Saturday 13 October 2018

KARANTA JERIN SUNAYEN FITATTUN MAWAKAN HAUSA HIP HOP 10 DA YAKAMATA KUSAN SU

Tura Wannan Zuwa Ga
Idan har shekarunka sun haura Talatin da biyar ba lallai bane kasan wadannan mutanen dana saka hotunansu, sai dai ina da yakinin danka ko kaninka in har yakai shekara 16 zuwa 25 cikin kankanin lokaci zai zayyana maka sunayensu, kuma zai iya reromaka baituka daga cikin wakokinsu.Marubuci: Rabiu Biyora

Su dai wadannan matasan sune wadanda suka fi samun nasara wajen isar da sako cikin sauki ga miliyoyin zuciyoyin matasan arewa dake tasowa.

1.. Morell.... fitaccen mawakin Hausa Hip hop wanda aka haifa a jihar Bauchi....

2.. Kheengz... Fitaccen Mawakin Hausa Hip hop daga garin Minna Jihar Niger..

3.. IBN.... Fitaccen mawakin Hausa Hip hop daga garin Jos jihar Plateau...

4..Vblaiz... Fitaccen mawakin Hausa Hip hop daga garin Jos jihar Plateau...

5..DJ Abba... Fitaccen mawakin Hausa Hip hop daga Jihar Kaduna....

6..Al'Chaddas... Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop wanda aka haifa a birnin London amma ya dawo Garin Jos da zama inda yake fitar da wakoki da harshen Hausa duk da cewa Igbo ne shi.

7.. Hafeez.... Shima fitaccen mawakin Hausa Hip hop ne daga jihar Kaduna.

8..Dr Smith... Gawurtaccen mawakin Hausa Hip hop daga Jihar Plateau...

9.. BOC Madaki.... Daya daga cikin mashahuran mawakin Hausa Hip hop dake sace zukatan matasan Arewa a wannan lokacin, daga jihar Bauchi yake....

10..CLassiq... Shine mawakin da aka sani musammam saboda wakar dayayi tare da Rahama Sadau wacce tasa har aka dakatar da ita daga harkar film, shima daga jihar Bauchi yake...

Fitattu Goma kenan da babu kamarsu yanzu haka a cikin mawakan Arewa, duk da cewa tasirinsu ya sanya kusan kowacce unguwa dake arewa yanzu ana samun sabbin mawakan Hausa Hip hop dake tasowa....

Zamani ne yazo da hakan, sai dai dayawan manyan Yan Arewa musammam musulmi sun kasa fuskantar wannan sabon lamarin da kawar dashi zai iya zama da wahala, kuma sun kasa temakawa matasansu da suka samu kansu a wannan sabon layin dake samar da aikinyi tare da manyan kudade gasu matasan dake wakokin.....

Da ace zamu fuskanci matsalar cikin hikima da mun karfafa musu gwiwa musammam wadanda suke asalin Hausa/Fulani, kunga zasu dinga kare yarenmu da addininmu a cikin wakokinsu maimakon ace mabiya wani addinin ne suke wakiltarmu kuma a yaren da kaso tamanin na masu yinsa musulmi ne.....

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user