Wednesday 3 October 2018

Karanta Kaji: Kuskure 7 da akai a cikin Film ɗin MAI KYAU tare da Sharhin Fim ɗin

Tura Wannan Zuwa Ga
Suna: Mai Kyau
Tsara Labari: Nazir Alkanawi
Kamfani: Abnur Entertainment
Shiryawa: Abdul Smart
Umarni: Sadik N. Mafia
Jarumai: Ali Nuhu, Fati Washa, Nuhu Abdullahi, Asiya Ahmad, Bashir Na Yaya, Maryam Ctb, Teema Makamashi, Hadiza Muhammad. Da sauran su.
Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an nuna Bilkisu (Asiya Ahmad) a zaune a cikin daki tayi kwalliya sannan ta sa zobuna da agogo, daga bisani kuma ta zabi talalmi me kyau ta saka sannan ta fita. Bayan ta fito tsakar gida inda mahaifiyar ta Hajiya Hindatu (Hadiza Muhammad) wadda ganin Bilkisu yasa ta tsaya tana yabon kyawun halittar ‘yar tata, hakan yasa Bilkisu taji dadi kuma sanda zata fita sai ta nuna idan dare yayi a rufe gida alamun ba lallai ta dawo a ranar ba, hakan ne yasa mahaifiyar ta Hajiya Hindatu ta tambayi kudin makarantar kanin Bilkisu a yayin da Bilkisun ta bata wasu daga cikin kudin kafin sanda zata dawo ta cika mata sauran.

Bayan Bilkisu ta fito sai ta shiga motar saurayin da yazo wajen ta (Nuhu Abdullahi) wanda shima ganin ta ne yasa ya fara yabon kyawun surar ta, amma sai ta nuna masa babu wanda yakai mahaifiyar ta iya yabon kyawun halitattar ta, duk da haka dai bai fasa yabon ta ba, a daidai sannan ne ta nemi izinin sa akan zataje wajen wata almajira tsohuwa dake kusa da wajen don ta bata sadaka kamar yadda ta saba, nan ta fito ta bawa almajirar sadaka, yayin da almajirar Nadiya (Fati Washa) tayi mata godiya. Bayan Bilkisu sun tafi da saurayin ta sai ya ajiye ta a ‘kofar gidan wasu ‘kawayen ta ‘yan bariki, anan Bilkisu ta nuna masa cewar tana bukatar kudi har kimanin naira miliyan daya, ai kuwa bai yi gardama ba ya tura mata kudin a cikin account din ta, bayan ya tura mata ne sai ta nuna zata shiga daga ciki wajen kawayen ta amma kada ya kira ta har sai ta kira sa saboda bata son takura, haka dai shima ya amince saboda yana lallaba ta ne don kar ta rabu dashi. Lokacin da Bilkisu ta shiga gidan da kawayen nata suke babbar kawarta (Teema Makamashi) ita ta fara tarar ta cikin murna tana yabon ta gami da shigo mata da bukatun abubuwan da take so domin Bilkisu ta fisu samun alhazai masu kudi, yayin da sauran kawayen kowa yake harkokin sa a cikin dakin, wasu na bushe-bushen hayakin shisha wasu kuma na danna waya, yanayin su gaba daya an nuna cewar mata ne masu zaman kan su, a sannan ne wata kawar su ta shigo wadda ba sa shiri da Bilkisu, itace ta nuna musu cewar a zaman nan da suke ba lallai karshen su yayi kyau ba, amma nan sukayi watsi da maganar ta suka cigaba da budirin su.

Wata rana Bilkisu tana kwance bisa cinyar mahaifiyar ta sai aka aiko wani matashi akan ana sallama da ita a kofar gida, jin cewar wanda yazo wajen ta a kasa yake ba’a mota ba kuma yanayin da aka misalta mata shi ne yasa ta gane talaka ne futuk ba irin mazan da take so ba, hakan yasa taki fita don haduwa dashi har sai da ya sake aikowa yana yi mata magiya. Bayan ta fita ne sai taga wanda yake sallama da ita(Ali Nuhu) wanda anan take ba da bata lokaci ba ya fada mata cewar son ta yake yi da aure, hakan ne yayi matukar bata mamaki ta soma nuna masa aibun sa har dai suka rabu dashi magana mai dadi bata fito daga bakin ta ba. Bayan dan wani lokaci sai Bilkisu ta sake zuwa wajen almajira Nadiya (Fati Washa) ta bata sadaka, a sannan ne almajirar ta nunawa Bilkisu cewa tana son yin wata muhimmiyar magana da ita, amma sai Bilkisu ta nuna mata cewar sai ta sake samun lokaci zata zo wajen ta.

Haka Bilkisu ta cigaba da yawo a gari yau itace da wannan namijin gobe kuma ta sake fita da wani namijin daban. Wata rana Bilkisu Billi ta koma wajen almajira Nadiya akan tazo jin maganar da Nadiya din take son fada mata. A sannan ne Nadiya ta nuna wa Bilkisu cewa ta gane kusan rayuwar su iri daya ce don haka tana shawartar ta akan ta fidda duk mijin da yake son ta tayi aure tun kafin rayuwa ta juya mata baya ta koma yin bara ko kuma ta kare rayuwar ta a gidan kaso, duk da dama almajirar ta taba yiwa Bilkisu addu’a a baya kan cewar Allah ya bata miji na gari, amma a sannan sai Bilkisu ta nuna mata cewar ita ba miji bane matsalar ta domin tana da masoyan da suke son ta da aure har sama da guda ashirin.

Hakan ne yasa bayan Bilkisu ta sake jin almajira Nadiya ta sake bata shawara akan yin aure don gujewa mummunan karshe, sai Bilkisu ta fusata gami da nuna cewar almajirar ta rainata ne saboda ganin cewar tana bata sadaka, har ta yunkura zata yi tafiyar ta sai almajira Nadiya ta sake kiran ta gami da nuna mata cewar lokacin da tana da kuruciya kamar na Bilkisun itama Nadiya Me Kyau ake ce mata kamar yadda ake kiran Bilkisu da Mai Kyau, kuma ita a nata zamanin har tafi Bilkisu kyau. Jin hakan ne yasa Bilkisu ta cika da tsananin mamaki ta dawo wajen almajira Nadiya tana tambayar ta akan cewar ta yaya hakan zai kasance ace tsohuwa kamar ta amma a baya ta fita kyau?

A nan ne almajira Nadiya take nuna mata cewar shi kyau bala’i ne sanadin kyawun ta ne ya jefa ta a cikin mummunan hali kuma duk wata mace mai kyau tana can cikin bariki ba ta zaune a wajen da ake aikata alheri, Bilkisu ta bukaci karin bayani amma sai almajira Nadiya ta nuna zata bata labarin rayuwar ta amma sai dai su ta shi daga nan kan hanya su koma gidan almajira Nadiya, nan fa Bilkisu ta amince suka tafi gidan almajira Nadiya. A can ne almajira Nadiya (Fati Washa) ta soma bawa Bilkisu labarin tarihin rayuwar ta na tun daga sanda aka haifeta mahaifiyar ta (Maryam Ctb) ta dauki burin duniya ta dora mata gami da cin alwashin cewa ‘yar ta Nadiya tafi karfin auren talaka sai mai kudi ko mai mulki, yayin da shi kuma mahaifin Nadiya (Bashir Na Yaya) ya kasance mutum ne shi talaka mai gudun duniya wanda abin duniya bai dameshi ba.

A kullum burin sa shine ya aurar da ‘yar sa Nadiya ga mutum me rufin asiri, yayin da ita kuma matarsa mahaifiyar Nadiya ta nuna sam ‘yarta ba zata auri talaka ba, haka itama Nadiya ta goyi da bayan mahaifiyar ta duk suka ki amincewa sa zabin sa. Nadiya kuwa ta cigaba da bin maza kowa yazo wajen ta to sai don yana sha’awar ta ne yake zuwa wajen ta ba wai don yana son ta ba. Akwai wani saurayin ta da suka jima tare dashi (Adam M. Adam) wanda ta nuna tana so ya fito suyi aure tunda ta bijirowa zabin mahaifin ta, amma sai ya nuna sam shi bai shirya aure ba kuma iyayen sa ma ba zasuyi masa aure a wannan lokacin ba, hasali ma shi kasar waje zai tafi karo karatu mai zurfi, haka dai ya rabu da Nadiya saboda taje masa da zancen aure, ana haka ne suka hadu da wani saurayi dan makaranta Aminu (Umar Gombe) wanda shi kuma ya nuna mata cewar auren ta yake son yi kuma na kyawun ta bane yasa zai aureta haka kawai yake son ta, jin hakan yasa Nadiya ta nuna masa rashin amincewar ta saboda tana ganin cewa shi mutum ne kamili bata dace dashi ba, duk da hakan Aminu bai daina bibiyar ta ba saboda ya nuna cewar da gaske shi zai iya auren ta a kowanne irin hali bai damu da yawon da take yi na bin mazan banza ba, ana tsaka da haka ne sai Nadiya ta samu juna biyu, iyayen ta suka rutsa ta da tambayar wanda yayi mata ciki amma ta nuna cewar itama bata sani ba saboda suna da yawa, sai da suka dage sannan ta fada musu cewar Aminu ne yayi mata cikin, jin hakan yasa mahaifin Nadiya (Bashir Na Yaya) ya tafi wajen iyayen Aminu ya sanar dasu halin da ake ciki duk da a zahiri shi Aminu yasan da cewa Nadiya kazafi tayi masa domin ba shi yayi mata ciki ba. Haka iyayen Aminu suka yanke hukuncin za su aura masa Nadiya tunda shi ya bata mata rayuwar ta. Jin hakan ne yasa Aminu ya tari Nadiya a hanya ya nuna mata rashin jin dadi akan kazafin da tayi masa sannan ya nuna zai tafi ba zata sake ganin sa ba.

Bayan Nadiya ta koma gida ne ta tarar da gawar mahaifin ta wanda bakin ciki ya kashe shi, ganin mahaifiyar ta tana kuka ita ma sai ta kara tsananta kuka fiye da wanda ta shigo gidan dashi. Bayan mutuwar mahaifin Nadiya ne aka koresu daga gidan. Nadiya ta cigaba da wahala har zuwa tsufanta. Bayan almajira Nadiya ta gama bawa Bilkisu labarin rayuwar ta sai jikin Bilkisu yayi sanyi ta kama kuka sannan ta tafi taje ta shafa bakin shuni a fuskar ta saboda ta tsani kyawun fuskar da take dashi, bayan komawar ta gida ne ta nuna wa mahaifiyar ta illar da kyawun ta ya jawo mata sannan ta shiryu ta daina yawon bin maza. Yayin da daga karshe kuma ta amince ta auri (Ali Nuhu) talakan da yake sana’ar aski wanda ya nuna yana son ta.

Saidai abin mamaki bayan an daura mata aure sai suka ga an kawo kyawawan motoci masu tsada an kwashi amarya da ‘yan rakiyar ta, hakan ne ya bawa kowa mamaki musamman kawayen Bilkius ‘yan bariki wadanda suka zo don ganewa idanun su irin gidan talakan da Bilkisu ta aura. Anan ne suka fahimci cewa ashe attajirin me kudi ta aura.

Abubuwan Birgewa:

1- Anyi kokari wajen nuna illar karuwanci wanda wasu matan suke jefa kan su ciki saboda wani dalili na kyawun surar da Allah ya basu ko kuma son abin duniya dake rudar su.

2- Jaruman sun yi kokari, musamman Bilkisu (Asiya Ahmad) wadda ta kasace sabuwar jaruma.

3- Fim din ya nuna cewa duk abinda yake rabon ka zaka same shi in kayi hakuri ko da kuwa ba ka bi ta mummunar hanya ba, kamar yadda a karshe Bilkisu ta auri attajiri.

4- Kalaman jaruman wato (Dialogue) sun yi dadi gami da ma’ana.

Kurakurai:

1- Lokacin da Ali Nuhu yake yiwa wani matashi aski, me kallo yaga Ali Nuhu ya juya yana kallon wani bangare cikin mamaki, wanda dalilin hakan yasa matashin da ake yiwa aski ya kama fada yana nuna bai dace Ali Nuhu ya dinga kallon macen da ta wuce ba. Shin ya akayi shi matashin da ake yiwa askin ya gane cewar mace Ali Nuhu yake kallo? Ya dace a nuna cewar matashin ya juya ya kalli wajen kafin yayi furucin bakin sa. Haka kuma shima me kallo bai ga abinda shi mai askin yake kallo ba wanda ya bashi mamaki, ya dace a nunawa me kallo ma abinda me askin yake kallo don tabbatar da maganar su.

2- An nuna wa me kallo cewa Bilkisu babbar yarinya ce wadda samari ke zubawa kudi har kusan miliyan daya a cikin account din ta, amma sai gashi har film din ya kare da jakar hannu kala daya ake ganin ta da ita, ya dace ace duk kayan da za’a ga ta saka to a nuna ta dauki jakar ratayawar da ta dace da kalar kayan jikin ta, amma ba wai a yi ta ganin ta da jaka kala daya ba.

3- Lokacin da Bilkisu tayi aure aka kaita gidan mijin ta, yanayin fuskar gidan da aka nuna yafi kama da wani babban hotel din ba gida ba.

4- Bayan an kori Nadiya da mahaifiyar ta daga gidan da suke haya a sanda me gidan ya mutu, shin ina mahaifiyar Nadiya take kuma meye makomar ta a labarin? Tunda an nuna wa me kallo cewa mahaifiyar Nadiya macece mai son abin duniya gami da wulakanta mijin ta, to ya dace a nuna wa me kallo makomar ta ko kuma a fadi yadda karshen ta ya kasance ko da baki ne.

5- An nuna cewa Nadiya tayi cikin shege, amma ba a nuna makomar juna biyun da ta samu din ba. Shin ta haihu ne ko kuma zubar da juna biyun aka yi? Ya dace a fadi yadda karshen juna biyun nata ya kasance.

6- An samu discontinuity a lokacin da Bilkisu taje wajen almajira Nadiya ta ba ta labarin rayuwar ta, jakar hannun Bilkisu ruwan goro ce mai turuwa, amma lokacin da ta dawo gida da bakin shuni a fuskar ta sai aka ganta rike da jaka ruwan goro me haske.

7- An nuna wanda zai auri Bilkisu a matsayin talaka futuk me sana’ar yiwa mutane aski, amma bayan auren sa da Bilkisu sai mai kallo ya gan shi a katafaren gida cikin daula wanda har wadanda suka kai amarya dakin ta suma suke mamakin faruwar hakan. Shin dama mutumin da ya aure ta din attajirin me kudi ne ba talaka ba? Idan kuma dama mai kudi ne wanda ya boye gaskiyar matsayin sa, to ya dace a yi bayanin yadda hakan ta kasance don a fahimtar da me kallo kuma a fidda shi daga cikin wasu-wasi.

Karkarewa:

Fim din ya fadakar kuma labarin ya tafi kai tsaye bai karye ba, sai dai kuma bai dace a nuna wa me kallo cewa duk wata mace kyakykyawa tana cikin bala’i ba, domin a kowace irin al’umma akan samu mutum na gari ba batacce kadai ba, ba zai taba yiwu wa ace duk wasu mata masu kyau a duniya halayyar su ta zamo iri daya da kyawawan matan da akayi bayani a cikin fim din nan ba. Wallahu a’alamu!

Karanta Kaji: Kuskure 5 da akai a cikin Film ɗin MATAR MAMMAN tare da Sharhin Fim ɗin

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: Leadership A Yau

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user