Wednesday 20 June 2018

KARANTA DUMBIN LADA MAI TARIN YAWA DAMAI KARANTA AL-QUR'ANI YAKE SAMU

Tura Wannan Zuwa
DUMBIN LADA MAI TARIN
YAWA DAMAI KARANTA AL-QUR'ANI YAKE SAMU.


Rubutawa: TAFARKIN TSIRA

Manzon Allah (S.A.W) yace:

"Wanda ya karanta Alqur'ani yana cikin Sallah, ga kowane harafi yanada lada dari.
Kuma wanda ya karanta Alqur'ani ba cikin Sallah ba amma yana da alwalla, shi kuma ga kowane harafi yanada lada Ashirin da biyar.

Kuma wanda ya karanta Alqur'ani batare da alwalla ba, ga kowane harafi yanada lada goma".

Wannan hadisin akwaishi acikin MUJALISUL ANWAR da DURRATUN NASIHINA.


Allahu Akbar!

Alqur'ani babban kundi!

Gulbi kake ba'a kai gacinka!

Kowa ya rike ka yadace!

Gaka Haske! Gaka Shiriya!

Gaka Hanya mikakkiya har aljannah!
Allah Sarkin rahama !


Alqur'ani yanada harafi guda DUBU DARI UKKU DA ASHIRIN DA UKKU, DA DARI SHIDDA DA SABA'IN DA DAYA. (323,671).

Don haka ga yadda lissafin yake:

WANDA YA KARANCE ALQUR'ANI CIKIN SALLAH.

Yana da lada: 32,367,100. Miliyan Talatin da biyu, da dubu dari ukku da sittin da bakwai da dari daya.

WANDA YA KARANCE ALQUR'ANI BA CIKIN SALLAH BA AMMA YANADA ALWALLA.

Yana da lada: 8,091,775. Miliyan takwas da dubu casa'in da daya da dari bakwai da saba'in da biyar.




WANDA YA KARANCE ALQUR'ANI BATARE DA ALWALLA BA.

Yana da lada: 3,236,710. Miliyan ukku da dubu dari biyu da talatin da shidda da dari bakwai da goma.

Don haka ya kamata ace kowane musulmi yana samun kashi guda daga cikin su, a kalla ya sauke Al-qur'ani sau daya duk bayan wata biyu.

Duk wanda baya karanta alqur'ani, to yanzu dai yaga irin hasarar ladar da yakeyi.
Shi kuma wanda yake karanta alqur'ani, to yaga dai irin ladan da yake samu.

Allah yakara sanya rabonmu a ciki, yakuma kara bamu ikon cigaba da karantawa.

Domin samun Labarai,Nishadi,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng

Ko ku biyo mu akan wannan sabuwar manhajar ta Muryar hausa24 domin samun dukkan wani sabon  posting Kai tsaye cikin sauki tare da Karantawa cikin hanya mafi sauki wannan dama ce ga masu amfani da Android domin samun damar sauke sabon App din Mu sannan ku turawa sauran 'yan Uwa da Abokanan Arziki
Nan zaku shiga ku Yi download Kai tsaye cikin sauki

http://www.datafilehost.com/get.php?file=6e14fd02

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Source: www.muryarhausa24.com.ng


TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user