Monday 15 April 2019

MU SHA DARIYA: INA 'YAN BOKON SUKE?

Tura Wannan Zuwa Ga
Wasu daliban Jami'ane suka tafi Night club sukai abin nan da ake kira da TILL-DAWN.

Kuma sun san suna da jarrabawa washe gari, gashi kuma basuyi karatu ba.

Saboda haka suka shirya yiwa farfesa karya.

Sai suka sanya kaya masu datti kuma suka bata jikinsu da bakin mai.

Da suka je ofis din Farsesa sai suka ce masa jiya da daddare sunje bikin abokinsu a wani kauye mai nisan 100km, a kan hanyarsu ta dawowa sukai faci, shine suka turo motar sai yanzu suka dawom; saboda haka suna neman Farfesa yai musu afuwa su dan dawo hayyacinsu kafin su zana exam din.

Farfesa da yaji haka sai ya tausaya masu yace suje nan da kwana uku su dawo.


Bayan kwana 3 suka dawo, farfesa yace dasu tun da dai wannan jarabawa ce ta musammman kowanne daya daga cikin su hudun nan za a sashi a aji daban-daban baza a hada suba.

 Dayake sun yi karatu sosai kuma sun shirya basu damuba sukace sun yarda.....


Jarabawar dai tana da Jimillar maki 100 kuma ta kunshi tambayoyi Guda biyar.

Amman da sharadin idan daya daga cikinsu ya amsa ba daidai ba to dukkan su hudun zasu samu zero mark.


Tambaya ta 1:

Rubuta sunan ka da lambarka...(20point)

Tambaya ta 2:

Ya sunan Ango da Amaryar da kuka je bikin su  (30marks)

Tambaya ta 3:

Wacce irin Mota kuke tukawa (20marks)

Tambaya ta 4:

Waye acikinku direban Motar (15point)

Tambaya ta 5:

Tayar wanne bangare ce tai facin?

(15marks)

In ka/ki na cikin su ya za ka/ki yi?


HahahahaShafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user