Friday 29 June 2018

Karanta Yanzu Kaji: Shin ko kasan dalilin da yasa 'yan Najeriya suka yi caa kan Cüneyt ???

Tura Wannan Zuwa Ga
Sau hudu Najeriya na shan kaye a hannun Argentina a gasar kofin duniya.


Alkali Çakır ya haifar da cece-kuce a "Karawar Kaddara" da Argentina ta yi da Najeriya a rukunin D.

Al'umar nahiyar Afirka,ta yi caa kan Baturken da ya alkalanci karawar Najeriya da Argentina.

Shin ko me yasa ?

Majiyarmu ta Trt Hausa ta tattaro Cewa"Hukunce-hukuncen da ya yanke a wasan da Argentina ta lallasa Najeriya 2 da 1, sun jawo wa alkalin wasa na kasar Turkiyya Çüneyt Çakir bakin jini".

Argentina wacce ta cim ma matsayin gaba, ta yi wa Najeriya fintinkau a minti na 14,bayan da Messi ya zura kwallo.

A hutun rabin lokaci, Argentina ce a sahun gaba da maki 1,yayin Najeriya ba ta zura kwallo ko daya ba.

A dakika ta 49, dan wasan Argentina, Javier Mascherano ya dakatar da bugun kusurwar da wani takwaransa na Najeriya ya yi.Abinda ya haifar da bugun daga kai sai mai tsaron gida ga Najeriya.

Haka zalika alkali ya hukunta Mascherano.
An leka bidiyoyin da kyamarorin bin diddigin wasanni suka dauka game da wannan lamari,kuma hukunci bai sauya ba.

Najeriya ta yi kunnen doki da abokiyar karawarta a sa'ilin da dan wasanta Victor Moses ya saka kwallo a ragar Argentina.
A dakika ta 75 kwallon da Najeriya ta buga ya ci karo da hannun dan kasar Argentina,Rojo,amma alkali ya ce a ci gaba da wasa.

'Yan Najeriya sun dinka kawo kara cewa sun samu bugun daga kai sai mai tsaro gida ,amma an hana su.Abinda yasa  alkali ya tsaida wasa don gano gaskiyar batun.

Kallon bidiyoyin wasan ke da wuya, sai Çakır ya ce wannan lamarin katari ne ba gangan ba.

A minti na 86 dan wasa Rojo ya zura kwallo a ragar Najeriya,wanda hakan yasa Argentina ta tara maki 3,yayin da Croatia kuma ta yi nasarar lallasa Iceland a mintinan karshe na karawarsu.

Wadannan hukunce-hunkucen da Cüneyt Çakır ya yanke sun fusata duniya matuka gaya,inda kawo yanzu ake ci gaba da yin caa kansa.

Idan Baku manta ba Muryar Hausa24 ta tattaro muku kadan Daga cikin Ra'ayoyin 'Yan Nigeria akan Wasan Nigeria da Argentina.

Babangida Lawal

Yanzu zakaga ya'yan jakuna, bakin haure yan 'cirani da ya'yan matsiyata suna murna an cire mu.

Sai adale, Kare, mahaukaci zai ki kasar sa.

Usman Inuwa Pantami

Argentina ta fitar da Najeriya da taimakon fifa wannan shine gaskiyar magana

Zaku iya karanta sauran Ra'ayoyin anan..

KARANTA WASU DAGA CIKIN RA'AYOYIN 'YAN NIGERIA AKAN SAKAMAKON WASAN NIGERIA DA ARGENTINA - HOTUNA DA CIKAKKEN LABARIN WASAN


Domin samun Labarai,Nishadi,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna, Hausa Videos,Wakoki Hausa, Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya


FARIN CIKIN KU SHINE FARIN CIKIN MU

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari  ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user