Wednesday 31 October 2018

Karanta Kaji: Duk ’Yan Halak Din Kannywood ’Yan Kwankwasiyya Ne Inji- Jarumi Mustapha Naburaska

Tura Wannan Zuwa
Fitaccen jarumin finafinan Hausa, MUSTAPHA BADAMASI, wanda a ka fi sani da MUSTAFA NABURASKA , ya yi fice a masana’antar ta Kannywood, musamman a bangaren fitowa cikin finafinan barkwanci.


 Ya dade ya na jan zarensa a masana’antar a cikin ‘yan wasan barkwanci, domin kuwa ko a shekarun baya, bayan rasuwar uban gidansu Marigayi Rabilu Musa Dan Ibro, akwai lokacin da Mustafa Naburaska tauraruwarsa ta fi ta kowa haske a cikin jaruman na barkwanci.

Duk da kasancewarsa fitaccen jarumi, Mustafa Naburaska za a iya cewa shi tudu biyu yake ci domin kuwa a fagen siyasa ma jarumin tauraruwarsa tana haskawa.

Domin jin ko wane ne Mustafa Naburaska a fagen fim da siyasa, sai ku biyo mu ku ji tattaunawar da LEADERSHIP A YAU LAHADI ta yi da shi a Kano.

Da farko za mu so ka gabatar da kanka ga masu karatunmu.

To ni dai sunana Mustafa Badamasi, wanda duniya ta fi sani da Mustafa Naburaska kuma dai a game da tarihin rayuwaa duk wanda yake bibiyarmu zan iya cewa abu ne da yake a bayyane amma dai ni haifaffen garin Kano ne an haife ni a cikin garin Kano na yi karatuna na firamare da sakandire a Kano kuma na je Zariya na yi karatu a yanzu dai shekaruna na haihuwa arba’in ba kadan.

To masu karatunmu za su so jin yadda ka fara harkar fim da har ta kai a yanzu ka shahara a fagen.

Ina ganin za a iya cewa da ga lokacin da na fara harkar nan ta fim ni ban ma shigo da niyyar na zama jarumi ba, na zo da niyyar na zama ko dai marubuci ko furodusa ko dai wani da ya ke ba da gudunmawa ta wata hanyar da ba ma sai an haska shi ba, ni dai bukatata mu hadu mu magance matsalolin da suke damun matasa maza da mata a cikin al’ummarmu, wannan ya ja hankalina da shigowa masana’antar domin ba da tawa gudunmawa, amma cikin ikon Allah sai ga shi na samu kaina a matsayin dan wasan barkwanci, wanda a yanzu cikin ikon Allah Ina daya daga cikin wadanda za a kalla a ce wane na daga cikin ‘yan wasan barkwanci.

A matsayinka na dan wasan barkwanci daman can shi ka fara ko kuma ka yi finafinai da ake cewa na ‘yan birni?

Eh, to, haka ne, na fara ma da su ne duk da yake suna da yawa kuma a yanzu ana maganar kusan shekaru 18 da farawa, ka ga ba zan iya tuna abin d ana fara yi ba, amma dai babban kamfanin da yake na iyayen gidana shi ne na su Sani Danja da Yakubu Muhammad, sun ba ni gudunmawa sosai kuma har gobe ina alfahari da su, don ba ni da iyayen gida sama da su a cikin harkar fim duk da cewar daga baya na koma bangaren Rabilu Musa Ibro inda daga nan na koma na zama dan wasan barkwanci.

To da ya ke ka taba bangare biyu na harkar ta fim da na soyayya da kuma na barkwanci, wanne ka fi jin dadin gudanar da shi?

Ai babu fim din da na fi jin dadin gudanar da shi kamar na barkwanci, saboda shi yayin ake da dora mu a sake mu mu yi yadda muke so, amma shi wancan ko an rubuta an ce ka gamsar da dan kallo ba za ka iya ba amma shi na barkwanci yanzu z aka gamsar da mai kallo.

Harkar fim ta ba ka dama da yawa ba mamaki har ma da tafiye-tafiye, ko wanne kasashe ka ziyarta?

To, gaskiya kasashen da na je ta dalilin wannan harkar fim tana da yawa, ka ga dai ni ma’abocin zuwa kasa mai tsarki ne, kuma na je Dubai, na je Amerika, na je Ingila, na je Afirka ta Kudu, da sauran kasashe wanda yawon bude ido ne ya kai ni, wasu ku ma karramawa ce ta kai ni.

To, ya ya ka ke gudanar da rayuwarka a zahiri tare da mutanen da suke ganin ka na fitowa a cikin fim?

Eh, gaskiya da yake a zahiri ni na kasance mutum ne da na ke boye kaina ba don komai ba sai don ga ka dai mutum amma idan ka shahara to rayuwa a cikin al’umma ba za ta yiwu ba, sai ka samu wani waje ka kebe kanka daga cikin jama’a, yadda in ka ga mutum tare da kai to shi ne ya zo wajenka ba kai ne ka zo wajensa ba, don haka mun fi yin mu’amalarmu da daddare, don ba don harkar siyasa da na ke yi ba, to da zai zama ba ni da kusanci da jama’a. To, amma harkar siyasa ta sa Ina shiga ko’ina.

To amma a yanzu an dan samu lokaci ba a ganin ka a harkar fim ko hutu ka tafi?

Eh, ba hutu na tafi ba, daman ni tsarina duk lokacin da aka kada gangar siyasa to nakan dauke kafa daga harkar fim na shiga harkar siyasa gadan-gadan. Sai kuma an gama na koma harkokina na fim.

Amma dai duk da kasancewarka dan siyasa ana ga nin ka a matsayin wanda ka dauki layin bin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Gaskiya ne, ni siyasar gidan Sanata Kwankwaso nake yi, kuma duk wanda yake harkar fim zan iya cewa Kwankwaso uba ne a gare shi, domin kuwa tun daga lokacin da ya hau gwamna har na farko ya fara shiga cikin ‘yan fim ya zame musu uwa da uba ta hanyar inganta sana’arsu don haka ma ko da ya fadi shekaru takwas sai da ’yan fim su ka shiga cikin kunci, don ina cikin ’yan fim din da kotu ta sa kudi duk wanda ya kawo ni za a ba shi wannan kudin, hakan ya sa na yi hijra daga Kano na koma Kaduna har sai da gwamnatun Shekarau ta kare mu ka dawo Kano mu ka ci gaba da zaman mu, kuma da Kwankwaso ya ci ya kara kiran mu mu ka zauna ya kara mayar da mu mutane ya yi mana abubuwa masu yawa na alheri wanda duk dan halak a cikin harkar ba zai manta da shi ba, don haka na dauki wannan tsarin na tafiyar Sanata Rabi’u Kwankwaso shi ne garkuwa a wajena shi ne ginshikina, don haka shi ne ubangidana a siyasa, kuma mu na nan da yawa masu akidar Kwankwaso a cikin ‘yan fim duk wanda ka gani a wani layi, to cirani ya kai shi, amma dai hakan bai hana wani ya dauki layin da ya ke ganin ya fi ma sa daidai ba.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: LEADERSHIP A YAU

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user