Sunday 24 March 2019

KARANTA KAJI: MANYAN DALILAN DA SUKA JAWO HARGITSI A JIHAR KANO

Tura Wannan Zuwa
Za6en jihar Kano, za6e ne da dukkanin al'ummar kasar nan suka saka ido suga yadda zai wakana, saboda sarkakiyar dake cikinsa, inda kowa ya zuba ido yaga yadda zata wakana.



Marubuci: Abba Ahmad Gwammaja

Sai dai kuma bayan da aka gudanar da zagayen farko a ranar 9 ga watan Maris din da muke ciki, wanda za6en bai kammala ba a wancan lokaci, inda aka saka yau Asabar 23 ga watan na Maris domin dawowa a karasashi.

Yayin gudanar da wannan za6e na yau ne aka gamu da kalubale, inda aka samu hargitsi a wasu wuraren da za6en ya gudana, wasu daga cikin dalilin da suka jawo sun hada da:

1. Umarnin Kwankwaso a karon farko.
Ana daf da gudanar da za6en ranar 9 ga wata ne Injiniya Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso ya gabatar da hira a kafafen yada labaran dake jihar Kano, inda yake yin bayani dalla-dalla a bisa shirye-shiryensu na za6en gwamna, wanda anan ne ya umarci matasan dake biyayya ga tafiyarsa ta Kwankwasiyya akan kowannensu ya kasance a bakin akwatin za6e ranar za6en na gwamna, inda ya kira lamarin da "Kowa agent". Sa6anin hukuncin da hukumar za6e ta kasa mai zaman kanta tayi na cewar kowacce akwati tana da wakilin jam'iyya guda daya kacal.
Matasan kuwa sun amsa umarninsa, musamman ma a tsakiyar birnin Kano, wanda hakan na daya daga cikin dalilan da suka bawa PDP din nasara a cikin birni, dan kuwa ganin idona ranar za6en na gwamna naga akwati da dama da wakilan jam'iyar PDP fiye da guda 5 suka zagayeta, kuma kowanne da alama a wuyansa (Tag).

2. Hargitsin jami'an gwamnati.
Bayan da aka kusan kammala tattara sakamakon za6en karamar hukumar Nassarawa ne za6e zagayen farko, wasu daga cikin jami'an gwamnatin jihar Kano, wadanda suka hada da Mataimakin gwamna jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna da kuma Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano Murtala Sulen Garo suka halarci cibiyar tattara sakamakon za6e ta karamar hukumar Nassarawa, har suka tayar da hargitsin da yakai ga yaga sakamakon za6en yankin, inda anan ne sakamakon za6en maza6ar Gama ya salwanta, wanda hakan ne ya jawo hukumar za6en da ayyana za6en a matsayin wanda bai kammala ba, dan kuwa maza6ar ta Gama ita kadai tana da adadin masu rijistar za6e da suka haura dubu 40.

3. Umarnin Kwankwaso a karo na biyu.
Bayan da aka bayyana za6en a matsayin wanda bai kammala ba, Injiya Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso ya sake hira da kafafen yada labarai a karo na biyu, inda ya bayyana fushinsa bisa ga abinda wadancan jami'an gwamnati sukayi na tada hargitsi a wajen tattara sakamakon za6e, inda anan ne naji yana bayyana cewar: " A za6en gaba, dukkanin matasan nan su fito a matsayin kowa agent, kowa security (jami'in tsaro), kuma kowa Camera man (mai daukar hoto), duk wanda ya ta6a akwatin za6e to wadancan matasa suyi masa hukuncin da Buhari ya bayar akan akwatin za6e".
Jin kunnena naji dan jaridar yana tambayarsa da cewa: "Ranka ya dade suyi kisa kenan? Su da ba jami'an tsaro ba mai ya hadasu da akwatin za6e kuma?".
Kwankwason ya mayar da martanin cewa: "Nidai kawai ce maka nayi suyi masa hukuncin da Baba Buhari yace ayiwa 6arawon akwatin za6e".
Inda su kuma matasan suka dauki aniyar cika umarnin nasa a karo na biyu.

4. Sakacin hukumar za6e.
Tabbas hukumara za6e tayi sakaci akan lamarin da ya jawo wannan hargitsi, dan kuma nasan wancan labari yaje mata, kuma ta samu labarin yadda wakilan Kwankwasiyya suka mamaye akwatin za6e a karon farko, kamata yayi ta fito fili ta bayyana abinda doka tace akan mutane nawa aka umarci kowacce jam'iyya ta bayar a matsayin wakikinta.

5.Kowa Kwamanda.
Bayan da Kwankwason ya bayyana wancan tsari nasa a karo na biyu, kuma jam'iyar APC tayi zargin cewa wancan tsari da PDP tayi a karon farko shine ya kayar da ita, kuma gashi yanzu ya kara bayyana wani sabon tsarin a karo na 2, shine ita ma ta bayyana cewa: "Ranar za6en gaba kowa Kwamanda ne".
Inda anan ne ta debo nata zugar kwamandojin suka tarwatsa wadancan agent, security da kuma camera man na PDP, domin kar su kara basu ruwa kamar yadda suka basu a farko.

6.Sakacin jami'an tsaro.
A zahirin gaskiya jami'an tsaro sunyi sakaci wajen barin wannan fafatawa tayi nisa, dan kuwa da ace sun dauki matakin gaggawa, tare da hukunta dukkanin wanda ya fara tayar da hargitsi a wurin da matsalar bata kai ga haka ba.

7. Tsira da mutunci.
'Yan Kwankwasiyya na kallon Ganduje a matsayin mayen mulki, yayin da 'yan Gandujiyya kuma ke kallon Kwankwaso a matsayin jagoran karfa-karfa.
Sam ba haka abin yake ba, dan kuwa kowannensu yana son tsira da mutuncinsa ne, domin wallahi idan dan uwansa ya dafe kujerar gwamna ba zai ji da dadi ba ta wajen bincike, wanda idan ba'a yi wasa ba har takai su ga hukumar EFCC ko kuma kotu.

Wadannan fa a takaice sune dalilan da suka jawo wannan fafatawa har aka kai ga yanayin da ake ciki a yanzu.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user