Saturday 23 March 2019

TAKAITACCEN TARIHIN YAKIN BIAFRA: ZA KU JI ABUBUWAN DA BAKU TABA JI BA A YAKIN BIAFRA

Tura Wannan Zuwa Ga
Wani  kundin asiri na difilomasiyya mai shafuka dubu 21 da Amurka ta fitar, ya zo da wasu  basasan Nijeriya daga 1967 zuwa 1970 wadanda kuma ba taba jinsu ba a baya.

ZA KU JI ABUBUWAN DA BAKU TABA JI BA A YAKIN BIAFRA.


Marubuci: Lawal Ali Reseacher

A safiyar ranar litinin din 1 ga Yulin 1967 matashin Shugaban kasar Nijeriya na lokacin, Janar Yakubu Gowon ya kasance cikin halin dimuwa a ofishinsa dake babban hedikwatar sojojin Nijeriya, wato barikin Dodan, a Legas. Dalilin dimuwar tasa kuwa shi ne matsin lambar da yake fama da shi, kan cewa lallai-ilalla ya bayar da izinin kai mamaya kan sabuwar Jamhuriyar Biafra da ta balle daga Nijeriya.A daidai wannan lokacin kuma manyan Jami’an sojan da aka tura kasashen wajen don samun horo, duk an maido da su gida. Jiragen kasa daga Kaduna da Kano kuma dauke da lodin sojoji da kayan aikinsu sun nausa tsallaken kogin Binuwai daga ta Kudu a karkashin jagorancin Kanar Muhammad Shuwa (yanzu marigayi) inda suka yi sansani a Makurdi.

Kafin nan motsawar rundunar Kanar Shuwa, an rigaya an jibge bataliya ta biyu a garin Adikpo. Bataliya ta hudu kuma a karkashin Manjo Sule Apollo, ta sauka a garin Oturko cikin shirin kafsa yaki.A dai wannan ranar, Manjo B.M. Usman, daya daga na hannun daman Janar Gowon, ya shaidawa Jami’in kula da lamurran soja a ofishin jakadancin Amurka dake Nijeriya cewa: “Na ma rasa abin da (Janar Gowon din) ke jira; domin mazaje dai sun riga sun shirya, kuma sun kagara da yaki.

Kalaminsa na umarni kadai suke jira.”Kazalika su ma mambobin majalisar koli ta mulkin soja, wadanda kan yi ganawa a kullum sau biyu, su maganar Gowon kawai suke jira. A takaice dai, duk kasar ta dauki haramin yaki. Ita ma ballalliyar Jamhuriyar Biafra, ta kimtsa tsaf, tana zaman ko-ta-kwana.Ranar 27 ga Yuni 1967, Mista Cyprian Ekwensi, mashahurin marubucin adabin nan, wanda a lokacin shi ne babban Daraktan watsa labarai na ’yan-awaren Biafra, ya shiga gidan rediyon Muryar Biafra din, wanda kafin ballewarsa, sunan sa rediyo Enugu, ya kirayi al’ummar Biafra da cewa su zauna cikin shirin kawo musu mamaya daga sojoji ran 29 ga watan, “Domin Arewa sun saba da kai hari yaki ne ran 29 ga wata.” Wannan maganar tasa kuma shagube ce ga Manjo T.Y. Danjuma, loakcin da ya shugabanci sojojin da suka kawar da magabacin Janar Gowon, wato Manjo Janar Aguyi-Ironsi, inda aka kashe shi a wani dajin bayan garin birnin Ibadan.A lokacin, Janar Gowon dai shekarunsa na haihuwa 31 ne, amma shi ke da ragamar tafiyar da harkokin al’ummar da ta kai mutum miliyan 57 har na tsawon watanni 10 cur, don haka, lamarin ke da nauyi a gare shi. Shi kuma Cif Obafemi Awolowo na da shekaru 58, a sannan kuma, shi ne amintaccen waziri kuma masahwarcin Gowon din a kan sha’anin harkokin waje; Mista Okoi Arikpo da Mista Philip Asiodu kuma, ko wannensu, yana aiki a ma’aikatan harkokin kasuwanci; da kuma na masana’antu. Dukkan su a matsayin ministocin ko wace ma’aikata.

Su ukun kuma, sun zarga zargen zargo wuyayen manyan kamfanonin mai na Dutch Oil da na Shell-BP, kasantuwar sun yi niyyar daina baiwa gwamnatin tarayyar Nijeriya harajojinsu, da nufin mikawa ga sabuwar gwamnatin ballalliyar Biafra; wadanda kuma sun kai fam dubu 250, daga ran 1 ga watan Yuni 1967 din.Dalili kuwa shi ne Laftanar Kanar Odumegwu Ojukwu, Shugaban ballalliyar Biafra ya umarci kamfanonin biyu da su koma da biyan harajojinsu ga gwamnatin da ke da mazaunin ta a birnin Enugu; in kuma sun ce ba haka ba, to fa za su fuskanci tarar da shallake hankali.A takaice dai, kuma kai tsaye, abin da hakan ke nufi shi ne Ojukwu ya bukaci kamfanin mai Shell-BP da ya biya gwamnatin shi harajin fam miliyan biyu ne; wannan kuma na nufin hana duk wani jirgin ruwan kasuwanci da na daukan mai tsayawa a tasoshin jiragen ruwan Koko, Warri, Sapele, Escrabos Bonny, Fatakwal, da kuma Kalaba; wadanda Ojukwun ya ayyana da cewa halastattun yankunan ballalliyar kasar Biafra ne, mulkan-kamilan. Yayin da ita kuma gwamnatin Nijeriya ta sarkafa ma kamfanoni takunkumin daina duk wata huldar tattalin arziki da ballaliyar gwamnatin Biafra.Gwari-gwari, Biafra na iko da doron kasa, inda rijiyoyin mai da na’urorin hako shi suke; gwamnatin Nijeriya kuma na iko da gabobin teku da kuma ruwayen teku din, inda jiragen ruwa ke karakainar kaiwa da komowa.

Don haka sai kamfanin Shell-BP ya samu kan sa a wani hali na gaba damisa, baya sayaki
Kan wannan asakalar, Jakadan Birtaniya a Nijeriya na lokacin, Sir Dabid Hunt, yayin wata ganawa da takwaransa na Amuka a Nijeriya, ya shaida masa cewa “Awolowa fa ya yi wa ma’aikatar kudin Nijeriya riko gam-gam; sannan kuma ya yi tsayin gwamin jaki kan tarawa Mista Stanley Gray, da ma wasu kwararru da suka zo daga Landan gajiya, har na tsawon kawana uku cur.” Wato sun yi iyakar-iyawarsu da Awo da ya amince da yarjejeniyar da ta fifita gwamnatin Nijeriya, sannan kuma kada ya sa kamfanin a wani yanayin da zai samu kansa, da ma’aikatan sa, gami da makudan jarin da ya zuba na fam miliyan 150, a cikin barazana daga dakarun Biafra. Amma dai Awolowo ya yi kememe da kemadagas din kin yarda da hakan. Yana mai kafa hujja da cewa duk wani abin da ba da gwamnatin Nijeriya za a yi shi ba, to la shakka, amincewa da ballalliyar Jamhuriyar Biafra ne; sannan kuma garabasa ce ga ’yan tawaye.Dangane da tabbatar da tsaron jarin da kamfanin ya zuba, da kuma kare lafiyar ma’aikatan kamfanin, sai gogan ya kafa hujja da cewa, matukar kamfanin zai zuba kudaden harajinsa a aljihun gwamnatin Nijeriya, to gwamnatin za ta samu kudaden da ko nawa ne, za ta iya kashewa, wajen yakar ’yan tawaye, kuma kadarorin Shell-BP za su tsira tsaf ba tare da wani kwarzane ba.Ko da yake, kafin nan, akwai tsohon taswirar Nijeriya a manne a jikin kyauren ofishin Janar Gowon. Don haka lokacin da Janar din ya bukaci Awolowo da ya shiga cikin gwamntinsa a yi da shi, sai da Awolowon ya kafa ma Janar din sharadin cewa dole ne Gowon ya tabbatar ya magance abin da ya kira da “kane-kanen da Arewa ta yi wa sauran sassan kasar.” Wata daya da yin wannan maganar, sai Gowon ya kekketa arewa zuwa jihohi shida; amma dai duk da haka, yankin arewan ne ke da fadi sosai.Da Gowon ya dora yatsar sa a kan taswirar, yana bitar ta sannu a hankali, da ya zo daidai inda nan ne kan iyakan ballalliyar Biafra, sai ya dakata, ya ce: “Wai ma, ta yaya za a yi, in bayar da izinin yakar jama’ata ne?” A wannan lokacin dai, ba Gowon ne Jami’in sojan da ya fi ko wanne mukami ba, sannan kuma shi ba Bahaushe Musulmi, walau daga Kano, Kaduna ko Sakkwato ba ne. Sannan kuma ya fito ne daga daya daga cikin kananan kabilun Arewacin Nijeriya, amma duk da haka, abubuwan da suka faru ne sanadiyyar cilluwar sama, inda ya zama babban kwamandan askarawan kasa baki daya, wanda hakan, a lokacin, a cewar kundin bayan, bai yi wa wasu Jami’an soja, ’yan siyasa, da Sarakunan arewa da dama, dadi ba.Sannan kuma, a lokacin, Gowon din na sane da yadda aka kyamaci al’ummar Ibo a Arewa.

Sannan kuma budurwarsa Inyamura, Edith Ike, ta fada masa yadda aka yi barazana ga rayuwarta fiye da sau shurin masaki a birnin Legas; bayan barowar ta arewa, a cikin watan Maris.Kamar yadda aka samu bayani daga bayanan asirin da Amurka ta tattara ran 1 ga Yuli 1967, a cewar wannan kundi, Edith dai a Arewa aka haife ta, kasantuwar mahaifanta sun zauna a Arewa din, har na tsawon shekaru 30, amma suka gudu suka koma Kudu maso Gabas a watan Oktoban 1966, lokacin da aka yi wa Inyamurai da dama, abin da wasu ke bayyanawa da kisan kiyashi a can. Amma kundin bayan rahoton asirin ya ce wadanda aka kashe din ba su wuce mutum dubu bakwai ba; ba kamar yadda wasu ke cewa wai mutum dubu 30 ne aka kashe ba.Donald Patterson na sashen kula da harkokin siyasa, da kuma Tom Smith na sashen kula da harkokin tattalin arziki a ofishin jakadancin Amurka din a Nijeriya, a wancan lokaci, kamar yadda kundin ya ruwaito, sun yi wani balaguro daga Legas zuwa arewacin Nijeriya, bayan ‘wannan kisan kiyashin’, ga abin da suka fada: “Wuraren da ake ce da su Sabon Gari, duk sun zama kangayen da ba kowa a cikin su, sannan kuma ga barbadin komatsai a barbade a kasa an gudu an bari, saboda gaggawar neman tsira. “Akasarin ’yan Arewan da muka zanta da su kuma ba wanda ya nuna nadamar sa kan abin da ya wakana ga ’yan kabilar Ibo. “Akwai wata rana ma, da wani Ba’aren da kula mana da filawoyi, ya baraci wani dan kabilar Ibon da ke girki. Bayan nan kuma, ba da wata jimawa ba, sai wannan kukun ya samfe zuwa yankin Kudu maso Gabas.” Kalaman Patterson kenan.Kafin nan kuma da kimanin mako daya Yakubu Gowon ya kira Jakadan Jamus a Nijeriya zuwa ofishinsa; da ma kuma Jamusawan sun jima da suna zumudin samun fada a gun gwamnatin Gowon, amma ba su samu ba sai da yaki ya barke. Bayan kare yakin kuma za a gyara duk wasu gine ginen da yaki ya lalata.

Saboda haka, su a gun su, za ta fadi gasassa kenan. Kafin a kai ga haka da kimananin shekaru biyu, an riga an ba su kwangilar gina gadar Ikko, wacce babban shugaban kamafanin Julius Berger da Jakadan Jamus din a Nijeriya suka rattaba hannayen su a kan yarjejeniyar kwangilar; Alhaji Shehu Shagari kuma ya kattaba nasa hanun a madadin gwamnatin tarayyar Nijeriya, a lokacin yana babban kwamishinan ayyuka da aikin safiyo na tarayya. Wannan kuma ita ce kwangilar farko da kamfanin Julius Berger ya fara yi a Nijeriya, wacce kuma aka ce za a kammala ta a wa’adin kasa da shekaru biyu. Amma dai gwamnatin Jamus din ta nemi karin hadin kai a tsakanin kasashen biyu a wasu al’amuran.

Domin nuna ma Nijeriya cewa da gaske kasar sa ke yi, Jakadan Jamus a Nijeriya na lokacin ya bai wa Shugaban kasa Janar Gowon tabbaci ta wayar tarho cewa, kasar sa za ta yi dukkanin abin da ya dace don kiyaye lafiyar Edith, wacce Inyamura ce, sannan kuma kawar Shugaban kasa Janar Gowon ce.A yammacin ran 30 ga Yuni ana daf da za ta bar Nijeriya zuwa Jamus din, kawar Gowon din, Edith, ta fadi wa Jami’in kula da lamurran soja a ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya, Mista Standish Brook, da matarsa, Gail cewa, ta so ta je Amurka ko Birtaniya ne, amma bazawarin ta Jack, (wato lakabin da take ma Gowon kenan) ya nace cewa sai dai ta je Jamus; don kamar yadda ta ce ya ce, nan ne zai fi mata aminci.A ganin Manjo B.M. Usman, da sauran manyan Jami’an Soja ’yan Arewa wadanda su ne mukarraban Gowon din, Shugaban kasar ya rika jan kafa ne kan ’yan awaren, saboda gaskiyar cewa kawar sa Inyamura ce daga yankin Kudu maso Gabas; an kuma fatattake su daga Arewa sun koma yankin su da zama. Ana cikin hakan ne kuma, kwatsam, ba zato ba tsammani, a lokacin wani taron majalisar kolin mulkin soja, ran 3 ga Yuli, don kawar da wancan zargin da manyan Jami’an sa ke masa, Shugaban kasar ya bayar da umarnin da aka dade ana jira, na daukan matakin soja gaba gadi kan ’yan awaren.


ZA KU JI ABUBUWAN DA BAKU TABA JI BA A YAKIN BIAFRA.


Yadda aka soma dauki ba dadi a tsakanin gwamnatin tarayya ne da kuma ’yan awaren Biafra, bayan bazawarar Janar Gowon, Inyamura Edith, ta keta hazo zuwa Jamus.

kamar yadda rahotannin asirin da gwamantin Amurka ta saki a baya-baya nan, suka ruwaito. Sannan kuma, da matsayin wasu kasashen duniya dangane da fafatawar.

Ga dai kashi na biyun nan:Rahoton asirin ya ce, hatta wakilin jaridar Daily Times ma, Tunde Akingbade, lokacin da ya dawo daga bakin dagar, da akai masa tambaya kan halin da dakarun Nijeriya ke ciki, sai ya kada baki ya ce sojan bataliya ta daya dai da ke Ogoja “kusan gangamin nakiyoyi da wani makamin wutar lantarki, sun shafe su gabaya.”.

A ’yan makwannin farko da fara yakin dai, a cewar wannan rahoton asirin, sojan Biafra ne ke samun galaba. Domin, a wani sakon tangaraho da ofishin ya aike da shi ga hukumomin birnin Washington, ya musu cewa: “a yanzu haka hankula na kwance lami-lumui a birnin Enugu; har ma Ojukwu na can na biki da budeden shagali gami da shargalle da manyan Jami’an sojan da ke tafiyar da yaki a fagen fama.”.

A janibin gwamnatin tarayya kuma, a lokacin akwai dimbin rudu mai yawa; domin, ko kusa, ba ta zaci cewa dakarun Biafra da na karfin da za ta iya fafatawa da ita ba. “Hatta Janar Gowon da manyan mashawartan sa kan harkokin soja ma, suna jin cewa za a yi gagarumar nasara ce, kasantuwar suna jin cewa galibin sojojin duk Hausawa ne”,

a cewar Jakadan Birtaniya a Nijeriya, Sir Dabid Hunt, lokacin da yake tattaunawa da takawaran sa na Amurka a Nijeriya din, ran 31 ga watan Mayu 1967. Wannan Baturen Ingilishin ya ci gaba da gaya ma Ba’amuken cewa wai “dakarun Nijeriya ba su yi ma abin wani nagartaccen shiri ba; sun ma zaci abin bai wuce wani dan karamin farmki ne ba kawai da za su kai.”Kai, hatta dakarun da suka nausa zuwa Obolo ta hanyar Nsukka daga Oturko ma, sai da suka ci karo da tsattsaurar turjiya daga ’yan tawayen da ya mayar da su baya cikin sauki. Dalili kuwa, shi ne sun fuskanci karancin albarusai, wanda hedkwatan soja dake Lagos ya alakanta hakan ga sakacin kwamandan rundunar, Kanar Mahammad Shuwa (yanzu marigayi); aka ce shi ne ya dinga yi wa dakarun koron albarushi. Shi kuma ya maida martini ga hedkwatar tsaro ta kasa da cewa ai ita ce ba ta ba shi abin a wadace ba, sannan kuma kadan din ma ba ta bayarwa a kan lokaci, in ya mika bukatar san a albarusai da suran kayan daga.

Sammatsin hakan kuma, a lokacin, ya rika samuwa ne sakamakon cewa ba ta hanya daya kawai kayan fada ke fitowa ba, wato hukumar kula da sha’anin makamai na gwamnatin tarayya.Ana cikin wannan hali ne, kwatsam sai Manjo S.A Alao, a lokacin shi ne ke rikon mukamin kwamandan sojan jiragen sama, ya balle ya koma sahun ’yan tawaye tare da wani Barturen Jamus, wanda shi ne mai bayar da shawarwari kan harkar da ta jibanci sojan sama. Wannan Bajamushe dai, sunan sa Laftanar Kanar Karl Shipp. Wannan baturen ne, kafin ballewar sa, ya rika yi wa Jami’an Nijeriya rakiya zuwa kasashen Turai, don sayo jiragen saman yaki da kayyakin kula da su.

Don haka, da ya koma bangaren Biafra ma, aikin sa kenan. Amma dai ba a samun nasarar da ake so.Bangaren gwamnatin tarayya ma ya rika yawon neman taimakon kayan yaki a kasahen duniya, inda Janar Gowon ya rubuta takardar neman taimakon kayan yaki ga shugaban Amurka na lokacin, amma dai ba cimma nasara ba.

Domin ma’aikatar harkokin wajen Amurka a lokacin, ta daukin matsayin cewa ba za ta tallafawa ko wane bangare da kayan yaki ba. Amma dai, ko wanne daga cikin mafadatan biyu, na da ’yancin sayen makamai daga kasuwannin makaman da ke cikin Amurka din.

Hukumar leken asirin Amurka ta CIA, a nata hasashen, ta ce bangaren Biafra ne zai yi nasara; yayin da Jami’an jakadancin kasar a Nijeriya kuma, suka yi kintacen cewa sashen gwamnatin tarayya ne ke da galaba a fafatawar da ake yi. Sannan kuma, in ji Jami’an difulomasiyar, dunkulalliyar Nijeriya ce za ta fi bayar da daman cimma muradun gwamantin Amurka sosai da sosai; fiye da a ce an yi Nijeriya ba yankin gabas maso kudu.

Wannan harshen damon da aka samu a tsakanin sassan biyu; mashahuriyar hukumar da tasirin ta ke da tasiri mai nauyi a gwamnatin Amurka; da kuma Jakadancin ta da ke kasar, wanda shi ne jiyau da ganau din duk wata sabata-juyatan da ake yi.

Shi ya sa ta ce, ta bakin sakataren harkokin wajen ta na lokacin, Mista Dean Rusk, to ita ’yar ba ruwanta ne a rikicin.Birtaniya kuma, a bangare ta, a lokacin wannan yaki, jan kafa ta rika yi.

Amma saboda naciyar Cif Obafemi Awolowo din da a lokacin ake masa lakabi da Mukaddashin Firaminista a duniyar difulomasiyyar lokacin, sai ya karkatar da akalar gwamnatin Janar Gowon zuwa ga tarayyar Sobiyet.A wani sakon wayar kebur kuma da Jakadan Amurka na lokacin a Jamus, Dk. Martin Hillenbrand ya aike wa takwaran sa da ke birnin Lagos, ya tsaigunta masa cewa Mista MCK Ajuluchukwu, wakilin musamman na Kanar Ojukwu ya gana da Jakadan tarayya Sobiyet a Nijeriya, Mista Aldender Romanob, a birnin Moscow, cikin Yunin 1967, inda Ajuluchujwu din ya lallami tarayyar Sobiyet din da ta amince ta samar wa da Biafra makamai. Inda shi kuma Alededer ya ce to sharadin haka shi ne ballalliyar gwamnatin tawayen ta mayar da bangaren man fetur ya zama mallakar kasa ne baki daya tukun, in har tana son hakan. Amma Ojukwu ya ki amincewa da wannan bukatar, bisa hujjar sa cewa ba shi da kudin da zai biya sauran kamfanonin man da ke hannayen jari a harkar; sannan kuma gwamnatin Biafra ma ba ta da kwararrun da za su iya sarrafawa da kuma tafiyar da na’urorin harkar man fetur din.Gazawar Biafra kan haka ke da wuya, wata daya kacal bayan nan, sai Mista Anthony Enahoro, Kwamimishinan yada labarai da kula da harkokin kwadago na tarayyar Nijeriya, ya ziyarci birnin Moscow, inda ya kattaba hannu kan yarjejeniyar musayar al’adu da Rasha; kana kuma ya yi alkawari a madadin gwamnatin tarayya cewa za a mayar da harkokin mai man fetur din kasar da ma duk ababan da suka jibance shi, su zama na kasa baki daya; matukar dai Rashar za ta bai wa Nijeriya makaman da za ta yaki ballallen yankin Biafra da su, da nufin mayar da Nijeriya dunkulallar kasa daya.

Jin haka ke da wuya, cikin ’yan kwanaki kadan, sai ga maka-makan jiragen sama dauke da kayan harhada jirgin yaki samfurin Migs 15 sun sauka a filayen jiragen saman Kano da na Lagos, sai harhadawa kawai ake jira. Amma ba mayar da bangaren mai ya zama na kasa baki daya ba.Ita kuma gwamnatin ballalliyar Biafra, saboda jin dadi da kuma farin cikin nasarar da ta samu a kafsawar baya ta hanyar amfani da jirgin ta mai saukar ungulu, samfurin B26; sai ta sake dasa ma wannan jirgin wani bindigan mashingan mai baki barkatai wand ta farmaki biranen Kano, Kaduna da kuma Makurdi da shi. A Kano ne aka dan yi rashin sa’a, duk da cewa ba samu rasa rayuka ba, amma dai wannan harin ya dan kwarzani fukafikin wani jirgin saman fasinja da ke tsaye a Kanon. Amma a Kaduna kam, B23 ya yi kashin bama-baman da suka dagargaza gine-gine da dan dama a sansanin sojan sama da ke birnin.

Jami’in kula da bangaren al’adu na karamin ofishin jakadancin Jamus da ke Kaduna ya tabbatar da aukuwar wannan farmaki, inda y ace wani injiyan gyaran jiragen sama Bajamushe ma da aka sa shi aikin gyaran wasu jiragen saman yakin Nijeriya ya mutu a wannan farmaki, ya rasa ran sa, wasu mutum biyu kuma sun raunata a wannan farmakin na ran 10 ga watan Agustan 1967.Mako daya bayan wannan farmakin ne aka damke Mista A. O. Amaku, wanda shi ne babban jami’in kula da sashen sauka da tashin jirage sama a filin jirgin saman Kaduna bias zargin sad a yi zakon kasa, saboda ya kashe na’urar da ke hango jiragen saman da ke tafe. Wannan ya baiwa jirgin farmakin Biafra daman isowa ba tare da an sani ba, har ya yi barnar day a yi. Kazalika kuma an zargi mataimakin sa dan kasar Birtaniya, Mista Palfrey.

Wannan ya sa a yi murabus daga mukamin sa kuma ya samfe gida Ingila. Ba shakka, a cewar rahoton sirrin Amurka, wannan farmakin ya tunzura arewawa da dama suka dinga tururuwa zuwa barikokin soja mafi kusa da niyyar shiga aikin soja don zuwa fagen daga. Za a ci gaba a fitowa ta gaba.A wani sakon tangarahon da Jakadan Amurka a Nijeriya, Mista Elbert Matthew ya aika wa hukumomin birnin Washington a cikin watan Yulin 1967, ya ce; wasu mutanen da aba san su ba sun yi yunkurin dargwaza wani shirgegen bom a hedkwatan ’yan sanda na Lagos a daren 2 ga watan Yulin 1967.

Sannan kuma wasu ’yan kunan bakin waken sun yi kokarin tuka mota cike da bama-bamai don shigar da ita cikin harabar hedkwatar ’yan sanda amma Jami’an da ke gadin a daren suka hana su, sai suka ajiye motar a gefen hanya, kusa da wani gidan mai. Barin gun da suka yi ke da wuya, sai bom din da suka dana a cikin motar ya dargwaje; gidan da ke kusa ya rushe a kan dukkanin mutanen da ke cikin sa suka mace, amma gidan man da ke kusa bai samu ko da kwarzane ba.

A wannan fashewar dai, mutum 11 ne suka samu raunuka, cikin kuma har da wasu daga cikin ’yan sandan da ke gadin hedkwatar, a wannan daren.

Za mu ci gaba Insha Allah.


KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN YAKIN BASASAR NIGERIA


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user