Monday 24 September 2018

YANZU-YANZU: LABARAI DA DUMI-DUMIN SU A TAKAICE HAR GUDA 10 - KARANTA SABABBIN LABARAI 10 DA SUKA FI DAUKAR HANKULAN DUNIYA SOSAI

Tura Wannan Zuwa Ga
1- Ahmed Makarfi yace shine d'an Takara kad'ai da Jam'iyar APC ke Tsaron A tsayar da shi ta Karar Shugaban kasa A Jam'iyar PDP cikin 'yan Takarkarunsu na PDP


Marubuci Usman Rangis Mawallafi Hadejia

2- Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alh Namadi Sambo yace ko Nadama ba yayi dan ya zama Mataimakin Shugaban kasa akarkashin Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan dan haka ma' shi Alfahari yake yi

3- Majalissar Dattije da ta Wakilai sun sake dage zaman Majallissar wanda suka shirya zasu dawo A Gobe Talata 25 ga watan Satumba Inda yanzu haka suka sake dage Zaman Majalissar har Ranar 9 ga watan Oktoba, Majaliisar ta bada dalilin cewar za'ayi zabukatan fitar da Gwani ne a wasu Jam'iyun kasar


4- Wasu 'yan Bindiga Sun Sace Mutane 7 a kauyen Nahuche a can karamar hukumar Bungudu dake jahar Zamfara inda suka Nemi abasu Miliyan Dari 100 kuma daga cikin wadanda suka sace har da tsohon Kansila Bello Daniya

A wani Labarin ma' A can Jahar Lagos ma' wasu 'yan Bindigar ne suka sake sace wasu fararen fata Goma sha 12 akan hanyarsu daga Lagos zuwa jahar Rivers, Bakwai 7 daga cikinsu 'yan kasar Philippines ne sauran kuma akwai 'yan kashashen Slovenia,Ukraine,Romania,Croatia,Bosnia

5- Dr Rabiu' Musa Kwankwaso ya fitar da Sirinkinsa Abba Kabir A Matsayin wanda yake son a tsayar dashi Takarar Gwamnan jahar ta Kano a karkashin Tutar Jam'iyar PDP haka zalika ya sake tsayar da wasu Surukan nasa Muktar Yerima da Nasiru sule Garo a Matsayen wadanda zasu tsaya takarar Majalissar wakilai, Tini dai wannan Mataki da ya dauka ya fara kawo rikici a jam'iyar tasu a jahar Kano

6- Jam'iyar APC ta sake Dage Ranar da ta shirya dan fitar da Gwani a matakin Shugaban kasa kamar yadda ta shirya zatayi ranar 25 A Gobe talata Amma sabida Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ya kasar ta dage har sai ranar 27

7- Gobara ta Tashi agidan Tsohon Gwamnan jahar Kano Malam Ibrahim Shekarau agidansa dake Unguwar Mundubawa inda Gobarar ta shafi Dakuna biyu 2 na gidan sakamakon Had'uwar da Wutar Lantarki tayi

8- Shugaban Jam'iyar PDP na kasa Chief Uche Secondus yayi watsi da Matakin da hukumar Zabe ta INEC ta dauka akan sake zaben wasu Mazabun, Inda ya Bukaci kawai hukumar zaben ta Amince da Mr Ademola Adeleke na Jam'iyarsu ta PDP da cewar shiya lashe zaben jahar ta Osun

9- A karon Farko cikin Shekara uku 3 Ma'aikatan jahar Kogi zasu karbi Albashinsu kashi 54% inda abaya kawai suke karbar kashi 22% zuwa 30%,

Gwamnan jahar ta Kogi Yahya Bello yace a hankali a hankali Ma'aikatan zasu karbi kashi 100% su


10- Tsohon Mataimakin Shugaban kasa kuma wanda ke son Jam'iyar PDP ta tsayar dashi takarar Shugaban kasa Alh Atiku Abubakar yace shi bashi da Matsala da Chief Olusegun Obasanjo Amma har idan shi yana Ganin Akwai Matsala a tsakaninsu To Matsalarsa ce

Menene Ra'ayinku ko wani labari ne yafi Jan hankalin ka/ki?
.
Ku ci gaba da Kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng domin samun cikakkun labaran akan lokaci.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki 

Mungode


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user