Saturday 25 August 2018

Karanta Cikakken Labarin Yanzu Jaruma Maryam Mah Zatai Bankwana da Masana'antar Shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood Har'abada

Tura Wannan Zuwa Ga
Jarumar Fina-Finan Hausa (Kannywood) Maryam Abacha wacce aka fi sani da sunan Maryam Mah tayi bankwana da Masana'antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood.

Maryam Mah

Hakan ya biyo bayan karatun da take yi na makarantar gaba da sakandire.

Maryam Mah ɗaya ce daga cikin fitattun Jaruman Kanywood waɗanda tauraruwar su take kan ganiyar haskawa a lokacin da take shirin barin kannywood, duba da yanayin Masana'antar a halin yanzu kannywood tafi buƙatar 'yam mata su'anninta sai ake ganin ita kakarta ta yanke saƙa tinda irin ta ake nema.

Amma abin mamaki a yanzu shine ɗif kamar ɗaukewar ruwa sai aka daina jin ɗuriyar jarumar a masana'anatar kannywood.

Dalilin da yasa wakilin mu bin diddigi ina Maryam Mah ta shiga? Kuma ko me ne ne dalilin da yasa aka daina ganin jarumar a kannywood??

Wakilin namu ya samu tattaunawa da ƙanwar jarumar anan garin kaduna, inda ta tabbatarwa da wakilin namu dalilin da yasa aka daina ganin fitowar jarumar a fina-finan hausa sun yanke shawarar cire jarumar a kannywood dama tin farko sai da su amince sannan tafara yin fim yanzu kuma lokaci yayi da zata daina fitowa a kannywood ta koma karatu.

Maryam Mah

Ga yadda tattaunawar su ta kasance a takaice:

Muryar Hausa24: ko me ne ne jarumar ke yi a halin yanzu?

Ƙanwar Mahaifiyarta: A halin yanzu jarumar tana yin karatu a jami'ar katsina .

Muryar Hausa24: Shin ko wannan yana ɗaya daga cikin  dalilan da yasa aka daina ganin jarumar a kannywood?

Kanwar Mahaifiyarta: Wannan shine dalilin cire ta daga kannywood.

Muryar Hausa24: abin tambaya anan shin idan ta kammala karatun zata dawo masana'antar shirya fina-finan hausa wato kannywood?

Kanwar Mahaifiyarta: Maryam Mah tabar Kannywood har'abada domin kuwa babu dalilin da zaisa ta dawo kannywwod

Wakilin mu yayi iyakar bakin ƙoƙarin sa domin samun zantawa da jarumar amma buƙatar hakan bata samu ba.

Jarumar ta fara shahara ne a fina-finan ta waɗanda su haskata kamar irin su Mata ko ƴa?, Sa'insa da sauran su.

Maryam Mah

Jarumar tana fitowa ne amatsayin matashiyar budurwa amaimakon cikakkiyar budurwa saboda ƙarancin shekarun da take dasu a wancan lokacin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user