Wednesday 31 October 2018

Karanta Kaji: Kuskure 6 da akai a cikin Film ɗin KAUYAWA 2018 tare da Sharhin Fim ɗin

Tura Wannan Zuwa
Suna: Kauyawa 2018
Tsara Labari: Maje Elhajj Hotoro
Kamfani: Mai Shadda Inbestment da Alrahuz Film Production
Shiryawa: Ali Worth Me
Umarni: Sadik N. Mafiya


Jarumai: Aminu Shariff Momo, Falalu A. Dorayi, Sulaiman Bosho, Rabi’u Rikadawa, Abubakar Dan Auta, Baballe Hayatu, Musa Mai Sana’a, Rabi’u Daushe, Jamila Umar Nagudu, Fatima Kokobi, Fati Abubakar Shu’uma, Iliyasu Abdulmumini Tantiri, Alasan Kwalle, Aliyu Rara, Tijjani Asase. Da sauran su.

Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an nuna (Fatima Kokobi) ta fito tsakar gida sai ta tarar da akuyar ta a daure, kuma an saka kwado an kulle da makulli, kasan cewar ta kurma sai ta tambayi mahaifiyar ta (Binta Kofar Soro) don jin wanda ya daure mata akuya, amma itama mahaifiyar ta wadda itama kurmar ce, sai ta nuna bata san wanda ya daure akuyar ba, adaidai sannan ne mahaifin yarinyar wato Subullu (Abubakar Dan Auta) ya fito daga cikin bandaki gami da nuna mata ya san wanda ya daure akuyar, a sannan suka dunguma suka nufi wajen Haladu (Falalu A. Doray) wanda ya nuna shi ya daure akuyar saboda idan an saketa tana yawo a gari tana yiwa jama’a barna, anan dai Subullu ya nuna lallai sai an saki akuyar don farantawa ‘yar ta sa rai.
Daga nan ne kuma aka nuna Huwaila (Fati Shu’uma) t agama kwalliya a cikin gidan su za ta dauki tallan goro da sigari, a sannan yayan ta makaho ( Sulaiman Bosho) ya shigo suka soma hira shi da mahaifiyar sa Subulluwa (Jamila Nagudu) suka nuna kushen sana’ar da Huwaila take yi saboda karuwai ne ke tallan goro da sigari, hakan yasa Huwaila da yayan ta makaho (Sulaiman Bosho) suka fara sa’insa, ganin haka ne yasa yayan nata ya dauki kyautar kudi ya bata don su daina rigimar saboda sanin cewa akan kudi za ta iya yin komai. Wata rana (Aminu Shariff Momo) yayi sallama da matar sa ya fita wajen aiki, sai wani barawo (Musa Mai Sana’a) ya nufo gidan sa don yin sata, zuwan sa ne sai ya tarar da kwarto yaje kwartanci wajen matar gidan, barawon ya labe jin tattaunawar da kwarton suke yi da matar gidan sai ga mijin ta ya dawo gida ya hango sa a jikin Katanga, hakan ne yasa ya nufo sa don ya kama sa, saidai kafin ya iso wajen ne kurma ‘yar subullu ta biyo akuyar ta cikin gidan da gudu da nufin kama ta, jin guje-gujen akuyar da kurmar ne yasa kwarto (Rabi’u Daushe) suka fito daga cikin daki a guje shi da matar gidan, wanda hakan kuma sai ya firgita barawon suka fice daga gidan a sanda me gidan (Aminu Sharif) yabi bayan su da nufin ya kama su gaba daya. A wannan lokacin ne kuma me unguwa (Aliyu Rara) ya tsiro da dokar kara haraji a cikin kauyen, yayin da ‘yan fadar sa su (Tijjani Asase) suka goyi da bayan sa, sannan suka dauke sa a kafadar su kasan cewar sa guntu suka nufi cikin gari das hi da nufin sanar da dokar sat a karin haraji, a sannan ne Haladu (Falalu A. Dorayi) ya taho da gudu akan abin hawa ya buge me unguwa ya baje a kasa, ganin hakan ne yasa ‘yan fadar sa suka bi bayan Haladu da nufin kama sa, suna cikin gudu ne Haladu ya hadadu da kwarto da barawo (Musa Mai Sana’a) da (Rabi’u Daushe) wadanda (Aminu Shariff) ya biyo su saboda sun shiga gidan sa yin kwartanci, haduwar su ne yasa suka gudu gaba daya suka buya a cikin wata bukka har sai bayan wadanda suka biyo su sun tafi sannan suka fito suka sake guduwa, a sannan ne ‘yan fadar me unguwa suka kama Haladu suka nufi wajen me unguwa da su. Yayin da su kuma barawo da kwarton da (Aminu Sharif) ya biyo suka buge su Jatau (Rabi’u Rikadawa) wanda ya zauna suke caca da abokan sa.
Ganin an buge su ne suka tsorata duk suka arce a guje, duk suka nufi gidan kwarto (Rabi’u Daushe) shigar su cikin gidan ne har suka buge dan (Rabi’u Daushe) yaron ya karye, yayin da (Aminu Shariff) ya kama su, kuma iyalan kwarton bayan sun ji abinda mijin su ya aikata suka yi tur da halin sa. A bangaren Jatau (Rabi’u Rikadawa) sai ya shawarci matar sad a nufin su dauki da gidan su da suke zaune a ciki gami da gidan yayan ta Subullu (Abubakar dan Auta) da nufin a su saka gidajen a caca don su cinye ainahin gidan abokan sa wanda su ma za su saka gidajen a caca. Jin hakan sai ta amince kuma shima yayan ta Subullu ya amince da hakan suka dauki gidajen suka saka a cikin caca.

Abubuwan Birgewa:

1. Fim din ya nishadantar sosai gami da rike hankalin me kallo don son sanin abinda zai faru a gaba.

2. Daraktan yayi kokari wajen nuna kwarewa akan aikin sa, kuma yayi kokarin ganin jaruman sun yi abinda ya dace da labarin, kuma jaruman sun yi kokari wajen taka rawar da ta dace.

3. An yi kokari wajen samar da wuraren da suka dace da labarin.

4. Sauti ya fita radau, camera ma ba laifi.

Kurakurai:

1. Lokacin da Huwaila (Fati Shu’uma) ta taho dauki da farantin siyar da sigari, a sanda za ta hadu da ‘yar gidan jitandara sanda za ta bada mata yaji, Camera tayi rawa sosai a farkon bude scene din sanda Huwaila ke tafe da farantin talla a hannun ta.

2. Lokacin da kurma ta biyo akuyar ta cikin gidan Jatau dan caca, a sanda ta tunkude Subulluwa (Jamila Nagudu) har ta fadi kasa kurma kuma ta fita, daga nan aka dauke scene din aka cigaba da labari sai bayan tsahon lokaci aka sake dawowa scene din aka nuna Subullu a kasa inda aka jefar da ita tana kokarin tashi tsaye, tsahon lokacin da aka dauke scene din a farko yayi tsahon da bai kamata ace sai a sannan za’a sake nuno wajen ba, domin yin hakan tamkar dawo da mai kallo baya ne akan abin da yayi zaton cewa ya jima da wucewa.

3. Me kallo yaga an nuna wasu ‘yan sanda sun kama wani mai mashin wanda ba shi da takardun mashin, a sannan ne aka ga Haladu ya zo sanye da kayan sojoji yana yi musu shirme. Shin ‘yan sandan ba sa fahimtar mutum me ilimi ne? Tun da an nuna Haladu mutum ne mara ilimi wanda yake yiwa jami’an tsaron shirme, ya dace a nuna mamaki a fuskokin jami’an tsaron na ganin soja haka wanda bai san kalma ta turanci ko guda daya ba.

4. Bayan Haladu ya buge me unguwa (Aliyu Rara) har ‘yan fadar sa su (Tijjani Asase) suka bi sa suka kama sa. Shin bayan an kama sa din wane hukunci aka yi masa? Tun da an nuna yadda ‘yan fadar suka shiga lungu da sako don su kamo Haladu, to ya dace a nuna irin hukuncin da suka yi masa.

5. Me kallo ya ga Haladu ya dauki wasu kayan sojoji a jikin Katanga ya saka a jikin say a fita yin barazana. Shin kayan sojojin na wanene? Tun da ba’a nuna soja ko sau daya a cikin kauyen ba, to ya dace a samar da dalilin ta yadda aka samar da kayan.

6. An nuna Jatau (Rabi’u Rikadawa) tare da abokan sa su Jitandara dasu Subullu duk sun saka gidajen su a caca, sai dai kuma har fim din ya kare ba’a nuna karshen cacar don bayyana wanda ya ci gasar ba.

Karkarewa:

Fim din ya nishadantar kuma ya ja hankalin masu kallo, sai dai kuma babu wani muhimmin darasi wanda kai tsaye mai kallo zai karu dashi, domin an nuna abubuwa na rashin tarbiyya wadan da jama’a suke aikatawa, amma ba’a bayyana hanyoyin gyaran su ba, sannan kuma labarin bai dire har karshe ba, domin akwai abubuwan da ba a kammala tare da karkare su ba. Wallahu a’alamu!

Karanta Kaji: Kuskure 6 da akai a cikin Film ɗin WATA RUGA tare da Sharhin Fim ɗin

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: Leadership A Yau

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user