin Muryar Hausa24 ya nuna"An haifi fitacciyar Jarumar Fina-Finan Hausa da kuma na Turanci wato Kannywood da Nollywood Rahama Sadau a 17-12-1993 a arewacin Kasar Nigeria".

Rahama Sadau ta fara harkar Fina-Finan Hausa cikin shekarar 2013

Jarumar Fina-Finan Hausa da kuma na kudancin Kasar Nigeria ta samu Lambobin Yabo kamar haka:

City People Movie Award for Face of Kannywood of the Year

City People Movie Award for Best Kannywood Actress of the Year

City People Movie Award for Kannywood Best New Actress of the Year

Rahama Sadau ta zama fitacciyar Jarumar Fina-Finan Africa  a Shekarar 2015 wanda  African Voice ke shiryawa.

Za ku tuna cêwa an kore Rahama daga Kannywood bayan Ƙungiyar masu hotó da wasaʼn Ƙwaikwaiƴo sun dakatar da ita domin wasan da ta yi tare da ClassiQ, wani mawaƙi wanda yake garin Jos.

Bayan an dakatar da Rahama, Jeta Amata da Akon sun gayyace ta zuwa Hollywood, domin yin sabon fim mai suna "The American King".(Waton "Sarikin Amirka").

Wannan shine Takaitaccen Tarihin Rayuwar Jarumar Fina-Finan Hausa da Kuma na Turanci wato Nollywod, Wanda Shafin Muryar Hausa24 ta tattaro mu Ku kadan Daga cikin Tarihin Rayuwar Jarumar Fina-Finan Kannywood da Nollywod, Ku ci gaba da kasancewa da Muryarhausa24.com.ng domin samun cikakken Tarihin Rayuwar Jaruma Rahama Sadau.


Source: www.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user