Wednesday 3 April 2019

ME CE CE SALLAH A TAKAICE?

Tura Wannan Zuwa Ga
Sallah na nufin addu'a.

Sallah acikin Addinin MusulinciAmma a shari'ance ibada ce ma'abociyar karatu da ayyuka kebabbu, da ake fara ta da kabbara a kuma rufe ta da sallama, sallah ita ce rukuni na biyu a cikin Addinin Musulunci bayan kalmar shahada, wato (ASH'HADU AN LA ILAHA ILALLAHU WA ASH'HADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH) sai ita.

kuma ita ce kashin bayan addini, saboda girmanta da matsayinta Allah bai aiko mala’ika da ita ba sai Allah Madaukakin Sarki Ya kirawo Annabi (SAW) a daren Isra’i da Mi’iraji ya bashi ita.

Yana daga girman sallah ambatonta da Allah Madaukakin Sarki Yayi sau hamsin da takwas (58) a cikin Alkur’ani, kamar inda yake cewa:

{وَأَقِيمُوا الصَّلَوةَ} [البقرة: 43]

Ma'ana: "Ku tsaida sallah"

{قُلْ لِعِبَادِيَ الَّذِينَ آمَنُوا يُقِيمُوا الصَّلَوةَ}[إبراهيم: 31]

Ma'ana: "Ka fada (Ya Muhammad S.A.W) ga bayina da suka yi imani su tsaida sallah".

Da sauran wurare a cikin Alqur'ani da dama.

Annabi (SAW) yana cewa: “Bainar rajuli wabainal kufri tarkus salati” (Rawahu Muslim).

Ma’ana: “Tsakanin mutum da kafirci shine barin sallah”.

Kuma ana umartar karamin yaro da yin Sallah tun yana dan shekara bakwai, kuma in ya kai shekara goma a doke shi in ya ki yi.

Sallah bata yiwuwa sai da alwala.Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user