Saturday 24 November 2018

KARANTA KAJI: YADDA AKA FANSO 'YAN TAGWAYEN DA AKAYI GARKUWA DA SU A ZAMAFARA DA DARASIN DA ZAMU KOYA

Tura Wannan Zuwa
Lokacin da Maigirma Sanata Kabiru Marafa ya bada tallafinshi Naira miliyon shida da sauran kudin da jama'ar Nigeria suka tallafa aka hada kudin ya kai Naira miliyon goma sha biyar, sai aka kira wadanda sukayi garkuwa da tagwayen aka sanar musu cewa kudin ya cika kamar yadda sukace a biyasu kafin su saki tagwayen, bayan an sanar da su cewa kudin ya cika sai sukace to a jirasu zasu kira don a kai musu kudin.



Bayan kamar awa uku sai suka kira wayan Ibrahim mijin yayarsu wanda ake sasantawa da shi, sukace a dauko kudin azo wani gari da ake kira Gurbin-Burai inda kwanaki masu garkuwa da mutane sukayi kashe-kashe da kone-kone sukace idan an isa garin a kirasu, kafin su Ibrahim su isa garin masu garkuwa da tagwayen suna ta kiransu a waya cewa mai yasa har yanzu ba su iso ba? sun gaji da jira, su fa zasu kashe tagwayen suyi tafiyarsu sai dai azo a dauki gawarsu, Ibrahim dai yayi ta basu hakuri yana cewa mun kusan isowa.

Bayan su Ibrahim sun isa garin na Gurbin-Burai suka kira masu garkuwan aka fada musu cewa sun iso garin, sai sukace to daga nan su biyo ta wani kauye da ake kira Dumburum daga Dumburum daji za'a shiga, to su Ibrahim sai suka ajiye motarsu suka nemi mashina guda uku, sai masu garkuwan suka kira waya sukace ai mun ganku ko taho garin na Dumburum zamu fada muku hanyar da zakubi ta kawoku cikin jeji inda muke, jama'a kunga wannan ya nuna cewa akwai masu yiwa 'yan bindigar leken asiri ko ta ina a cikin wadannan garuruwa na Zamfara.

Daga garin Dumburum su Ibrahim sunyi tafiya kamar tsawon kilo mita 15 a cikin jeji, suna cikin tafiya kawai sai suka fara ganin mutane da bindigogi suna ta bullowa wanda yawansu ya kai kusan mutum dari da hamsin, kuma kowa rike yake da bindiga kirar AK47 ana cewa su dakata a gurin, sai su Ibrahim suka dakata suka sauka daga kan mashina, da ma su uku ne, da shi Ibrahim mijin yayarsu, da wanda zai auri Hussaina, da babban yayansu, sai Ibrahim ya dauko kudin ya ajiye a gabansa wanda aka zuba kudin a cikin jaka guda biyu, 'yan bindigar sun gewayesu a tsakiyar jeji, bayan kamar mintuna biyu sai ga shugaban kuma ogan 'yan bindigar ya bullo tare da tawagarsa rike da manyan bindigogi tagwayen suna bayanshi.

Haka shugaban barayin ya matso har kusa da Ibrahim inda kudin suke ajiye a cikin jaka a 'kasa, bai ce masa komai ba sai yayi umarni da wasu yaranshi guda biyu su bude jakan su kirga kudin, bayan sun kammala kirga kudin gaba daya ya cika miliyon 15, sai ogan yace a mayar da kudin cikin jaka a daure, da akayi haka, sai ogan barayin ya tsuguna a gaban kudin ya debi kasa da hannunshi ya watsa akan jakakkunan kudin, sai ya mike tsaye ya hau kan jakakkunan kudin da kafafunshi, sai ya daga kanshi sama yana karanta wasu 'dalasimai irin na tsafi, yana tayi har kusan kamar mintuna 2 sai ya saukar da kanshi kasa, ya kuma sauka daga jakar kudin ya ja da baya, sai yayi umarni ga yaranshi da su dauki kudin, sai suka dauka, sai ya kalli Ibrahim yayi dariya sai yace sannunku da zuwa ashe kuna son kannenku.

Sai Ibrahim ya amsa masa, sai yace ai ba wanda baya son kannenshi oga, daga nan sai yayi umarni da a kawo tagwayen ya mikasu ga Ibrahim yace su juya su tafi kar su kuskura su juya baya, Ibrahim yace mun gode oga, shine suka dauko tagwayen suka iso har kauyen Gurbin-Burai inda motarsu take, daga nan sai Ibrahim ya fara kiran waya suna sanar da 'yan uwa da wadanda suka tallafa cewa tagwayen sun kubuta lafiya.

Jama'a wannan shine bayanin abinda ya faru game da yadda akaje aka karbo tagwayen.

Abinda bincikenmu ya tabbatar mana shi ne an jima ana bibiyar tagwayen domin ayi garkuwa da su, mutane da dama suna da hannu a cikin garkuwa da 'yan matan, wato nazarin da mukayi a kai shine wadannan masu aikata laifin garkuwa da mutane sun kawo wata sabuwar hanyar yin garkuwa da mutane ta hanyar bibiyar mutanen da suke mu'amala da dandalin sada zumunta na zamani musamman wadanda suke watsa hotunansu a social media, masu garkuwan suna la'akari da farin jinin wanda yake social media da yawan jama'ar da suke tare da shi wanda idan sunyi garkuwa da shi dole za'a biyasu kudi.

Kunga wadannan tagwaye babban abinda yayi sanadiyyar jefa su cikin wannan bala'i shine saka hotunansu da suke yi a social media da irin yadda ake kambamasu, wadanda sukayi garkuwa da su sun dauki lokaci mai tsawo suna bin diddiginsu har zuwa ranar da tagwayen suka ziyarci garin Mahaifinsu domin su raba katin aurensu, garin kauye ne, a daren ranar da za'ayi garkuwa da su tun isarsu garin suke ta yawo, kuma duk inda suka wuce sai an nunasu, da dare yayi misalin karfe 11 da wasu mintuna akaje gidan kawarsu da suka sauka zasu kwana aka sacesu gaba daya, har da kanin mijin kawar tasu, da ita kawar tasu aka tafi dasu jeji.

Muna nazarin ayyukan masu garkuwa da mutane da dabarunsu, mun sani cewa idan masu garkuwa da mutane sun kama mutum biyu ko sama da haka, to ba sa yarda su sake daya ko biyu su bar wani, a'a sai dai su sakesu gaba daya, to amma wannan sun kamasu gaba daya, sai suka saki tagwayen sauran kuma ba'a sakesu ba, wannan zai tabbatar maka da cewa masu garkuwan sunyi karfin da ya wuce tunanin duk wani mai tunani ko hasashe da nazari, kuma wannan babban kalubale ne ga gwamnatin Nigeria, mahukunta sai sunyi da gaske imba haka ba masifar zata mamaye jihohi da dama a Nigeria.

Daga karshe ina kira ga 'yan mata da mazaje masu yada hotunansu a kafofin sada zumunta kuma suke da dunbin masoya da suyi taka tsantsan, sannan su kiyaye sirrin tsaron kawunansu, ku dena bayyana inda zakuje idan zakuyi tafiya, bayyanawan hatsari ne mai girma a irin wannan lokaci da muka tsinci kanmu, a dinga 6atar da kafa idan za'ayi tafiya ko za'a dawo daga tafiya.

Muna rokon Allah Ya tsaremu daga dukkan sharri da makirci da mugun tarko.

Yaa Allah duk masu bibiyarmu da sharri ko cutarwa Allah Ka mayar da sharrin da cutarwan zuwa kansu Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source:  Datti Assalafy



TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user