Thursday 23 August 2018

Karanta Cikakken Labarin Donald Trump ya shiga tsaka mai wuya a halin Yanzu

Tura Wannan Zuwa Ga
Kotu a Amurka ta gayyaci tsohon lauyan Shugaban Kasar Donald Trump bisa samun bayanan lauyansa na yanzu cewa, Cohen din yana da wasu muhimman bayanai na Trump.




Kakakin Ofishin Karbar Haraji na New York James Gazzale ya fitar d a sanarwar cewa, sun shaida yadda aka gayyaci Michael Cohen zuwa kotu.

Lauwayn Cohen Lanny Davis ya tattauna da tashar CNN inda ya ce, Cohen ya san wasu muhimman bayanai game da Trump da suka shafi jihohin Washington da New York.

Cohen ya mika kansa ga Hukumar Bincike ta FBI a birnin New York inda bayan sha biyun rana aka kai shi kotu inda aka kuma ce, FBI na son yin yarjejeniya da Cohen saboda muhimman bayanan da ya sani game da Trump.

An kuma bayyana cewar Cohen ya amince da yin sama da fadi da haraji da kudin kamfen zabe.

Trump ya bayyana cewa, an biya dala dubu 130 daga cikin kudin kamfen don yi wa wata mata mai suna Stormy Daniels ado kuma an bayar da kudin ta hannun Cohen, amma a shi kuma Cohen ya bayar da shaida sabanin haka a gaban kotun.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: TRT HAUSA
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user