Thursday 21 June 2018

Yadda Abokin Mahaifina Ya Kai Ni Karuwanci A Libiya-Karanta Yanzu Kaji Yadda Abin yafaru

Tura Wannan Zuwa Ga



’Yan Nijeriya su 150 da aka dawo dasu daga Libiya, wadanda mafi yawancin su mata ne, sun samu yanci ganin sunyi tsawon tafiyar kilomita 300 daga Lagos zuwa Benin bayan sun samu arcewa daga jafa’in da suka baro, kasar da mafi yawancin aka yaudara aka yi safarar su,
inda a bisa mafarkin su, idan sun shiga kasar kakar su ta yanke saka. Sai dai, mafarkin nasu sai ya juya zuwa zaman cikin aikin bauta, inda wasu da dama suka mutu.


Rubutawa: Leadership A Yau

A makon da ya gabata an dawo da wasu ‘yan jihar su 150, inda a karon farko na dawo da ‘yan jihar an dawo da kashi na farko su 87 a watan Okutoba.

Daga cikin wadanda aka maido a ranar Laraba su 23, akwai mata masu juna biyu da kuma ‘yan mata su 13. Da ka gansu, za ka ga yadda jikin su yake dauke da raunuka da alamun matsananciyar wahala da alamun chututtuka tabban harbin bindiga. Gwamnatin jihar a karkashin ‘yan sintirin ta na yakki da safarar biladama da kwamishinan Shari’a kuma Atoni Janar na jihar Farfesa Yinka Omorogbe yake jagoranta ganin wadanda aka dawo dasu sun isa ga ‘yan uwansu ta hanya ta hanyar yin hadaka da kungiyar fadakarwa ta matasa bakin haure (IYAMIDR) da kwamarade Solomon Okoduwa yakejagoranta.
An dawo dasu ne sakamakon daukin gwamanatin jihar tare da hadin gwiwar hukumomin kasa da kasa da suka taimaka wajen tantance wadanda suke garkame a gidan yari na gwamnati dana zaman kansa a kasar ta Libiya.
Ga mafi yawancin su kasar Italiya suka so su isa. Wasu sun sayar da kadarorin su don yin balaguron wasu kuma da basu da abinda zasu sayar,sun shiga yarje ce da wadanda zasu dauki nauyin su yin balaguron ‘yan jihar ta Edo don ayi safarar dasu, inda zasu biya su a nan gana. Sai dai, dukkan wannan rukunin biyu, su a karshe sun cinci kansu a gidajen gidan Yari na Libiya.
Lokacin da yake tsokaci akan kokarin da Gwamnan jihar Godwin Obaseki ya yi akan lamarin, kwamarade Okoduwa ya bayyana cewar, Godwin Obaseki ya sanya a dinga biyan su wasu ‘yan kudi duk wata wadanda kuma suke son rungumar sana’a an basu taimako don inganta hazakar su.

Matasan da kuma suke son komawa makaranta, gwamnatin ta dauki nauyon karatun su. Muna son muyi amfani dasu a matsayin jakadu wajen bai wa wadanda keda nufin ficewa don su karya masu kwarin gwaiwar yin hakan.
Wata yarinya ‘yar shekara 20 mai suna Beauty Okoro wadda tana daya daga cikin wadanda aka dawo dasu a ranar Larabar ta shirya tsaf, don zama mai yin wa’azi akan yin balaguro zuwa Libya ko Italiya. Ta bayyana yadda aka yaudare ta aka yi balaguron da ita, inda aka tilasta mata shiga yin karuwanci, harda hannun abokin mahaifin dake da zama a Libya. Yarinyar ta ce, “na yi balaguron ranar hudu ga watan Yunin shekarar
data gabata kuma wanda ya dauki nauyin tafiya ta, a cikin mako daya zamu isa Italiya, amma da muka isa Libya, sai labarin ya canza”.
Ta ci gaba da cewa, wadanda suke daukar nauyin suna cewa ba wani wuya isa Italiya, amma yanzu na koyi darasi kuma ina ganin ya kamata gwamnati ta damko su don a hukunta su, sai ta kuma barke da kuka, wadannan masu daukar nauyin suna nan a Edo kuma suna da ‘yan koren su a Libya, kasuwanci ne da suke kullawa idona kuma ya gane mini a ‘yan shekaru na 20.
Beauty ta kara da cewa, lokacin da naje wani waje da ake kira Ghetto, ina wajen tare da wata yarinya, inda suka sheda mana cewar, wani mutumya ce zamu dinga yin karuwanci, inda bayan kwana daya wata mata tazo wajen ta saye ni a matsayin bai war ta, ta saye ni akan naira 1,700, inda ta kuma umarce ni in biya ta naira 450, 000, duk ya hada da abincin da zanci da kudin ruwan da zan dinga yin wanka.

“Na kira mahaifi na nayi masa bayanin cewar ta ce mutane na su turo min kudi ko kuma zan zama karuwa don su fitar da kudin su, mahaifi na ya turo min da naira 50,000, inda ya roke su zai sayar da filin sa don cika masu sauran kudin.
Mijin uwar dakin na dan Nijeriya ne,mahaifi na yaso ya sayar masa da filin don su taimaka mini, amma ya ce bai bukata don baida ra’ayi da inda filin yake saboda haka ba zai saya ba.
Beauty ta bayyana cewar,” bani da wani zabi da ya wuce yin abinda uwar daki na ta ce inyi, wato karuwanci, inda naci gaba da kwanan da mutanekala-kala, nayi mata aiki har na watanni biyu kuma ba’a bari na in fita.
“Na sanar da mahaifi a cikin kangin da na samu kaina, inda ya ce mini yana da aboki a Libya da zai tuntuba don ya taimaka mini ya kuma tuntubi mutumin man, amma mutumin ya ce mashi yana zaune ne a wani gari da ban a kasar.”
Ta ce, mutumin ya ce mini in tambayi uwar dakina akan yadda zai zo ya dauke ni kuma ashirye yake ya biya ta kudin, na tambaye ta sai ta ce mini ince wa masa ya biya naira 300,000, amma sai nace mata ai mahaifi na ya riga ya biya naira 50,000, ma’ana sauran naira 250,000, shi kuma abokin mahaifin nawa ya ce, yana da kawai naira 200,00 da zai bai wa matar. Ta bayyana cewar, mun roki matar, inda ta amince ta karbi wannankudin, kuma ya kawo naira 220,000 harda kudin motar da za a kai ni inda yake ta haka ne na bar gidan matar. Bayan dana isa gidan sa, nan ma duk irin masha’ar ce ake aikatawa, inda na ake wata mai kula da gidan shida ita suka umarce in dinga yin karuwanci.

Maihaifi na bai san cewar abokin nasa ya kawo ni gun matarbane don yin karuwanci ba.
Mutumin ya ce zan biya shi naira 440,000 kuma bani da wani zabi sai dai inyi aiki tukuru, inda a cikin watan Disambar shekarar data gabata, nakammala biyan kudin na kuma fara buga-bugar neman kudi ta kashin kaina don in tsallaka taku zuwa Italiya. Na tara naira 400,000 na bai wa mutumin naira 300,000 don ya ajiye mini, inda ganin cewar na san ina da kudi na yanke shawarar inje in sayi kayan abinci da zan yi amfani dashi in zan haura tekun, na samu mutumin don ya bani kudi na amma ya ce mini ba zai bani ba, na gaya masa cewar, wannan zalunci ne domin yana kwana dani kuma duk da cewar na biya shi kudin ajiye ni da ya yi a gidan sa amma bai gode ba.
Ya fara duka na har saida na kwanta ciwo, inda na kira mahaifiya ta nace mata ina son in bar wanan gidan. Kaddara kuma ta hauni bayan banga al’ada ta ba a wannan watan inda na gayawa mutumin cewar ina ganin ina da juna biyu. Mutumin ya ce mini inje inyi gwaji, amma a ranar da nayi shirin zuwa gwajin sai naga al’ada ta, daga nan sai ya fara jibgata cewar naje na
cire cikin ne amma na fada masa gaskiya cewar ba haka bane. Ya ce ba zai kyale ne ba domin naje na zubar masa da ciki, inda ya yi barazanar zai kira ‘yan iskan yaran Libya don su lallasa ni, ina ganin tasku a wancan gidan amma ban san abinda zan iya yi ba. Daga baya na hadu da wani Fasto a kafar sadarwa ta Facebook na kuma gaya masa matsala ta, inda ya umarce ni in sayi farin hankici in tura masa masa hoton mutumin.

Faston ya sheda mani cewar, mutumin sunan sa Ade kuma bayara be ne ya dauki fitsari na ya kaiwa wani lokitan gargajiya sai na fashe da kuka, amma Faston ya ce mini kada in damu. Mu ‘yan mata takwas ne a gidan da muke yi wa mutumin aiki kuma yana kwana damu sannan kuma mu biya shi. A lokacin da yazo yana son kwana dani na tambaye shi yaushe zai ‘yanta ni? sai ya ce mini kada in damu Labaraba mai zuwa zai ‘yanta ni.

A ranar da ya yi alkarin, sha daya ga watan Yuni, ya kira ni ya bani batirin waya kirar Nokia inyi masa charji, inda a daren ranar ya sheda mini cewar, mota zata zo ta dauke ni ya kuma ce mini kudin tafiya ta naira 60,000, daga yankin Tripoli inda zan tafi ta hanyar rafi zuwa Italiya.

Mutumin ya yi ikirarin cewar ya biya kimanin naira 210,000 don yin balaguron nawa, harda na tsallakawa kogin zuwa Italiya, amma na sheda masa cewar, har yanzu yana rike da kudi na. Bayan dana isa sansanin wanda daga sansanin zuwa Italiya ya kai kimanin awa daya da mintuna talatin, a sansanin mun sha wuya sosai domin babu abinci ba kuma kudi, na kira mutumin a waya ya ce mini in dawo gidan sa, amma nace masa da in dawo gidan sa,mutuwa ta tafi min duk da cewar akwai zafi a sansanin.
Ko wanne lokaci muka tashi sai muyi ta jin tashin bindiga, inda mutane zasu yi ta guje-guje harda hallaka mutane kamar kaji kuma akwai wani dare dana farka daga barci naga mutane suna ta guje-guje, inda na fadi har naji ciwo a kaina. Mutane sun hango ni suka ceto ni suka kai ni wajen magani aka bani magani, kuma akwai ranar da aka umarci mutane suzo don a tsallakar dasu. Wani kawa ta Anita ta shiga cikin jirgin domin ana tafiya dasu kashi-kashi ne, amma Anita ta mutu a cikin jirgin ruwan lokacin da kife lokacin da suke gujewa jami’an tsaro.

Na gano cewar matsalar mutumin ya karbi kudi daga gun mu, amma bai biya jami’an kumar sanya ido akan shige da fice na Libiya ba da suke kula da kogin ba.

Mun ji cewar mutumin yana tunkaho cewar, mahaifin sa sananne ne a a kasar, inda yaki biyan jami’an kudin duk da cewar ya karbi kudaden mu don tsallakawa rafin damu, ana kiran mutumin Ginabo.
Jami’an sun zo, kuma sun san cewar mu fasinjojin Ginabo ne, inda suka fara jibgar Ginabo da kira shakiyi makarya ci cewar ya karbi kudaden mu ya kuma yi watsi damu da kuma kin biyan mu. Suna yin maganar ne a cikin harshen larabci, jami’an sun kama mu suka kuma umarce da mu kira ‘yan uwan mu su turo mana kudi ko kuma a kashe mu.
Yadda na dawo shi ne wani mutum ya ce mini mu biya naira 20,000 domin yana lura da wani sansani muna wajen sai ‘yan sanda suka zo sukafara bin kowa, inda muka ranta ana kare kuma mutumin mai kula da sansanin ya kai mu wani daki ya karbe mana kudaden mu da wayoyin mu mu kimanin ‘yan mata takwas.

‘Yan sandan sun yi wa wajen kawanya suka kama mu suka kaimu gidan Yari, inda anan ne wasu jami’an Majalisar Dinkin Duniya ta tazo gun mu suka kawo mana Burodi kanana da ake bamu dai-dai wani lokaci kuma raba mana shikafar da aka dafa bata dafo sosai ba wadda ko kare bai kamata a bai wa ba, amma dole muka ci gaba da ci a haka.
Wani lokacin suna zuwa abinci kwayoyin sanya maye, inda kana gama ci sai barci a kasa sai suy mana fyade, amma daga baya jami’an su fara jigilar mu zuwa dawo wa Nijeriya, amma babu sunana a ciki har ta kai babu abinci da ruwa kuma akwai ‘yan Nikeriya da yawa a gidan Yarin. Daga abinda idona ya gane mini a gidan Yarin, akwai dubban ‘yan Nijeriya a gidan Yari da ban-da-ban. Ko wanne lokaci idan ka tashi zaka ga mutane biyar sun mutu saboda cunkoson dake gidan Yarin idan ina jin kishirwa babu ruwan sha,amma naga ruwa a kusa da gawar wani,inda banda wani zabi dole na dauka nasha don kada nima na mutu na rufe
ido na na sha ruwan.

Wadanan mutanen basu da imani a bisa maganar gaskiya, nayi dana sanin bala guron dana yi kuma ban cewar rafin yana tattare da hadari ba. Wanda ya dauki nauyin tafiyar dani bai gaya mini haka ba kuma shawara ta ga mutane ita ce, su daina cin burin zuwa Italiya ta haramtacciyar hanya, domin na ga tasku a matsayina na yarin ‘yar shekara 20, na karbi takardar sheadar kammala jarrabawar SSCE kafinn inyi balaguron, ina kira ga gwamnati ta taimaka min da aiki, ina kuma bai wa matasa shawara kada su kuskura suyi tunanin barin kasar nan amma su yi aikin su a Nijeriya duk da cewar ana shan wuya a Nijeriya amma su dukufa da addu’a don fita daga cikin wahalar da ake ciki, domin nima rashin hakuri na shi ya janyo mini hakan. Wata yarinya ‘yar shekara 24 mai suna Igbinewo Praise ita ma ta bayyana
irin taskun data samu kanta lokacin da tayi balaguron da mijin ta kuma ayau tana dauke da juna biyu amma mijin nata har yanzu yana Libiya.

A cewar ta, “na yi balaguron ne tare dashi amma har yanzu yana can, kafin tafiyar mu in sayar da kaya ne kuma ni marainiya ce, nida mijina ya biya naira 900,000 ga wanda ya dauki nauyin tafiyar mu bayan da muka isa Libya,naci sa’a ni ce ta farko da aka tsallakar dani, amma
miji na yana cikin daya tawagar da za a tsallakar.

Bayan mun tafi jirgin mu ya samu matsala a tsakiyar tekun mun jima a nan babu masu kawo mana dauki, amma jirgin Majalisar Dinki Duniya yazo ya kawo mana dauki daga nan aka kama mu, mijina yaje ya biya naira 250,000 don a sako ni daga gidan Yari, inda wani ya ce sai mun kara biyan naira 150,000 don a tsallakar dani, inda miji na ya biya.
A lokacin muna shirin tafiya sai jami’an kula da shige da fice suka zo suka kama mu suka kaimu gidan Yari, inda na shafe watanni a can kafin a kaimu sansanin kwashe bakin haure. Ba’a waje daya nake tare da miji na ba, amma muna ganin juna kullum, abin mamaki gani da juna biyu amma babu abinci, suna bamu karamin Burodi guda daya a kullum kuma kai zaka sayi ruwan sha da kudin ka kuma da tsada, mijina yana kiran mutanen sa su turo mana kudi.

Da farko abinda suka gaya mana cewar a cikin mako biyu kacal zamu isa Italiya, amma mu bamu san haka abin yake ba. Mun shafe mako daya a sahara kuma ga zafi. Wani abin mamaki lokacin da muka tafi mun kai mu talatin da uku amma a lokacin da muka isa sansanin dake Libiya muna da mutane ashirin da bakwai wadanda suke a raye nayi sa’a ina daga cikin wadanda aka kiega da suka dawo amma kafin na tafi da miji na Kuma duk ya rame bai jin dadi, a takaice ya ce min makon sa biyu bai yi wanka ba kuma ba abinci, lokacin dana ga mijina na fashe da kuka yadda naga ya koma kamar mahaukaci ban san cewar yana raye ba.
Basa barin su dawo wa saboda an riga an mayar dasu bayi suna yin aiki ba tare da biyan su ba, ina kira ga gwamnati da ta dawo da su gida.


Domin samun Labarai,Nishadi,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Source: www.muryarhausa24.com.ng
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user