Thursday 27 September 2018

KARANTA KAJI: TARIHIN ASALIN ZAMFARAWA

Tura Wannan Zuwa
Birnin Dutsi wanda a halin yanzu yake ƙarƙashin Masarautar Zurmi dake Jahar Zamfara, nan ne akace Zamfarawa suka Fara yada zango, a lokacin da suka riski ƙasar Hausa daga wurin zaman su na asali dake Gabas ta tsakiya.


Marubuci: Hon. Ibrahim Ɗan madamin Birnin Magaji

Jagoran su, da ake kira Dakka ne ya fara Sarauta a wannan Gari na Dutci/Dutsi a wajajen Shekarar 1300 AD.

Ance Waɗan nan Mutanen (Zamfarawan Farko ) masu tsayi ne da girman jiki sosai , kusan wannan ne dalilin da ke sanyawa ana alaƙan ta su da Jinsin Samudawa.

Haka kuma Kaburburan su da ke Dutci /Dutsi a halin yanzu ma wani babban misali ne na irin girman Jikin nasu.

Bayan Mutuwar Sarki Dakka Wanda shine Mahaifin Sarauniya Argoje/Yargoje, an yi Sarakuna biyu kafin ta samu damar ɗarewa kan Karagar Mulki.

Ance Ƴargoje tayi Mulki a tsakiyar ƙarni na 13 miladiyya.

Kuma ta Shahara a lokacin ta , domin har a dajin Kuyambana da ke ƙasar Ɗansadau ta Jahar Zamfara ta yanzu takan Zauna da Majalisar ta , tana yanke hukunci akan lamurran da suka shafi al'ummar ta.

A Yanzu haka akwai wata fitilar ta da ke ajiye a ginin hukumar Adana Kayan Tarihi da al'adun Gargajiya na Jahar Zamfara wanda ake dangantawa da ita.

Bayan Rasuwar ta a Dutci /Dutsi sai aka naɗa ƙanenta mai suna Bakurukuru a matsayin Sabon Sarki.

Sarki Bakurukuru ɗan Dakka ne ya ƙirƙiri Sabuwar Hedikwatar Zamfarawa, Mai Suna Birnin Zamfara daga ƙarshe-ƙarshen ƙarni na 13 zuwa farko-farkon ƙarni na 14 , shune silar da zamfarawan suka tashi daga Dutci/Dutsi zuwa can Birnin Zamfaran, inda sunan Gonar Alkalin Zamfarawan ya amshe sunan Birnin na Zamfara.

A Wannan Wuri ne suka yi Mulki har lokacin da Gobirawa suka ƙwache Birnin daga hannun su a cikin ƙarni na 17.

Zamu ci gaba Insha Allah.

Karanta Kaji: Takaitaccen Tarihin Yaren Harshen Hausa 

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng aduk inda ku Kasance a faɗin Duniya domin samun sahihan Tarihi Daban-Daban a faɗin Duniya.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user