Friday 24 August 2018

Karanta Cikakken Bayanin Yadda akai Mawaki Rarara yayi silar Shigar Jaruma Hauwa S. Garba Masana'antar Kannywood

Tura Wannan Zuwa Ga
Hauwa S. Garba wadda aka fi sani da lakabin ‘Mama’ a masana’antar fina-finan Hausa, tana daga cikin jarumai mata masu tasowa a cikin masana’antar, inda duk da cewa ba ta dauki wani lokaci mai tsawo a cikin masana’antar ba, amma za a iya cewa ta shigo masana’antar da kafar dama, musamman idan aka yi la’akari da yawan fina-finan da ta yi da kuma wanda take kan yi a yanzu.


Hauwa S. Garba da Rarara

Aminiya ta tattauna da jaruma kan dalilin da ya sa ta shiga harkar fim da kuma burin da take da shi a masa’anatar, ta kuma bayyana nasorin da ta cimma a harkar fim.

 Ga yadda hirar ta kasance:

Za mu fara da gabatar da kanki…

Hauwa Garba (Mama): Sunana Hauwa S. Garba, wadda aka fi sani da lakabin ‘Mama’ a harkar fim. Dangane da tarihin rayuwata kuwa zan iya cewa, ni haifaffiyar garin Legas ce, kuma an haife ni a shekarar 1999, na yi karatun firamare da sakandare a Legas, daga baya kuma na yi difloma a Maiduguri. Bayan na gama kuma na shigo masana’antar fina-finai ta Kannywood.

Kin ce a Legas aka haife ki, kuma karatunki na gaba da sakandire a Maiduguri kika yi, to yaya aka yi hakan ta faru?

E haka ne, a Legas aka haife ni, amma iyayena ’yan asalin Maiduguri ne, aiki ne ya kai mahaifina can. Sai aka haife ni a can din. Don haka da bayan na kammala sakandire sai aka dawo da ni gida na ci gaba da karatu.

To, yaya aka yi kika samu kanki a cikin harkar fim?

To na samu kaina a harkar fim ne ta dalilin mawaki Dauda Kahutu Rarara. Shi ne silar shiga ta harkar fim, domin lokacin da na zo Kano ina wajen yayan mahaifina a Unguwar danladi Nasidi, sai na ji ina sha’awar yin fim, sai wata ’yar’uwata take cewa ta san Dauda Rarara, sai ta kawo ni wajensa. To da muka zo sai ya fada mini cewa shi ba fim yake yi ba, amma dai zai hada ni da masu yin fim. Daga nan ya hada ni da su Usman Mu’azu, daga nan sai aka shigar da ni. Bayan na cike duk wasu ka’idojin da ake bi kafin a shiga harkar fim sai na zama ’yar fim kuma jaruma.

A wace shekara kika shigo, kuma wadanne fim kika fara yi?

Na shiga harkar ne a karshen 2014, kuma fim din da na fara yi shi ne ‘Duniya Labari’ wanda furodusa Usman Mu’azu ya yi mini.

Daga lokacin zuwa yanzu fina-finan da kika yi za su kai kamar nawa?

To daga lokacin da na fara yi zuwa yanzu fina-finan da na yi za su kai kamar 40, duk da cewa ba zan iya kawo sunansu duka ba, amma zan iya kawo sunan wasu kadan daga cikinsu kamar ‘Rumfar Shehu’ da ‘Gobarar Mata’ da ‘Malam Zalimu’ da ‘Gidan Abinci’ da dai sauransu.

Hauwa S. Garba

A cikin fina-finan da kika yi wanne ya fi burge ki?

To, gaskiya duk fina-finan da na yi suna burge ni, amma dai wanda ya fi burge ni kuma ya fi canza mini tsarin rayuwata ta fim shi ne ‘Rumfar Shehu’, saboda na fito a matsayin matar Bayerabe, kuma ni ma a matsayin Bayerabiya. To wannan rol din ya burge ni saboda abu ne wanda ban taba yinsa ba. Da farko ma na yi zaton ba zan iya ba, sai kuma na ga na yi shi. Kuma na bayar da abin da ake so.

A yanzu a matsayinki wadda kika saba da harkar fim, yaya za ki kwatanta rayuwarki ta kafin ki fara fim da kuma yanzu da kike a matsayin ’yar fim?

Gaskiya rayuwar ta bambanta sosai. Saboda a da da ba a san fuskata ba zan iya fita na yi harkokin rayuwa yadda nake so babu wanda ya kula da ni, to amma yanzu ba zai yiwu ba, saboda an san fuskata duk inda na je don haka dole wasu abubuwan sai ka rage don komai naka ba zai zama a boye ba, kowa ya saka maka ido ne.

To ganin yanzu kin zama cikin jaruman da ake damawa da su za a iya cewa kin cimma burinki?

E to, zan iya cewa na cimma, amma dai da dan saura har yanzu. Don haka muna fatan Allah Ya cika mana burin da nake da shi.

Hauwa S. Garba

To wai wanne burin ne ma kike da shi a harkar fim?

To, ka san duk harkar da mutum yake yi akwai wani burin da yake da shi a kansa. Ni burina a harkar fim farko na fadakar kuma alhamdulillah, ko yanzu na yi abin da na yi. Baya ga haka duk harkar da mutum yake yi yana son ya zama fitacce, don haka ina da burin na zama fitacciya a cikin harkar fim wadda ake yayi a cikin mata. Sannan ina da burin yadda na fara harkar lafiya na yi aure na bar harkar lafiya.

Wani lokaci idan mutum zai fara harkar fim yakan samu matsala daga gidansu ta wajen nuna rashin amincewa da shigarsa harkar.

Ko ke ma kin samu irin wannan matsalar?

To ni gaskiya ban samu matsala ba, saboda tun da farko sai da na sanar da su kuma suka nuna amincewa. Kuma ko da na shigo masana’antar ma ban samu wata matsala da su ba. Amma ina ji dai daga bakin ’yan’uwa irin matsalar da suke samu idan sun shigo.

Hauwa S. Garba


Me ya fi ba ki sha’awa a rayuwarki ta harkar fim?

To ni abin da ya fi ba ni sha’awa dai shi ne na gan ni cikin abokan aikina idan mun je lokeshin mu hadu muna ta wasa da dariya.

Ko kina da ra’ayin nan gaba ke ma ki shirya fim naki na kanki?

Sosai ma kuwa, ina da wannan burin, domin ai ci gaba ne idan kana sana’a kai ma ka yi na kanka ya fi, don haka nan gaba kadan idan na samu dama zan yi.

Me kika dauki harkar fim?

To ni harkar fim na dauke ta sana’a, domin ko a yanzu na samu alheri a cikinta, kuma ban san abin da zan samu nan gaba ba.

Kina cewa ba ki san abin da za ki samu nan gaba ba, wani sai ya dauka kin shiga harkar ne babu ranar fita. Ko haka din ne?

To kamar yadda ban san shiga ba, kuma da lokacin ya yi sai Allah Ya shigo da ni, haka ma fitar sai ranar da Allah Ya nufa. Ko ina so ko ba na so haka zan bar harkar fim wata rana.

Mene ne sakonki na karshe?

Sakona shi ne ina yi wa kowa fatan alheri, kuma yadda na fara harkar nan lafiya Allah Ya sa in gama lafiya.

Hotuna daga shafin www.MuryarHausa24.com.ng ku ci gaba da kasancewa damu domin samun tarihin jaruman kannywood dana bollywood.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki 

Mungode

Source: Aminiya 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user