Friday 6 July 2018

Karanta Cikakken Tarihin Ahmed Musa: Abubuwan da Yakamata Ku sani dangane da Rayuwar Dan Wasan Kwallon Kafa Ahmed Musa - Hotuna da Cikakken Tarihi

Tura Wannan Zuwa Ga
Ahmed Musa dan wasan kwallon kafa ne na Najeriya wanda ke taka leda a kulob din kwallon kafa a Turai a karo na farko a kulob din Rukuni na Rasha, CSKA Moscow, inda ya tashi daga cikin manyan kungiyoyi a kasarsa.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

An haifi Ahmed Musa ne a Watan Oktoba a shekarar 1992 a Garin Jos da ke Jihar Filato.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Tun yana ‘Dan shekara 14 dai Ahmed Musa ya fara nunawa Duniya irin kwarewar sa a Kulob din GBS da ke Jos.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Gwarzon ‘Dan wasan nan na Kungiyar Super Eagles na Najeriya watau Ahmed Musa yayi suna a Duniya don haka mu ka kawo maku kadan daga cikin tarihin babban ‘Dan kwallon.


Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

A shekarar 2007 ne aka fara sanin ‘Dan wasa Ahmed Musa a Duniya wanda hakan ta sa Kungiya kwallon kafa na JUTH da ke Jos ta dauke sa. A nan kuma Ahmed Musa ya zura kwallaye har 4 a shekarar.


Biography of Ahmed Musa by Muryar

Bayan JUTH ne Ahmed Musa ya koma Kungiyar Kano Pillars a matsayin ‘Dan wasan aro.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

A Kano Pillars ne dai Musa ya kafa tarihi ya ci kwallayen da ba a taba cin su ba a Gasar Firimiya na Najeriya.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

A 2010 ne Musa ya koma Kungiyar Turai ta VVV Venlo sai dai bai iya fara bugawa ba sai da ya cika shekara 18 a Duniya. A wasan da ya fara bugawa kuwa ya nuna kan sa inda ya samowa Kungiyar sa finariti.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Bayan nan ne dai Tauraruwar Musa ta rika haskawa har ta kai Kungiyar CSKA Moscow su ka saye sa a 2012 bayan wasu da dama sun yi kokarin sayo ‘Dan wasan. Bayan shekaru kadan ne kuma ya koma Leicester City na Ingila.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

A gida kuma dai Ahmed Musa ya nuna kwarewar a Super Eagles inda ya ci kwallo 2 a wasan Najeriya da Kasar Argentina a 2014. A Gasar cin kofin na Duniya da ake yi a bana ma dai Musa ya sake zura kwallaye 2.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Ahmed Musa dai ya auri Jamila wanda ta haifa masa ‘Ya ‘ya 2. Daga baya dai su ka rabu bayan sun samu sabani a Ingila.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Musa ya koma ya auri Juliet Ejue wanda ta fito daga Kudancin Najeriya

Biography of Ahmed Musa by Muryar

Babban 'Dan wasan kwallon gaban na Kungiyar Leicester City Ahmed Musa dai mutum ne mai taimakon jama’a a Kano da ma Najeriya baki daya.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Ahmed Musa Musulmi ne wanda ya kuma rike addinin sa domin kuwa a kan gan shi a Masallaci da sauran wuraren ibada cikin kayan addini.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Babban 'Dan wasan ya taba rike Kyaftin din Super Eagles kuma shi yake goya lamba 7. Kafin nan Musa ya buga Kungiyar U-21 na Najeriya.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Mahaifinsa   Musulmi ne daga jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya yayin da mahaifiyarsa itama ta kasance Musulma, matar mahaifinsa ta biyu, ta kasance Kirista daga Jihar Edo.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

A shekara ta 2009 zuwa shekara ta 2007, Musa ya sake komawa Kano Pillars inda ya zura kwallaye 18 a wasanni 25 da kuma bugawa tawagar zuwa matsayi na biyu.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Bayan wannan gwagwarmaya, Musa ya karbi talanti a ƙasashen waje don shiga kungiyar VVV-Venlo ta kwallon kafa na Dutch Eredivisie.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Ya kasance a yanzu ya taimaka wa Najeriya lashe kofin gasar matasa na Afrika 2011, inda ya lashe kyautar mafi kyawun k'wallo, sa'an nan kuma FIFA U-20 a gasar cin kofin duniya ta FIFA 2011, inda aka zabe shi a wasanni na Golden Ball.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

A watan Janairu 2012, Ahmed Musa ya kori Netherlands a Rasha, ya shiga CSKA Moscow a matsayin kudin da ba a bayyana ba, ya lashe gasar Premier ta Ingila da Cup a farkon Wasan da yayi a kulob din

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Ahmed Musa na daga cikin 'yan wasan Najeriya wanda ya lashe gasar cin kofin kasashen Afrika na 2013, kafin ya sake kasancewa cikin tawagar FIFA Confederations Cup ta 2013.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Ahmed Musa ya ci gaba da taka leda a CSKA Moscow har zuwa shekarar 2016 a lokacin da ya koma Leicester City

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

A watan Janairun 2018, Musa ya koma CSKA Moscow don watanni 4 don samun lokaci mai tsawo kafin ya shiga gasar cin kofin duniya.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Ahmed Musa ya
ce yana da kimanin dolar Amirka miliyan $18.

ba abin mamaki ba ne Kasancewar shi Dan Wasan Kwallo, ya Mallaki gidaje a Jos, London, Moscow da kuma motoci da suka hada da Range Rover Sport.


Biography of Ahmed Musa

Sabon shiga gasar Firimiya na Ingila Fulham tare da sabon abokin adawar ta Huddersfield na neman kawo fitaccen dan wasan Super eagles, Ahmed Musa, don ya taka masu leda a kakar 2018/2019.

Biography of Ahmed Musa

Duba da irin rawar da ya taka tare da tawagar
Super eagles a gasar kofin duniya na wanan shekara, dan wasa mai tauraro Ahmed Musa ya shiga takardar yan wasa da kungiyar Fulham da Huddersfield na Ingila ke nema.

Biography of Ahmed Musa

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Leicester na tunanin sakin shi zuwa ga ciniki mafi soyuwa tsakanin kungiyoyi biyun dake neman siyan shi.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Ahmed Musa bai samu dama ba a Leicester bisa ga rawar da James Vardy ke takawa wajen zura kwallo a raga wanda dashi masoya da kungiyar ke takama dashi.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Ahmed Musa ya dawo kungiyar Leicester da taka leda a kakar 2016 sai dai amma bai samu damar nuna ma jama'a dabarar sa ba sakamakon rashin samun lokaci da yake fuskanta a kungiyar.

Wata kila idan ya koma Huddersfield ko Fulham tauraron sa zai haska a gasar firimiya na kakar 2018/2019.

Biograph of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Dan wasan dai ya taka rawar gani a gasar kofin duniya wanda ke gudana a kasar Rasha da tawagar Nijeriya.

A cikin wasanin rukuni uku da Nijeriya ta buga, dan wasan ya zura kwallo biyu a raga.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Duk da cewa Nijeriya bata yi nasarar tsallakewa zuwa zagaye na biyu, kwallayen da Ahmed Musa ya zura a raga wasan Nijeriya da Iceland  yana daga cikin abubuwan da haifar da farin cikin ga yan kasa. Kuma yana daga cikin wanda ya birge a gasar.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Sakamakon kwallo biyu da ya saka a raga a gasar, Ahmed Musa, ya kafa tarihi a tarihin kwallon kafa  na Nijeriya.

Shine dan wasan tawagar super eagles da yafi kwallo a gasar kofin duniya ta FIFA.

Ahmed Musa ya saki Jamila, ya Auri Juliet Adeh Ejue

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Abin ta kai har manya da iyaye su ka shigo cikin maganar domin a lallabi Jamila ta hakura da karin auren Mijin na ta amma abu ya faskara. Har Mahaifiyar Dan wasar ta je har Ingila domin ta shawo kan Sirikar ta amma fa tace sam ba za ta yarda ayi mata kishiya ba

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Hakan ta sa aka raba jiha tsakanin Ahmed din da Jamila uwar ‘ya ‘yan sa biyu bayan da ya tubure cewa sai ya kara aure ita ma ta cije.

Ahmed Musa Da Abdullahi Shehu Sun Yi Wa Marayu Goma Ta Arziki A Sokoto

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24


'Yan wasan kwallon kafar Nijeriya Ahmad Musa da Abdullahi Shehu sun kai ziyara a makarantar UK Jarma Academic (akasarin yaran daga jahohin maiduguri da Yobe wadanda suka rasa iyayen su sanadiyyar rikicin Boko Haram) inda Abdullahi ya ba su tallafin kayan abinci da suka hada da buhunan shinkafa guda dari, kwalin indomi hamsin da katon ashirin na lemun kwalba.


Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

A bangaren wasanni kuma, Abdullahi Shehu ya b su kala biyu na kayan wasa da kwallo biyu domin su motsa jikinsu.
Dan kwallon na Nijeriya, Abdullahi Shehu dan asalin jihar Sokoto ne.


Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24



Abokinsa Ahmad Musa shi ma ya bayar da naira milyan da rabi domin cigaba da hidimar wadannan bayin Allah.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Shugaban hukumar zakka da wakafi na jiha kuma shugaban dauko yaran ne Malam Muhammad Lawal Maidoki ya karbe su a madadin Jarman Sokoto, Dr. Ummarun Kwabo.


Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

A. A Kwamishinan Matasa da Wasanni ne ya jagoranci tafiyar matasan tare da goyon bayan dimbin matasa masu goyon bayan 'yan wasan.

Biography of Ahmed Musa by Muryar Hausa24

Matsayin Halitta da La'akari Kan Jiki

Cikakken Suna: Ahmed Musa

Ranar Haihuwa: Oktoba 14, 1992

Wurin Haihuwa: Jos, Nijeriya

Tsawo: 5 feet 7 inci (170 cm)

Nauyi: 62kg

Rubutawa da Fassarawa tare da tacewa Wakilin Shafin Muryar Hausa24  M. KABIRU MUHAMMAD

Wannan shine cikakken Tarihin Ahmed Musa, zaku iya Aiko Mana da sunan Dan Wasan Kwallon da kuke son a fassara muku Tarihin shi ko mu kawo muku shi matukar duniya ta San shi aika sakon a email din mu muryarHausa24@gmail.com

Hotan yaron Ahmed Musa kamar yadda mu Sami hotan a Shafin mahaifin sa (Wato Ahmed Musa) 

Domin samun Labarai,Nishadi,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya


DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng 

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user