Saturday 30 June 2018

TAKAITACCEN TARIHIN IMAM MUHAMMAD IBN HASAN AL SHAIBANI - KARANTA A NATSE KAJI

Tura Wannan Zuwa Ga
Marubuci: SADIQ TUKUR GWARZO

An haifi Imam Muhammad Al Shaibani a garin Wasit dake cikin kasar Iraqi a shekarar 750 miladiyya.
A wannan garin ya taso cikin neman ilimi har girmansa daga bisani ya koma birnin Kufa mazaunin Imam Abu Hanifa da zama.

Mahaifinsa sojan yaƙi ne na kasar Iraqi amma yafi sha'awar ɗansa ya koyi ilimi da hikimomi. Don haka tun yana ɗan shekaru 18 yake zuwa birnin Kufa ɗaukar karatu, daga baya ma ya dawo birnin da zama.

Ance yayi karatu a gaban Imam Abu Hanifa na tsawon shekaru biyu, sannan ya ɗauki karatu a wurin wani malami babba mai suna Abu Yusuf, daga nan kuma ya zagaya wuraren Imam Sufiyanul Thawri da Imam Awza'i da Imam Maliki dake Madina duk ya ɗauki karatu. Don haka sai iliminsa yasa ya soma samun ɗaukaka tun yana matashi.

Da fari dai, ance ya zamo Malami a birnin Kufa tun yana ɗan shekaru 20 da haihuwa, sannan ya zamo Alkali a wajajen wannan lokaci.

Al Shaibani ya koma Bagadaza koyon ilimi. Acan ne ya haɗu da Halifan musulumci Harun Rashid wanda ya girmamashi tare da naɗashi matsayin alkali a fadarsa.

Sannan ance har Imam Muhammad Ibn Idris Ash-Shafi'i ya ya koyar karatu, koda yake daga baya akace ai Imam Shafi'in ya taɓa rubuta takarda mai nuna baiken malamin nasa akan wasu ra'ayoyi nashi na ilimi, amma dai an samu cewar yana matukar girmamashi.

Tare da Imam Al Shaibani Halifa Haruna Rashid ya tafi birnin Khorasan a wani lokaci daya kai ziyara can, haka kuma yana a matsayin alkali a karkashinsa har mutuwa ta riske shi a birnin Rey cikin shekarar 805 miladiyya.

Imam Shaibani yayi aikin ilimi sosai musamman a fannin sharia, shine marubucin littafin daya samar da ka'idojin yin yakin jihadi a cikin addinin musulunci ya kuma sanar da yanayin daya kamata ace an cika kafin tabbatar da daular musulunci a kowanne wuri.

Hak kuma yayi rubututtuka akan hukuncin ganima a yaki, da hukuncin fursunonin yaki, da kare martabar yara ƙananu da kuma mata a wajen yaki gami da matsayin amfani da guba a wajen yaki.

Ance da waɗannan rubututtuka daular Abbasid ta rinka amfani a matsayin kaidojin yin yaki ga alƙaryu da kuma yarjejeniyar samar da zama lafiya tsakanin masarautu, musamman ga abokiyar husumarta dake Turkiyya wadda Rumawa ke jagoranta, watau daular Byzantine.

Daga littattafan daya rubuta a zamanin rayuwarsa akwai:-

-Al Mabsuɗa
-Al Jamiul Kabir
-Al Jamiul Saghir
-Al Siyar Al Kabir
-Al Ziyadat

Da wasunsu.


Da fatan Allah yajiƙansa Amin.

Domin samun Labarai,Nishadi,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna, Hausa Videos,Wakoki Hausa, Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya


FARIN CIKIN KU SHINE FARIN CIKIN MU

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari  ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user