Monday 15 April 2019

HOTUNA DA CIKAKKEN TARIHIN SHEIKH JA'AFAR MAHMUD ADAM: ABUBUWAN DA YAKAMATA KU SANI DANGANE DA RAYUWAR MARIGAYI SHEIKH JA'AFAR MAHMOUD ADAM

Tura Wannan Zuwa
An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam a garin Daura, a shekara ta 1962 (ko da yake wani lokacin yakan ce 1964).

Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam

Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ya fara karatunsa na allo a gidansu, a wurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini.

Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin su, wanda kuma shi ne musabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano.

Tun kafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Jaafar ya riga ya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978.

Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar
ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980.

Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian
Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru
na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu.

 Haka ya rika yin wannan karatu guda biyu:

Waccan makarantar ya je ta da daddare bayan sallar isha'i, waccan kuma ta koyo harshen larabcin da yamma.

 Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar
GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988.

A shekara ta 1989, malam jafar ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci, A Oundurman Sudan.

Sannan kuma, kafin rasuwarsa, ya riga ya yi nisa wajen karatunsa na digiri na uku, wato digiri da digirgir (PhD), a Jami’ar Usman Ɗan Fodiyo da take Sokoto.


Sheikh Ja'afar Mahmoud 

Daga cikin malamansa na ilimi, akwai:

- malaminsa na farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa

- Malam Nuhu a unguwar Dandago, wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi a gurinsa

- Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab a wajensa.

-Sheikh Abubakar Jibrin limamin masallacin Juma'a na BUK

- Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano.

Daga cikin malaman mallam jafar na jami'a kuma akwai:

 Sheikh Abdurrafi'u da Dr. Khalid Assabt.

Sheikh Ja'afar Mahmoud 

Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar da su, sun hada da:

1. Karatun alkurani mai girma wato sheikh ja'afar mahmoud Holy Quran recitation

2. Complete tafseer of the Holy Quran mp3 sheikh jafar Mahmud

3. Kitab tauhid

4. Umdatul Ahkaam

5. Arba'una Hadith

6. Kashfusshubuhaat

7. Bulugul Maraam

8. Riyaadussalihiin

9. Siratun Nabawiy

10. Ahkaamul Janaa'iz

11. Siffatus Salaatun Nabi

Shin ko kunsan Baiwa 11 Da Allah Ya Yi Wa Sheikh Ja'afar Yayin Rasuwarsa?


Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam a

1. SHAHADA: Ya yi Shahada iri daya da ta Sayyidina Umar (R.A).

2. Ya rasu ranar Juma'a: Rasuwar Ranar Juma'a alama ce da ake kyautata wa Mutum zato ya samu dacewa.

3. Mahaddacin Alkur'ani ne: Ana kyautata zaton duk wanda ya haddace Alkur'ani Mai Girma ya kuma kiyaye shi ya yada shi. Zai samu rabauta ranar Lahira.

4. Kisan Gilla: Duk Muminin da aka yi wa kisan gilla ana sa ran laifukan sa sun rataya a wuyan wanda ya kashe shi.

5. Ya cika da kalmar SHAHADA: Kafin rasuwar sa an ji shi ya na maimaita kalmar La ila ha illallah Muhammadur Rasulullah

6. Dandazon Mutanen da suka halarci jana'izarsa: Ana kyautata zaton duk mamacin da mutane 40 suka halarci jana'izarsa wadanda ba sa shirka zai samu dacewa.

7. Ya rasu ya na Sallar Asuba. Sallar Asuba na daya daga cikin Sallah mai madaukakiyar daraja.

8. Limami ne shi: Jagorancin Sallah wata babbar baiwa ce da ke kusanta Bawa zuwa ga Allah.

9. Ya Karanta Suratul MA'ARIJ: Kafin a kai ga kashe shi ya karanta sura daga cikin Alkur'ani Mai Girma.

10. Ya Dago Daga SUJADA: Sai bayan da ya dago daga sujada sannan makisan sa suka fara harbin sa.

11.Ya Nemi Gafarar Mutane Kafin Rayuwar sa. (Duk wanda na yi wa ba daidai ba don Allah ya yafe min).

Kafin rasuwarsa, malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin cibiyar (Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre).

Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (13/04/2007) sakamakon harin da wadansu 'yan ta'adda suka kai masa, a dai-dai lokacin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin Juma'a na Dorayi.

Ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 dai-dai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa.

Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka halarci jana'izarsa, kuma an binne shi ne a makabartar Dorayi.

Allah ya jikan malam yasa Aljannah makomarsa.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user