Friday 26 October 2018

KARANTA KAJI: MU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA DARASI NA UKU

Tura Wannan Zuwa
Domin taimaka wa dalibai masu nazarin harshen hausa, da kuma masu so rubutunsu ya yi ma'ana da saukin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.



DARASI NA UKU

Amfani da Babban Baƙi

Kamar yadda muka gani yayin ƙididdige baƙaƙe da wasula na Hausa, cewa akwai manyan baƙaƙe da ƙanana. To ƙananan baƙaƙe aka fi yin amfani da su cikin rubutu na yau da kullum. Akan yi rubutu da manyan baƙaƙe zalla ne a wurare na musamman, kamar rubuta kanun labari ko cike wata takarda (fom), dm.

Ba a son hautsuna manyan baƙaƙe da ƙanana cikin rubutu. Duk da haka ana amfani da manyan baƙaƙe ne a wasu keɓaɓɓun wurare. Ga kaɗan daga cikinsu:

Farkon rubutu:

Wato duk abin da za a rubuta, da babban baƙi za a fara rubuta kalmar farko. Misali:
Ƙungiyar Gizago ta ƙasa ke ɗaukar nauyin gabatar muku da wannan shiri a dandalinta na fesbuk.

Farkon jumla:

Wato bayan ƙare cikakken zance da sanya aya, kalmar farko ta jumla ta gaba za ta fara ne da babban baƙi.

Misali:

Mun ga ƙaramar salla lafiya. Allah ya nuna mana babbar salla.

Farkon sakin layi:

Wato bayan gama wani sakin layi, to in za a shiga wani sabo sai a fara shi da babban baƙi. Misali, bayanin da muka yi na baƙin Alhamza, mun yi shi ne cikin sakin layi biyu, inda kowannensu ya fara da babban baƙi.

Farkon sunan yanka:

Sunan yanka ya ƙunshi sunayen mutane da wurare da garuruwa da birane da ƙasashen duniya, da duk wani kafaffen suna. To akan fara rubuta shi da babban baƙi.

Misali:

Muhammadu, Hadijatu, Alhaji Ƙasimu, Dandalin Murtala, Titin Ahmadu Bello, Jami’ar Sakkwato, Bunguɗu, Zariya, Masar, Faransa, da sauransu.

Bayan alamar tambaya da ta motsin rai:
Wato duk sa’ad da aka yi wata tambaya a rubuce, aka sanya alamar tambaya, ko aka faɗi wata kalma ko jumla ta al’ajabi ko tsananin farin ciki ko damuwa, aka sanya alamar motsin rai a ƙarshenta, to kalmar da za ta biyo bayanta za ta fara ne da babban baƙi.

Misali:

Wa ke nema na? To ga ni na zo.

Wayyo! Abin gwanin ban tausayi.

Alhamdu lillahi! Bana an biya min kujerar Makka!

Za mu ci gaba  a sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah, Idan akwai mai tambaya a kan wannan darasi na yau sai a tura  tambaya zuwa
muryarhausa24@gmail.com mungode .

Wannan wani sabon darasi ne da
Waziri Aku tare da haɗin gwiwar Shafin Muryar Hausa24 su ka ɗauki nauyin kawowa 'yan uwa ɗalibai masu yin nazarin harshen Hausa da kuma masu son koyon ƙa'idojin rubutun harshen Hausa domin rubutunsu ya yi ma'ana da sauƙin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.

A lura da haƙƙin mallaka wajen kwafin ɗin rubutu, darasin zai rika zuwa muku duk ranar Juma'a, daidai wannan lokaci, tare da taimakon Malam Nasir G. Ahmad .

KARANTA KAJI: MU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA DARASI NA BIYU

Za mu ci gaba  a sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah, Idan akwai mai tambaya a kan wannan darasi na yau sai a tura  tambaya zuwa
muryarhausa24@gmail.com mungode .


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user