Tuesday 2 April 2019

Karanta Ka ji: Tatsuniyar Gizo da Budurwar Danko Labari Mai Kayatarwa

Tura Wannan Zuwa Ga
GATAN GATAN KU TAZO MU JITA...



Gizo ne dai da koki. Shi ke nan. Shi Gizo ne dai da matarsa koki. Yauwa to.

Shi ke nan, sai ya ce zai yi shkar gyada, shi kuma daman ba shukar gyada zai yi ba. To shi ke nan sai ya yace a soya masa gyadar, sai aka soya wa Gizo gyada.

Daman sai ya zauna Gizo ya cinye gyadan nan, ya tafi jeji ya je ya yi birgima, ya je ya yi birgima, ya dawo ya ce da koki, koki, na dawo daga -- na dawo daga wajen gonar.

Sai ta ce, Yauwa, Gizo, sannu, sannunka. Ai gara da ka je ka zago gun aikin. Nan ko daman ba aikin yake zuwa ba.

Har kak har kaka ta yi. Lokacin gyada ya yi, sai ya je gonar, Gizo ya je gonar sarki. Daman da ya je gonar sarki ya je gonar sarki, sai ya je ya cicciro gyada kullum. Yana zuwa gonar sarki yana ciro gyada yana kawo wa koki.

Shi ke nan sai rannan sai sarki ya ce! Wannan barna dai ta isa. Bari dai yau - bari dai yau in yi fakon ɓarawon nan da yake satar mini gyadata. Da mun tura fadawa.

Daman Gizo da man da ya ji labarin - mm sarki zai tura fadawansa daman sai ya yi shiga buta. Ya shiga cikin buta, ya je ya buya. Daman da fadawan sarki suka zo sai ya taho yana:

Kurtu bambam kurtu

Kurtu maci dan sarki

Kurtu maci fadawa

Kurtu maci fadawan kansa.

Shi ke nan sai fadawan sarki suka zura a guje, suka ce ba za su iya ba sai sarkin ma ya ce, to, ku, mu je.

Sai sarki ya yiwo shiri shi ma ya taho daman da ya taho shi ma sai maza Gizo ya kuma - ya kuma shiga cikin buta. Sai ya kuma ce masa,

Kurtu bambam kurtu

Kurtu maci ɗan sarki

Kurtu maci fadawa

Kurtu maci fadawan kansa.

Nan ma sai ya koma rugawa a guje. Sarki ya ce ba zai iya ba.


Sai aka ce a yi budurwar danƙo. Sai aka yi budurwar danko.

Daman - daman da ya zo aka shirsshirya mata kayan abinci masu daɗi. Aka zo aka ajiye.


Daman da Gizo ya zo ya ga wannan budurwar dankon. Sai ya ce, a'a! Wannan 'yar budurwar, kina da kyau. Bari in ci dan abinci naki ne? Ya dauki abincin nan ya ciccinye, ya ciccinye abincin.

Sai ya ce, Yar budurwa budurwa, mu ga jikin naki. Sai ya taba, sai ya make, ya koma tabawa, ya koma makewa. Har sarakan suka zo suka same shi. Yana tsaye a halin da yake. Shi ke nan sai suka kama shi suka je suka ɗaure shi.

Sai kura ta zo ta ga Gizo a ɗaure sai ta ce, Taf! Gizo? Me ya same ka kake ɗaure? Sai ya ce, Da Allah, gafara can.

Nima da za'a kawo mini sa. Ya ce, To, kunce ni! Mm. Bari in kunce ka, ni ka daure ni. Ni a kawo mini san. Shi ke nan sai ta ce, to
Sai Gizo ya kunce mm kura ta kwance Gizo. 

Ta daure mm Gizo ya daure kura. Daman sai fadawa suka zo. Sai suka zo suka ga kura sai suka ce, ila! Kun ga Gizo ya zama kura. Nan ma suka samu suka yimata dukan tsiya, suka yimata dukan tsiya. 

Shi ke nan sai gara ta zo sai ta ce, ku ne dai mutanen zamani, a yi muku rana ku yi mutum dare.

Sai ta ce, Ba zan miki ba.

Sai ta ce, To, taushe ni. Sai ta taushe mata igiya. Sai ta ce wa gara, Gara, taru mani in yi miki addua. Sai gara ta taru. Ta lashe ta, da ta lashe ta Gizo ya samu ya gudu. Sai kura ta samu, ta tafi.

Ashe da ma Gizo ya hau kan kanya. 

Sai wannan kura ta je gindin kanya.

Sai Gizo ya ƙwalo mata kanya mai zafi.

Sai ta ce, ìKai! Kai! Kai! Wannan dana tsuntsu, Allah ya tsine aka albarka!

Sai ta daga kai sai ta ga Gizo. Sai ta ce, ìAaaa! Gizo, to sauko, sauko in cinye ka.

Sai ya ce, ìTo, ban da abinki ana cin mutum da guntun kashi a ciki?

Sai ta ce, to sai ta ce, To tafi ka je ka yiwo.
Ya ce, In tsuguna anan?

Sai ta ce, A'a.

in tsuguna anan?

Ta ce, A'a.

in tsuguna anan?
Ta ce, "I'

Can da nisa.

in tsuguna anan?

Sai ta ce, E, to tsuguna anan.

Sai ya ce, Na'am? Sai ya ce, Iye?

Ta ce, Kai kai da kai da waye kai kuma kake maganar?

Sai ya ce, A'a, cewa aka yi in na ga kura da guntun kirgi in kirawo ta.

Shi ke nan, ta ruga a guje, sai ta gudu. 

Ƙurunƙus kan ɗan ɓera.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user