Friday 19 October 2018

KARANTA KAJI: ME BUHARI YA AIWATAR A JIHAR KANO CIKIN SHEKARU UKU ?

Tura Wannan Zuwa Ga
Shakka babu, wannan tambaya tana nan tuli guda cikin zukatan wasu daga cikin al'umma, su na kuma yinta lokaci bayan lokaci sannan kuma su na da bukatar samun amsa da gamsassun bayanai.Marubuci: Bashir Abdullahi El-bash


Kuma Ba komai ba ne ke haifar da wannan tambaya face kasancewar Kano sha kundum kan 'kauna da soyayyar Shugaba Muhammadu Buhari tun daga farkon shigarsa Siyasa a (2002) har zuwa yau.

Ba shakka, shi ma Shugaba Muhamadu Buhari ya na nuna 'kauna da kulawa ga Kano da Kanawa duba da yadda ya 'debi tulin al'ummar Kano ya jajjefa cikin mukamai daban-daban domin hatta mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu dan Kano ne, kuma wannan ya isa girman misalin da zai gaskata tasirin Kanawa cikin gwamnatin Buhari. Wannan kenan.

Mu dawo kan tambayar da al'umma suke yawan yi domin neman sanin irin ayyukan raya Jiha da shugaba Muhammadu Buhari ya assalawa Kano cikin wadannan shekaru uku.

Cikin ikon Allah a jiya Laraba, 17/10/2018, cibiyar sadarwar zamani ta Shugaba Muhammadu Buhari "The Buhari New Media Center" (BNMC), reshen Jihar Kano, 'karkashin jagorancin shugabanta,
Bashir Abdullahi El-bash , mun samu nasarar gudanar da rangadin duba ayyukan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a Jihar Kano, bisa ga dafawa gami da sahalewar hadimin shugaban 'kasa Buhari kan sabbin kafafen sadarwa na zamani (New Media), kuma shugaban cibiyar na 'kasa gaba 'daya Mallam Bashir Ahmad.

Daga cikin ayyukan da muka samu damar ziyarta, akwai:

1. Wani gagarumin aiki na gadar sama, aikin da tun zamanin tsohon shugaban 'kasa marigayi Janar Sani Abacha aka fara amma babu wani shugaban 'kasa da ya cigaba da aikin har sai da Shugaba Muhammadu Buhari ya zo ya dora daga inda aka tsaya, kuma tuni aiki ya kammala an fara zirga-zirga a saman gadar, 'kasan ma kuma ana cigaba da aikin domin samun nasarar kammalawa gaba 'daya. Za mu fahimci muhimmancin wannan aiki, idan muka yi duba da yadda Kano take da cinkoson ababen hawa sakamakon dumbin albarkar dan adam da Allah ya yi mana. Sannan aikin zai 'kara taimakawa wajen 'kara 'kawata gari.

1. Da kuma aikin gina wata makekiyar kurkuku irin ta zamani, wacce duk Afirika babu irin ta. Domin akwai gine-gine na zamani irin tsarin gine-ginen kurkuku a turai kamar gun shan magani (Asibiti), da wurin Koya Sana'a da wurin da ake ajiye mutum kafin a yanke masa hukunci (zaman wakafi), da kuma wurin da ake ajiye masu laifi tare kuma da Masallaci gami da Coci hadi da katafaren ginin gidajen ma'aikatan gidan. A kan wannan gaba ma akwai bukatar mu dan yi sharshi kan wannan aiki domin jama'ar da suke amfani da shi wajen aibata ko nuna kushe ga 'kokarin Shugaba Muhammadu Buhari na samar da wannan aiki, ko shakka babu, idan muka yi duba da irin cinkoso da matsi gami da takurar da ake samu a gidajen kurkuku ta yadda har wasu suke mutuwa da jikkata, lallai Kano tana bukatar wannan gini, kuma dole mu godewa Shugaba Muhammadu Buhari. 

Sannan wani abun sambarka shi ne yanayin tsarin da aka yi wa kurkukun na samar da guraben gyaran halin daurarru da koya masu sana'u gami da ba su damar koyon karatu da gudanar da ibada cikin nutsuwa.

3. Haka zalika, Shugaba Muhammadu Buhari ya samar da cibiyar ba da wutar lantarki a garin Wudil, wadda za ta ba wa garuruwan: Wudil, Garko, Albasu, Ajingi, Takai da Sumaila wutar lantarki. Kuma tuntuni aiki ya kammala nan gaba kadan za a bude shi domin al'umma su sami wuta. Tabbas, shi ma wannan aiki abin a yaba ne duba da muhimmancin wutar lantarki kan fannin cigaba da bunkasar tattalin arziki.

4. Har wa yau, akwai gidaje da Shugaba Muhammadu Buhari yake samarwa a kwanar Jaba dake karamar hukumar Fagge, duk domin samar da muhalli ga Kanawa. Muhimmancin muhalli ma ga rayuwar dan adam kowa ya sani, babu bukatar sai na zurfafa sharshi da tsokaci akai.

5. Bugu da 'kari, Shugaba Muhammadu Buhari na cigaba da gyaran titunan: Kano zuwa Katsina da kuma Kano zuwa Kaduna zuwa Abuja hadi da Kano zuwa Maiduguri. Sanin kowa ne wadannan hanyoyi sun yi mummunar lalacewar da suke haddasa hadura da janyo hasarar rayuka da na dukiya, amma cikin ikon Allah, ga shi yau Shugaba Muhammadu Buhari ya na gyarawa, gyaran da gwamnatocin baya suka gaza.

6. Sai kuma wani makeken Dam na ruwa da Shugaba Muhammadu Buhari ya samar a karamar hakumar 'Kunchi ta Jihar Kano. Shakka babu, ruwa shi ne abokin aiki domin shi za a sha a rayu har ma a samu damar gudanar da aikin noma da shi domin samar da abinci da bunkasar tattalin arziki a 'kasa.

Wannan fa kadan kenan daga cikin dumbin ayyukan alkhairan da Kano ta amfana a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, amma saboda adawa irin ta Siyasa, sai ka ji wasu su na tambayar wai "me Shugaba Muhammadu Buhari ya assalawa Kanawa cikin shekaru uku". Alhalin kuwa, suna sane da duk irin wadannan ayyukan alkhairan.

Insha Allahu, cibiyar sadarwar zamani ta Shugaba Muhammadu Buhari (BNMC) a Jihar Kano, ba za mu yi 'kasa a gwiwa ba, sannu a hankali za mu cigaba da yin wannan rangadi domin wayar da kawunan al'ummar Jihar Kano wadanda ba su fahimci alkhairan da Shugaba Muhammadu Buhari ya samar a Jihar Kano ba su sani.

Bashir Abdullahi Elbash
(BNMC) Coordinator Kano State Chapter.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user