Showing posts with label Tatsuniyoyi daban-daban. Show all posts
Showing posts with label Tatsuniyoyi daban-daban. Show all posts

Friday, 16 August 2024

Gajeriyar Tatsuniyar Yara Mai Dadi Ta Wani  Jaki Da Abokan Shi

Gajeriyar Tatsuniyar Yara Mai Dadi Ta Wani Jaki Da Abokan Shi

Wani manomi ne dai ya ke da jakinsa wanda ya ke aiki da shi shekara da shekaru. A kwana a tashi jaki ya fara tsufa har ba ya iya moriyar maigidansa da komai. Da manomi ya ga haka sai ya fara shawarar yadda zai rabu da jaki ko ma ya halaka shi ya huta da ciyar da shi da ya ke yi kullum.


Tatsuniyar Jaki Da Abokan Shi
Hoto: Contosdefadascomagigi


Marubuci: Bukar Mada


Da jaki ya gane abin da manomi ke shirin ƙulla masa sai ya gudu. Ya ce a ransa, "Bari na shiga birni na koyi waƙa, wata ƙila na zamo mai dogaro da kaina!" 


Yana cikin tafiya a hanya, sai ya haɗu da kare yana kwance a gefen hanya, sai faman fuka ya ke yi. Jaki ya tambayi kare me ya same shi ya ke ta fuka?


Kare ya ce, "Ai da ƙyar na sha a hannun mai gidana, wai zai kashe ni saboda yanzu na tsufa ba na iya farauto masa komai. Yanzu ina tunanin yadda zan yi da rayuwata in riƙa samun abinci"


Jaki ya ce, "Af! Matsalarmu ɗaya da kai. Ni zan shiga birni ne na koyi waƙa, idan za ka bi ni taso mu je." Kare ya tashi ya bi Jaki suka ci gaba da tafiya.


Ba su yi nisa da tafiya ba, sai suka haɗu da kyanwa/mage a kan hanya, tana tafiya shajaran majaran, kamar wadda aka tsamo daga cikin ruwan zafi.


Jaki ya dube ta ya ce, "Ah, su maguru 'yan gatan mutane, yau kuma me ya same ki duk kamarki ta canja haka?"


Kyanwa ta dubi Jaki ta ce, "Ba dole kamata ta canza ba, uwargijiyata na neman ta halaka ni wai saboda na tsufa, ba na iya kama ɓerayen da suke yi mata ɓarna a gida. Sai dai na sha madara na kwanta a kan shimfiɗa ina lashe jikina. Wai ita ta gaji da ba ni madara tunda ba ni da moriyar komai. Yanzu ban san yaya zan yi da rayuwata ba."


Jaki ya ce, "Kai 'yan Adam akwai butulci, mu ma abinda ya faru da mu ke nan. Za mu shiga birni mu koyi waƙa, mu dogara da kanmu, idan za ki bi mu shi ke nan." Kyanwa ta amince da bin su.


Jaki da kare da kyanwa suka kama hanya suka nufi birni. Suna cikin tafiya sai suka haɗu da zakara, gashin jikinsa a yamutse. Jaki ya tambaye shi abin da ya same shi.


Zakara ya ce, "Na yi daron yanka ne! Yau ina cikin hutawa sai na ji maigidana ya kama ni, wai zai yanka wa baƙonsa da zai kawo masa ziyara, ni kuwa ban san lokacin da na fizge daga hannunsa ba. Ina cikin gudu ke nan muka haɗu da ku."


Jaki ya ce, "Mu ma nan duk guduwa muka yi daga iyayen gijinmu. Za mu shiga birni ne mu koyi waƙa, idan kana da sha'awa ka biyo mu mu tafi. Zakara ya bi su, suka rangada.


Can sun kusa isa birni sai dare ya yi musu. Jaki ya ce su kwana a nan kafin gari ya waye su shiga birni. Suka sami wata babbar itaciya, Jaki da Kare suka kwanta a ƙarƙashin ta, Kyanwa da Zakara kuwa suka hau saman itaciyar. Zakara ya haye can ƙololuwar itaciya.


Da dare ya fara yi sosai, sai Zakara ya ƙyalla ido ya hango hasken wuta can nesa da su. Ya faɗa wa saura, suka ce lalle gida ne inda hasken nan ke fitowa, yana da kyau su matsa can su kwana, da su kwana cikin daji. Suka tashi suka nufi inda hasken ke fitowa har suka zo dab da shi. Suka ga ashe gida ne, kaɗe-kaɗe da bushe-bushe na fitowa daga ciki.


Suka matsa kusa da wani ɗaki da tagarsa take a buɗe. Da ya ke Jaki ya fi su tsawo, sai ya leƙa ta tagar. Ya ga mutane ne zaune, suna ci suna sha, wasu kuma suna kiɗa da busa da rawa. Jaki ya faɗa wa abokan tafiyarsa abin da ya gani. Ya tambaye su ko akwai dabarar da za su yi su kori mutanen nan su mallake gidan, su yi zamansu a nan suna koyon waƙa.


Kare ya ba da shawara cewa, zai hau bayan Jaki, kyanwa ta hau bayansa, Zakara ya hau bayan Kyanwa, su afka cikin ɗakin, mutanen za su ji tsoro su gudu su bar musu gidan. Duk suka amince da wannan shawara ta kare.


Kare ya hau bayan Jaki, kyanwa ta hau bayan Kare, Zakara ya hau bayan Kyanwa. Suka shiga gidan, suka zagaya ta ƙofar ɗakin, suka afka cikin ɗakin. Jaki ya ƙwala kuka, kare ya yi haushi, kyanwa ta yi kuka, zakara ya ƙwala cara. Mutane suka firgita, suka yi waje da gudu, suka bar kayan kiɗa da busa.


Jaki, kare, kyanwa da zakara suka zauna suka ci suka sha, suka yi hani'an. Sun samu gida, ga kuma kayan waƙa sun samu. Da suka gama cin abinci, suka kwanta domin su huta, zuwa da safe su fara koyon waƙarsu.


Mutanen nan kuwa da aka kora daga cikin gida, suka yi ta mamakin abin da ya koro su daga cikin gidan nan. Can suna tsaye suna hangen gidan daga nesa, sai suka ga an kashe wutar gidan, ya koma cikin duhu. Sai wani mutum mai ƙarfin hali da jarumta a cikinsu ya ce zai je ya dubo ko mene ne a cikin gidan nan.


Ya tafi har ya shiga cikin gidan, ya shiga cikin ɗaki. Ya laluba inda ashana ta ke ya ɗauka. Ya ƙyasta domin ya kunna fitila, sai kuwa hasken ashanar nan ya ɗauko idanun kyanwa, ya gansu war war war. Sai ya tsorata ya yi waje da gudu, wajen fita ya taka wutsiyar kare, da kare ya ji zafi sai ya zafga masa cizo a ƙafa har jini ya fita. Ya ƙara ruɗewa ya faɗa wa jaki. Jaki kuma ya taƙarƙare iya ƙarfinsa ya watsa masa harbi, ji kake tim!


Mutumin dai ya yi ƙarfin hali ya fita da gudu. Kafin ya fita kuma zakara ya yi tsalle ya karta masa yaga a fuska. Yana isa wurin 'yan uwansa, sai ya ce musu ai sarkin aljanu ne ya sauka gidan da rundunarsa gaba ɗaya, akwai masu wuƙaƙe, akwai kuma masu kulake, don haka kada wanda ya kuskura ya ƙara zuwa kusa da gidan nan.


Jaki da kare da kyanwa da zakara suka yi zamansu cikin gidan nan, ga abinci da ruwa, ga kuma kayan kiɗa da busa. Suka yi ta koyon waƙarsu, ba  wani mutumin da ya ƙara kuskura ya matsa kusa da gidan nan, ballantana a dame su. Wa ma zai matsa kusa da fadar sarkin aljanu ya sha kulake!


Kurungus kan ɗan ɓera, ba don gizo ba, da na yi ƙarya....!

Saturday, 18 May 2024

Karanta Tatsuniyar Manomi Da Jaki

Karanta Tatsuniyar Manomi Da Jaki

INA YARA?


GA-TA-NAN GA-TA-NANKU


Wani manomi ne yake da Jakinsa da yake hawa kullum idan zai je gona. Manomin nan na kula da jakinsa matuka. Ana ba shi abinci mai kyau da ruwa, kuma kullum ana share masa wurin kwanciyarsa. Ran nan bayan manomi ya dawo gona da jaki, ya zauna yana hutawa, Jaki kuwa yana kwance can gefe cikin inuwa, sai ga wani ɗan kwikwiyo ya zo gaban manomi yana 'yan tsalle-tsallensa na wasa yana lasar kafafun manomi. Manomi kuwa yana kallonsa yana dariya, har dai ɗan kwikwiyo ya faɗa bisa jikinsa.


Tatsuniya
Hoto: Next Avenue


Manomi ya riƙa shafa jikin ɗan kwikwiyo cikin jin daɗi, ya sa hannunsa cikin aljihu ya fito da wani abinci ya ba ɗan kwikwiyo. 


Ashe duk abin nan da ake yi Jaki da ke can gefe kwance yana kallo. Shi ma sai ya tashi yana tsalle-tsalle, kamar yadda ya ga ɗan kwikwiyo, na yi, wai shi ma ya burge mai gidansa.


Da manomi ya ga haka sai ya fara dariya, Jaki kuwa ganin ya fara shiga gun mai gida, sai ya matso ya ɗora wa mai gida ƙafafunsa, wai shi ma zai hau jikinsa kamar yadda ɗan kwikwiyo ya yi.


Ko da yaran mai gida suka ga Jaki na shirin lahanta mai gida, sai suka taso masa da kulake, suka yi ta ɗimar shi. Jaki ya gudu yana cewa: " Ashe dai inda wani ya yi rawa aka ba shi kuɗi, idan wani ya yi duka zai sha.".


KURUNGUS.


Tushe/Asali: Kundin Tsatsuba 

Friday, 23 August 2019

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WATA MARAINIYA DA DAN SARKI

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WATA MARAINIYA DA DAN SARKI

Akwai wata yarinya marainiya, watau wadda take ba uwa ba uba; kuma ita kadai ce a wurin mahaifiyarta, lokacin da mahaifanta suka rasu suka bar ta. Ta sha wulakanci a wurin kishiyar uwarta, wadda take da ’ya’ya maza da mata, wadanda duka suka taru a kanta suka rika yi mata wulakanci.

Labarin Marainiya da Ɗan Sarki




Marubuci: Bukar Mada

+2348021218337

Daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI 1

DR. Bukar Usman


Gidan Dabino Publishers 2012

A cikin wannan yanayin kullum da sassafe takan je gindin wata kurna ta zauna, ta yi ta kuka.

Wannan kurna tana yin ’ya’ya masu yawa, ga kuma zaki zakwai. Abincinta ke nan daga safe har yamma, kuma idan za ta koma gida sai ta debo wadanda za ta ci da dare.

To akwai wani dan sarki kyakkyawa, mai suna Aminu, wanda ’yar kishiyar uwarta take so, to amma shi kuma ba ya son ta. Shi ma kuma yakan je shan iska, ya hau kan wannan bishiyar kurna da marainiyar take zama a gindinta, ta sha ’ya’yanta, yana kallon kowa, amma babu wanda zai gan shi don ganyen bishiyar ya boye shi.

Shi ke nan, wata rana marainiya tana zaune sai dan sarki ya sauko daga bishiya sai ya ce: “Sannunki ’yan mata.”

Sai ta ce: “Yauwa samari."

Aminu ya ce: “Me ke damun ki ne? Kullum sai in zo in gan ki a gindin wannan bishiya, har ma domin tunanin da kike yi ba ki sanin zuwana, kuma ga shi kikan riga ni zuwa don ni sai da la’asar nake zuwa, har in hau bishiya ba ki gan ni ba.”

“To yaya kake zama a kan bishiyar kuma mai kaya?" Ta tambaye shi.

Sai ya ce: “Ni na san dabarar da nake yi.”

Haka dai suka ci gaba da hirarsu har ya kawo ga maganar aure, sai ta ce: “Ni dai marainiya ce, ba ni da uwa, ba ni da uba.”

Sai Dan sarki Aminu ya ce: “Yau na zama uwa da uba a wurinki.”

Suna nan yana kiran ta, har ya fara zuwa gidan su marainiya. Da ’yar kishiyar ta gane Dan sarki ne yake zuwa wurinta, sai ta ce ta san makircin da za ta yi. Sai ta sayo allurai da yawa ta je ta sossoka a inda Aminu yake zama idan ya zo wurin marainiya. Da zuwansa sai ya zauna a kan alluran nan, kuma gaba daya alluran suka shiga jikinsa.

Nan da nan ya fara jin zazzabi, ya tashi ya tafi gida. Ciwon Dan sarki dai ya gagara warkewa, babu irin maganin da ba a yi ba.

Wata rana marainiya ta tafi diban ruwa a rafi, sai ta ji aljanu suna maganar Dan sarki ba shi da lafiya, amma da an samo kashin tsutsotsi masu cin mutane a bayan wani gari mai nisa, aka jika masa ya sha to zai warke.

Da marainiya ta ji sai ta yi maza ta dauki goranta, ta je gida, ta aske kanta ta shafe jikinta da bakin tukunya, ta sa kayan maza, ta Dauki kwano, kamar almajiri zai je bara.

Ta kama hanyar wancan gari mai nisa, inda za ta samo kashin tsutsa mai cin mutum, har sai da ta yi tafiyar shekara biyu kafin ta isa wurin tsutsotsin. Sai ta je wurinsu a hankali, ta kwanta don in sun ji motsin tafiyarta za su cinye ta. A hankali ta yi ta lalubowa dai dai. Bayan ta sami abin da ta je nema, sai ta kama hanyar garinsu, ta isa lafiya.

Bayan ta dan huta, sai ta kama hanyar gidan Sarki, ta tarar mutane makil sun cika fada suna jiran mutuwar Aminu. Da zuwa fada sai ta fara bara, mutane sun Dauka namiji ne, suka ce: “Kai kana ganin dan sarki babu lafiya amma sai ka zo ka yi mana bara don ba ka da kunya?" Sai ta ce: “Ku bar ni in duba shi ko zai warke. Akwai wani magani da nake tafe da shi." Sai suka daka wa Dan almajiri tsawa, suka ce: “Duk duniyar nan babu wanda zai warkar da shi sai kai?”

Sai ta ce: “A bar ni mana in dan gwada.”

Da kyar aka bar shi ya shiga. Da shiga sai ta ciro wannan kashin tsutsa, ta jika, ta ba dan sarki, ya sha. Cikin ikon Allah nan take sai ya fara amai, duk ya amayar da ciwon da ke damunsa, ya warke sarai. Kowa yana mamakin dan almajiri.

A cikin farin ciki Sarki ya ce: “Zan ba ka gida da dawakai da dukiya mai yawa.” Shi ma Sarki bai san da mace yake magana ba.

Sai ta ce: “A' a ba na son wannan.”

Sai Sarki ya ce: “To me kake so?”

Ba tare da bata lokaci ba, marainiyar da ake zato namiji ce ta ce: “Ni dai babu abin da nake so kamar zoben hannunsa.”

Dan sarki Aminu bai taba zaton zai rabu da wannan zobe ba, amma sai ya cire ya ba ta.

Ta karba ta tafi.

Bayan kwana biyu sai ya je gidan su marainiya a cikin fushi, ya ce da ita: “A duk garin nan babu wanda bai san da rashin lafiyata ba, amma ke ba ki taba zuwa gani na ba."

A cikin tattausar murya ta kalle shi ta ce: “Zauna ka ji labari.”

Ya zauna ta fara gaya masa yadda ta yi. Da ta gama sai ya ce: “Karya ne, idan maganarki gaskiya ce, to me aka bai wa dan almajirin?”

Sai ta ce: “Zobe.”

Ya ce: “To idan ke ce, nuna min zoben.”

Sai ta dauko ta ba shi.

Ya duba zobe, ya tabbatar zobensa ne. Daga nan ya fara mamaki. Ya dauke ta suka je gaban babansa, suka gaya masa labarin kome. Ya sa aka daura musu aure, aka yi gagarumin biki, kuma aka ba su kyautar gari guda da dukiya mai tarin yawa, suka ci gaba da cin duniyarsu da tsinke.

Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa:

1. Rabon kwado ba ya hawa sama

2. Mai nema yana tare da samu

3. Mai rabon ganin badi ko ana ha maza ha mata sai ya gani.

4. Hassada ga mai rabo taki ce.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








Tuesday, 2 April 2019

Karanta Ka ji: Tatsuniyar Gizo da Budurwar Danko Labari Mai Kayatarwa

Karanta Ka ji: Tatsuniyar Gizo da Budurwar Danko Labari Mai Kayatarwa

GATAN GATAN KU TAZO MU JITA...



Gizo ne dai da koki. Shi ke nan. Shi Gizo ne dai da matarsa koki. Yauwa to.

Shi ke nan, sai ya ce zai yi shkar gyada, shi kuma daman ba shukar gyada zai yi ba. To shi ke nan sai ya yace a soya masa gyadar, sai aka soya wa Gizo gyada.

Daman sai ya zauna Gizo ya cinye gyadan nan, ya tafi jeji ya je ya yi birgima, ya je ya yi birgima, ya dawo ya ce da koki, koki, na dawo daga -- na dawo daga wajen gonar.

Sai ta ce, Yauwa, Gizo, sannu, sannunka. Ai gara da ka je ka zago gun aikin. Nan ko daman ba aikin yake zuwa ba.

Har kak har kaka ta yi. Lokacin gyada ya yi, sai ya je gonar, Gizo ya je gonar sarki. Daman da ya je gonar sarki ya je gonar sarki, sai ya je ya cicciro gyada kullum. Yana zuwa gonar sarki yana ciro gyada yana kawo wa koki.

Shi ke nan sai rannan sai sarki ya ce! Wannan barna dai ta isa. Bari dai yau - bari dai yau in yi fakon ɓarawon nan da yake satar mini gyadata. Da mun tura fadawa.

Daman Gizo da man da ya ji labarin - mm sarki zai tura fadawansa daman sai ya yi shiga buta. Ya shiga cikin buta, ya je ya buya. Daman da fadawan sarki suka zo sai ya taho yana:

Kurtu bambam kurtu

Kurtu maci dan sarki

Kurtu maci fadawa

Kurtu maci fadawan kansa.

Shi ke nan sai fadawan sarki suka zura a guje, suka ce ba za su iya ba sai sarkin ma ya ce, to, ku, mu je.

Sai sarki ya yiwo shiri shi ma ya taho daman da ya taho shi ma sai maza Gizo ya kuma - ya kuma shiga cikin buta. Sai ya kuma ce masa,

Kurtu bambam kurtu

Kurtu maci ɗan sarki

Kurtu maci fadawa

Kurtu maci fadawan kansa.

Nan ma sai ya koma rugawa a guje. Sarki ya ce ba zai iya ba.


Sai aka ce a yi budurwar danƙo. Sai aka yi budurwar danko.

Daman - daman da ya zo aka shirsshirya mata kayan abinci masu daɗi. Aka zo aka ajiye.


Daman da Gizo ya zo ya ga wannan budurwar dankon. Sai ya ce, a'a! Wannan 'yar budurwar, kina da kyau. Bari in ci dan abinci naki ne? Ya dauki abincin nan ya ciccinye, ya ciccinye abincin.

Sai ya ce, Yar budurwa budurwa, mu ga jikin naki. Sai ya taba, sai ya make, ya koma tabawa, ya koma makewa. Har sarakan suka zo suka same shi. Yana tsaye a halin da yake. Shi ke nan sai suka kama shi suka je suka ɗaure shi.

Sai kura ta zo ta ga Gizo a ɗaure sai ta ce, Taf! Gizo? Me ya same ka kake ɗaure? Sai ya ce, Da Allah, gafara can.

Nima da za'a kawo mini sa. Ya ce, To, kunce ni! Mm. Bari in kunce ka, ni ka daure ni. Ni a kawo mini san. Shi ke nan sai ta ce, to
Sai Gizo ya kunce mm kura ta kwance Gizo. 

Ta daure mm Gizo ya daure kura. Daman sai fadawa suka zo. Sai suka zo suka ga kura sai suka ce, ila! Kun ga Gizo ya zama kura. Nan ma suka samu suka yimata dukan tsiya, suka yimata dukan tsiya. 

Shi ke nan sai gara ta zo sai ta ce, ku ne dai mutanen zamani, a yi muku rana ku yi mutum dare.

Sai ta ce, Ba zan miki ba.

Sai ta ce, To, taushe ni. Sai ta taushe mata igiya. Sai ta ce wa gara, Gara, taru mani in yi miki addua. Sai gara ta taru. Ta lashe ta, da ta lashe ta Gizo ya samu ya gudu. Sai kura ta samu, ta tafi.

Ashe da ma Gizo ya hau kan kanya. 

Sai wannan kura ta je gindin kanya.

Sai Gizo ya ƙwalo mata kanya mai zafi.

Sai ta ce, ìKai! Kai! Kai! Wannan dana tsuntsu, Allah ya tsine aka albarka!

Sai ta daga kai sai ta ga Gizo. Sai ta ce, ìAaaa! Gizo, to sauko, sauko in cinye ka.

Sai ya ce, ìTo, ban da abinki ana cin mutum da guntun kashi a ciki?

Sai ta ce, to sai ta ce, To tafi ka je ka yiwo.
Ya ce, In tsuguna anan?

Sai ta ce, A'a.

in tsuguna anan?

Ta ce, A'a.

in tsuguna anan?
Ta ce, "I'

Can da nisa.

in tsuguna anan?

Sai ta ce, E, to tsuguna anan.

Sai ya ce, Na'am? Sai ya ce, Iye?

Ta ce, Kai kai da kai da waye kai kuma kake maganar?

Sai ya ce, A'a, cewa aka yi in na ga kura da guntun kirgi in kirawo ta.

Shi ke nan, ta ruga a guje, sai ta gudu. 

Ƙurunƙus kan ɗan ɓera.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


Saturday, 14 October 2017

Nishadi: TATSUNIYAR SARKI MAHLANU DA 'YAN MATA

Nishadi: TATSUNIYAR SARKI MAHLANU DA 'YAN MATA

(wannan tatsuniya ce tsohuwa wadda aka
samota daga al'ummar Bantu dake nan Afirka.)


Marubuci: SADIQ TUKUR GWARZO

A wani lokaci mai tsawo daya gabata, anyi wani
mutum wanda yake da 'ya'ya biyu. Dukkan su
yan mata ne, kuma sun isa aure.

Rannan sai wannan mutum ya tsallaka ruwa
izuwa wani gari domin ziyara. Da isar sa sai yake
jin labarin sarkin Garin wanda hamshaki ne yana
neman aure, kuma an gwada dukkan yan matan
garin amma basuyi masa ba.

Dawowar sa gida keda wuya sai ya sanar da
iyalinsa. Babbar 'yarsa wadda sunan ta
Mpunzikazi, tace zata je domin auren sarki.
Mahaifinta yayi murna da haka, ya turawa yan
uwa da abokansa na arziki don suzo a rakata
izuwa garin ta yadda zata zamo matar sarki,
amma sai mpunzikazi tace tafi son a barta taje
ita kadai.
Washe gari taci kwalliya ta kama hanya, tana
cikin tafiya sai ta hadu da Bera. Bera ya matso
gareta yace "kina so na nuna miki hanya?''. Sai
kuwa mpunzikazi tayi tsaki, tace "gafara nan,
waye kai da zaka nuna min hanya?"
Daga nan
bata kara bi takansa ba ta wuce.
Shikuwa sai
cewa yayi "indai a haka zaki to bazaki ci nasara
ba".
Tayi gaba kenan, sai ga kwado yazo gareta.
Kwado yace "idan kinaso zan nuna miki hanya".
Sai kuwa ta daka masa tsawa, tace "kai kauce,
har ka isa kayi magana da matar sarki?"
Sai kwado yace kije gaba, zakiga abinda zai faru"
Taci gaba da tafiya kenan sai ga wani yaro yana
kiwon dabbobi.

Da ganinta sai ya matso kusa
yana cewa "yayata ina zuwa haka?"
Mpunzikazi taja tsaki tace " waye kai da zaka
kira ni da yayarka? Kai kauce kabani wuri."
Yaro ya kara cewa "ina jin yunwa, ko zaki
taimakeni da abinda zanci?"
Sai kuwa ta kara daka masa tsawa tace " ka
kauce ka bani wuri fa nace!!!"
Sai yaro yace " ai kuwa indai haka zakiyo, to ba
zaki dawo ba"
Mpunzikazi dai ta wuce gaba.
Tayi gaba kenan,
sai ga wata tsohuwa tana zaune bisa wani
dandamalin dutse.
Tsohuwa tace "sannu da zuwa
'yar nan ga shawara zam baki: idan kika je gaba
zaki ga bishiyoyi suna miki dariya, kada ki sake
kiyi musu dariya.

Zaki ga kabakin madara da
zuma, kada ki sake kisha, sannan zakiga wani
mutum wuyansa a saman kansa, yana dauke da
ruwan sha, ko yayi miki tayi kada kisha".
Sai kuwa Mpunikazi tayi tsaki tace " wannan
mummunar tsohuwa da rigima take, ko meye
ruwanta dani oho?"
Ai kuwa wucewar ta keda wuya, sai ga bishiyoyi
na dariya, nan itama ta kyalkyale musu da dariya.
Taga kuttun zuma da madara, ta zauna ta
sharba, taga mutumin da wuyansa ke saman
kansa ya bata ruwa ta karbe tasha.
Bayan duk an gama wannan ne ta iso kofar
garin.
Zata shiga kenan sai ga wata budurwa
zata debo ruwa, ashe yar uwar sarkin ce.
Budurwar tace da mpunzikazi "yar uwata ina
zakije ne haka?"
Mpunzikazi tace " wacece ke da kike min
wannan tambayar? To nice matar da sarkin ku
zai aura"
Sai budurwar tazo gare ta tana cewa "tsaya na
nuna miki ta hanyar da zaki shiga garin" Amma
ina, mpunzikazi bata kula taba, ta wuce kurum
abinta.
Da shigarta garin sai mutanen garin suka
tambayeta abinda a kawota, ita kuma ta fada
musu, sai akace mata sarki baya gari yanzu,
amma ga hatsi ta girka masa abinci, idan ya
dawo zaici.
Haka kuwa akayi. Bayan ta gama abinci zuwa
yamma, sai ga guguwa na kadawa, alamun sarki
ya dawo kenan.
Zuwa can aka ce tazo sarki zai ganta. Da
shigarta inda sarkin yake sai ta tsorata, domin
kuwa wani katon maciji ta gani mai kawuna
biyar, a yaren su ana kiransa 'Makanda Mahlanu'.
Ta ajiye masa abincin data girka yaci, sai kuwa
yace abincin ba dadi don haka bata cancanci
zama matar sa ba, nan take ya kanannadeta ya
kashe ta.

Labari sai yazowa yan uwanta cewa batayi
nasara ba.
Hakan yasa kanwarta shirin cewa
itama zata jarraba. Sunan ta mpunzanyana.
Ubanta yace zai tara mutane suyi mata rakiya,
tace to baba babu matsala. Da ranar tafiya tazo
sai suka fita suka kama hanya. Can sai ga bera a
gaban su. Bera yace "yarinya ko kina so na nuna
miki hanya?"
Mpunzanyana tace "ai kuwa zanji dadi idan ka
nuna min ta inda zamu bi". Daga nan sai ya nuna
musu inda zasu bi, suka wuce.
Sunyi gaba kenan sai ga wata tsohuwa. Tsohuwa
tace "yarinya bari na baki shawara, idan kika yi
gaba zakiga hanya ya kasu biyu, babba da
karama, to karamar zaki bi"
Mpunzanyana tace
"Nagode babata, zanyi kamar yadda kika ce"
Haka kuwa akayi kamar yadda tsohuwa ta fada,
suka bi karamar hanya.

Daga nan kuma sai ga
kwado. Kwado yace " bari na baki shawara, idan
kika je garin zakiga wata budurwa a bakin kofa,
ki girmamata yar uwar sarki ce, za kuma ace kiyi
ma sarkin abinci, ki tabbata kinyi abinci mai dadi,
sannan idan kika ga sarkin kada ki tsorata"
Mpunzayana tayi godiya ta wuce.
Bayan sun isa kofar gari, sai ga budurwa yar
uwar sarki. Ta tambaye su abinda ya kawo su,
mpunzayana ta fada mata, sai kuwa budurwar ta
nuna musu ta hanyar da ya kamata su shiga
garin.

Shigar su keda wuya aka gabatar musu da hatsi
domin tayiwa sarki abinci kafin dawowar sa.
Mpunzayana ta natsu tayi girki mai kayatarwa.
Zuwa yamma sai taji guguwa na tasowa, alamun
sarki ya dawo kenan.

Ta dauki abinci ta nufi inda akace mata yake.
Ta
ganshi katon macici mai kawuna biyar, amma ta
dake ba tare da taji tsoro ba, ta gabatar masa da
abincin. Da macijin yaci abincin sai yaji dadin sa,
yace hakika itace matar dazai aura.
Kawai sai
taga yayi birgima ya rikide izuwa santalelen
saurayi.

Akayi biki gagarumi, ya sanyata a gidan sarauta
tare da duk yan uwanta. Ya zama yana matukar
kaunar ta.
Shikenan, kurunkus..

**Darasin Tatauniyar shine; Tarbiyya.
Hakika
babu mai iya cin nasara a rayuwa matukar yana
kaskanta nutane, baya girmama su.

Allah ya bamu dacewa amin.