Shahararriyar kungiyar bincike da tona asirin cin hanci da rashawa mai suna Citizens United For Peace and Stability in Nigeria (CUPS) karkashin jagorancin Professor Dr. Idris Ahmed ta bankako wasu bayanan cin hanci da rashawa da zamba cikin aminci wanda gwamnatin Amurka take tuhumar tsohon mataimakin shugaba Kasa Atiku Abubakar da aikatawa.
Marubuci: Datti Assalafiy
Wani kakkarfan kwamitin bincike na sanatocin Amurka ne suka gudanar da binciken wanda akwai dogon bayanai mai dauke da shafuka dari uku da ashirin da takwas (328) wanda yake kunshe da bayanan yadda Atiku Abubakar ya sace arzikin Nigeria sama da dalar amurka miliyon arba'in ($40,000,000) kimanin naira biliyan goma sha biyar da miliyan dari bakwai da hamsin (N15,750,000,000)
Atiku Abubakar ya boye wadannan makudan kudade ne a kasar Amurka ta hannun matarshi ta hudu mai suna Mrs Jennifer Doglas Abubakar wanda tayi karyan cewa ita dalibace a wancan lokacin, sai yasa ta bude asusun ajiyar banki (bank account) guda 30 a can kasar Amurka domin ya boye kudaden.
Wannan dalilin ne yasa har abada Atiku Abubakar bai isa yaje Kasar Amurka ba saboda zasu cafkeshi, duk da yana da manyan kadarori da biliyoyin naira da ya jibge a kasar ta Amurka, mai son ya karanta cikakken labarin ya shiga wannan link din...
http://cupstv.wordpress.com/2017/09/
12/how-the-usa-senate-indicted-atiku-for-money-laundering/?fbclid=IwAR0IjUcpmgZv_TVBzStxO
L1kniNRC7RZjGaUd6nlo_2ODHAofeAqmVXSqUw
Sannan zakuga hotunan gidaje, Atiku Abubakar ne ya saya a Maryland Kasar Amurka, amma mahukuntan Amurka sun kwace gidan saboda binciken da suke masa na cin hanci da rashawa amma ya kasa zuwa ya kare kansa.
Hakika lokaci yayi da gwamnatin Nigeria zata hada kai da gwamnatin Amurka su binciki Atiku Abubakar har sai ya kare kansa daga zargin da ake masa na cin hanci da rashawa da zamba cikin aminci
Jama'a kunga dai yadda akayi aka talauta 'yan Nigeria, shiyasa dole zamusha wahala kafin mu farfado.
Allah Ka taimaki shugaba Buhari Ka bashi nasara Amin.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode
Source: www.MuryarHausa24.com.ng
Saturday 13 October 2018
TURA WANNAN ZUWA GA
Mawallafi: MURYAR HAUSA24 ONLINE MEDIA verified_user
MAKALOLI MASU ALAKA
- Blog Comments
- Facebook Comments