Sunday 14 October 2018

Karanta Kaji: Babban Dalilin da Yasa Buhari Haramtawa Mutane 50 Fita Kasashen Waje

Tura Wannan Zuwa
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya fitar da wata doka da ta haramtawa wasu 'yan kasar su 50 fita kasashen waje.


Wadannan mutane ana tuhumar su ne da yin ruf-da-ciki da kudin kasa, abin da ya sa aka umarci jami'an tsaro da su sa ido a kan su don kar su samu damar sulalewa su bar kasar.

Mai magana da yawun shugaban kasar kan harkokin watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa, shugaban kasar ya dauki matakin ne bisa la'akari da cewa akwai wadanda gwamnati da kuma sassa daban-daban na bincike na hukumomin Najeriya ke gudanar da bincike a kan wasu makudan kudade a gida da waje, abin fargabar inji Garba Shehu, shi ne kada su je su salwantar da wadannan kudade kamar yadda ya faru da wasu a baya.

Garba Shehu, ya ce to dakatar da su daga zuwa wajen inda suka ajiye ko boye wannan dukiya a waje saboda kada su salwantar da ita ta yadda ba bu wanda zai amfana, shi ya sa aka fitar da dokar.

Mai ba wa shugaban Najeriyar shawara, ya ce zirga-zirgar da aka hana irin wadannan mutane, na da tasiri a shari'ance.

Garba Shehu ya ce duk wanda ya san bai dauki kayan jama'a ya mallakawa kansa ba, to ba shi da wata fargaba dangane da wannan sabuwar doka.

A wani labarin kuma, tuni dai babbar jam'iyya adawa a Najeriya PDP, ta yi watsi da da matakin da shugaban kasar ya dauka na sanya hannu kan wata doka da ta haramta wa wasu 'yan kasar su 50 fita waje, saboda zargin cin hanci da rashawa.

Jam'iyyar ta yi zargin cewa an kafa dokar ne don takura wa wasu 'yan PDP da za su iya kawo cikas ga takarar shugaba Buhari a zabe mai zuwa.

Tuni dai kungiyoyin da ke fafutukar yaki da rashawa suka ce wannan mataki da shugaban Najeriyar ya dauka na kafa dokar haramta wa wasu 'yan kasar fita kasashen waje ta yi dai-dai.

Malam Abdulkarim Dayyabu, shi ne shugaban rundunar Adalci ta Najeriya, ya kuma shaida wa BBC cewa, wannan mataki da aka dauka abune da yakamata, har ma na so a makara wajen daukarsa.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: BBC HAUSA
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user