Tuesday 3 July 2018

Karanta Wannan Labarin: Ina da tabbacin Kaca-Kaca zanyi da Buhari a 2019 cikin Jam'iyyar PDP - Dr Rabi'u Musa Kwankwaso

Tura Wannan Zuwa Ga
Tsohon gwanman Kano kuma Sanata a jam'iyyar APC ya ce shi ne mutumin da ya fi kowa karfi da farin jinin da zai iya kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.


Injiniya Rab'iu Musa Kwankwaso ya shaida wa fitaccen dan jaridar kuma mawallafi, Dele Momodou kamar yadda BBC ta ruwaito cewa shi yanzu ba shi da wata jam'iyya amma PDP ce ta fi kowacce dama da karfin kayar da shugaban, idan har ta ci gaba da bin tafarkin demokuradiyya.

Kwankwaso yasha alwashin cewar shi ya shiryawa jam'iyar APC dabarun da ya kaita ga samun nasarar da ya aza Buhari bisa karagar mulki a zaben 2015 da ta gabata.

Kwankwaso ya cigaba da cewar “Akwai bukatar Jam'iyar PDP ta fiddo da dantakara daga dayan jihohin Kano, Katsina ko Kaduna idan har tana bukatar lashe zabe mai zuwa. Zayyi matukar wahala PDP ta lashe zaben 2019 idan har ta fiddo da dantakara daga wata jiha sabanin jihohi Ukun nan. Inji Kwankwaso


“Ina da tabbacin kada Buhari idan har na samu wannan damar.

KARANTA YANZU KAJI: Takaitaccen Tarihin Rayuwar Dr Rabiu Musa Kwankwaso


Kuyi Mana hakuri na rashin kawo muku Labarin akan lokaci .

Domin samun Labarai,Nishadi,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna, Hausa Videos,Wakoki Hausa, Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya


DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA WWW.MURYARHAUSA24.COM.NG FARIN CIKIN AL'UMMA

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: wwww.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user