Sunday 28 October 2018

Karanta Aure Ko Zina?

Tura Wannan Zuwa Ga
A yau idan ka ce za ka yi aure, daga ranar da ka fara fafutuka, zuwa ranar aurenka, in ba kai wasa ba sai wando ya daina zama a qugunka saboda tsadar aure tun daga sadaki, kayan lefe da kudin gaisuwar uwa da uba da sauran su.


Marubuci: Mal. Muhammad Nazifi Hashim Samaru Zaria.

Wannan ya sa samari da dama suka kasa yin aure.

Amma a yau idan ka yi niyyar yin zina a rana daya (in dai za ka iya yi) da mata 20 ko sama da haka za ka iya yi. Sannan kuma kudin da za ka kashe ba zai taka kara ba ballantana ya karya shi. Kai wasu ma ko sisi ba sa kashewa, kyauta sukeyi saboda yan matan gasu nan kamar jamfa a Jos, kuma suna bukatar auren amma samari ba kudi, iyaye kuma sai mai kudin suke so.

Wannan ya sa aka taru aka hada karfi da karfe tsakanin samari da yan mata da kuma iyaye ake ta sabawa Allah kullum.

Na daga cikin abubuwan da za su kawo karshen zinace-zinace shi ne farashin aure ya fado kasa warwas!, Domin babban abun
bukata a aure shi ne sadaki, shi ma
idan babu shi ana iya badawa bashi, duk fa Musulunci ya yi haka ne domin a rage fasadi a doron kasa.

A haqiqanin gaskiya tun da na tashi ban taba gani ko jin labarin an daura aure bashi ba. Kai hasali makowacce shekara farashin aure qara tashi sama yake kamar gwauran zabo.

Sai dai nasan farashin sadaki yana yin tsada ne bisa dalilin talauci da ake fama da shi. Sakamakon wasu iyayen suna karawa kudin yawa nedomin suyi wa yarsu kayan daki dan a fita kunya.

Ita kuma kunya ana so a fice ta ne a gurin yan gutsiri-tsoma, wadanda idan ba a yi wa yarinya kayan a zo a gani ba za su bi unguwa suna gulmace-gulmace, karshe ya koma gori wajen amarya da iyayenta.

Wannan yasa iyaye ke tsauwala kudin sadaki da abubuwa makamanta wannan.

To amma, sai suka manta cewa ita
kunya ta Ubangiji ake gudu, ba ta
wani ba.

Domin idan diyarka tayi cikin shege a gidanka sai ka fi kowa jin kunya a duniya, kuma wannan shi ne abin kunya da ake gudu, amma ba kunyar kayan lefe ko sadaki ba.

Kalli abinda waɗannan 'yam mata da samarin su aikata kalla kasha mamaki...

DOWNLOAD VIDEO HERE

Muryar Hausa24 Allah ya kare mana zuri'ar mu baki ɗaya Amin.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user