Tuesday 3 July 2018

Karanta Yanzu Kaji: Har Yanzu Ban San Kungiyar Da Zan Koma Ba Inji-Ahmed Musa

Tura Wannan Zuwa
Dan wasan tawagar Super Eagles dan kungiyar kwallon kafa ta Leceister City dake kasar Ingila, Ahmad Musa, ya bayyana cewa kawo yanzu dai bai san kungiyar da zai koma ba domin buga wasa a kakar wasa mai zuwa amma kuma ya ce zai koma kungiyar sa ta Leceister City bayan ya kammala hutu.



Musa, wanda ya zura kwallaye biyu a wasan da kasar Nijeriya ta lallasa kasar Iceland a wasa na biyu da suka fafata a gasar cin kofn duniya dai tuni kungiyoyi suka fara zawarcinsa domin yakoma kungiyar a kakar wasa mai zuwa.

“ Ni ma ban san kungiyar da zan bugawa wasa ba a kakar wasa mai zuwa kawai dai abin da nasani shi ne cewa bayan na kammala hutu zan koma kungiya ta ta Leceister City domin ci gaba da daukar horo don tunkarar kakar wasa mai zuwa” in ji Ahamd Musa.

Kungiyoyi da dama a nahiyar turai sun nuna sha’awarsu na daukar dan wasan wanda yakoma kungiyar CSKA Moscow a matsayin aro a watan Janairun daya gabata kuma cikin kungiyoyin akwai kungiyar Galatassary da ke kasar Turkiyya.

Tuni dai aka fitar da wani hoto wanda ya nuna ‘yar dan wasan tana sanye da rigar kungiyar Galatassary sai dai dan wasan ya ce wannan hoton ba gaskiya ba ne kawai wani magoyin bayan kungiyar Galatassary ne ya hada hoton.

“ Wannan hoton ba gaskiya ba ne kawai hadawa wani magoyin bayan kungiyar yayi saboda yanason in koma kungiyar” a cewar Ahmad Musa.

Tuni dai tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya ta dawo gida bayan data kasa fitowa daga cikin rukunin daya hada da kasashen Crotia da Argentina da kuma kasar Iceland.

Ku Kasance da MuryarHausa24.com.ng aduk inda Ku Kasance domin samun Takaitaccen Tarihin Rayuwar Ahmed Musa.

Domin samun Labarai,Nishadi,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna, Hausa Videos,Wakoki Hausa, Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya


FARIN CIKIN KU SHINE FARIN CIKIN MU

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari  ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: Leadership A Yau
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user